A dai-dai lokacin da ya rage kasa da kwanaki 7 a gudanar da bukukuwan babbar sallah, a Najeriya raguna na nan jibge a kasuwanni ba bu masu siya .
A wannan shekarar, da dama daga cikin masu sayan Raguna da wuri-wuri kamar yadda aka saba a baya, ba su halarci kasuwa ba har zuwa yanzu.
Masu sayar da dabbobi a kusuwanni sun ce, duk da kudadan ragunan sun banbanta da na bara ,ba a zuwa ana saya sosai.
Masu siyan ragunan da yanzu suka siya, sun shaidawa BBC cewa, farashin ragunan a bana da sauki idan aka kwatanta da na bara.
A bara dai dai sai da aka kai raguna sayarwa a kasuwanin Jamhuriyar Nijar daga Najeriya sanadiyar tabbarbarewar darajar da kudin kasar wato Naira ya yi.
Tambayar ita ce, shin ko a bana ma saboda rashin cinnkin raguna yayinda Sallah ke karatowa zai sa 'yan kasuwa fita da ragunan na su zuwa kasashen waje?
Source: BBC Hausa
Title :
Alamu Ya Nuna Cewa Raguna Zasuyi Kwantai
Description : A dai-dai lokacin da ya rage kasa da kwanaki 7 a gudanar da bukukuwan babbar sallah, a Najeriya raguna na nan jibge a kasuwanni ba bu masu s...
Rating :
5