Kasuwar musayar 'yan kwallo na nufin irin makudan kudin da ake kashewa a ciniki a kasuwar. Cinikin Neymar da aka yi kan kudi fam miliyan 198 daga Barcelona zuwa PSG na nufin dan wasan zai dinga samun kudi fam 775,477 duk mako. Nawa ne albashinka idan aka kwatanta da na wani babban dan kwallo? Yi amfani da kwakuletarmu don gano hakan.
Masu kungiyoyin kwallon kafa a Turai har yanzu suna da sauran lokacin kashe kudade masu yawa kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara a ranar Alhamis da daddare. Yawan kudin da aka kashe a Gasar Premier a bana tuni ya zarce na bara inda aka kashe fam biliyan 1.165.
A shekarar 2001 lokacin da Sol Campbell ya bar Tottenham zuwa Arsenal, albashinsa a mako ya kai fam 100,000, wanda hakan ya sa ya zama dan kwallo na farko a Birtaniya da yake karbar albashin dubu daruruwa. Shekara 16 bayan nan sai Sergio Aguero na Manchester City da Paul Pogba na Manchester United su ma suka fara karbar albashin fam 200,000 a mako.
Matsakaicin albashin da aka biya 'yan wasan Premier a kakar wasan bara shi ne fam miliyan 2.4, a cewar wani rahoto na jaridar da ake wallafawa a intanet ta Sporting Intelligence. Wannan ya yi daidai da fam 46,000 duk mako, wanda ya fi abin da matsaikacin ma'aikacin gwamnati ke dauka duk shekara a Birtaniya.
Hanyar bincike: Sashen Wasanni na BBC ne ya bayar da rahoton adadin kudin da 'yan wasa ke samu wanda aka yi amfani da shi a wannan bincike. Adadin yana nuna yawan kudin ne kafin a cire haraji, kuma bai hada da abin da dan wasa ke samu daga tallace-tallace ba. Kungiyar Kwadago Ta Duniya ILO, ce ta samar da kididdigar matsakaicin albashin kasa-kasa da na duniya baki daya. Bayanan ILO ya lissafa abin da masu albashi kawai ke samu ne, ba abin da masu aiki na kashin kansu ke samu ba. Domin kwatanta albashin da sauran kasashe, wannan kwakuleta na sassauya adadin ta hanyar amfani da musayar kudi da Bankin Duniya ya samar. An samu bayanan rigunan 'yan kwallo ne daga shafinsu na intanet a watan Agustan 2017.
Wadanda suka shirya: Nassos Stylianou, Nathan Mercer, Paul Fletcher, Chris Osborne da kuma John Stanton. Wanda ya yi taswirar 'yan wasan Zoe Bartholomew da Laura Cantadori. Wadanda suka tsara Laura Cantadori da James Offer. Wadanda suka inganta Aidan Fewster, Rosie Gollancz da kuma Becky Rush.
Source: BBC Hausa
Title :
Aikin Shekara Nawa Zakayi Kafin Kasami Albashin Dan Kwallo?
Description : Kasuwar musayar 'yan kwallo na nufin irin makudan kudin da ake kashewa a ciniki a kasuwar. Cinikin Neymar da aka yi kan kudi fam miliyan...
Rating :
5