Gwamnatin kasar, Saliyo ta ce yawan adadin wadanda suka mutu sakamakon ibtila'in zaftarewar laka a Freetown babban birnin kasar ya haura zuwa 441.
Ana cigaba da tono karin wasu gawawwaki daga buraguzan gine-ginen a gundumar Regent, a inda da karin wasu mutane 600 suka yi batan dabo.
Sojoji na taimakawa wajen aikin kuma daya jami'in na cewa kai komo da kayan aiki na gamuwa da cikas a yankin.
Mahukunta na kara yin gargadi kan hadarin barkewar annobar cutattuka sakamakon shan gurbatacen ruwan sha.
Sun kuma umarci mazauna yankin na Regent, inda masifar zabtarewar kasar ta halaka daruruwan jama`a da su yi kaura zuwa wani wuri saboda yankin na fuskantar yiwuwar sake zabtarewar kasa a nan gaba.
An dai yi jana`izar akalla mutum 550, wandanda masifar zabtarewar kasa da ambaliya suka halaka, yayin da alkaluma ke cewa har yanzu ba a ji duriyar wasu mutum 600 ba.
Hukumar kula da al`amuran da suka shafi bala`i a kasar ta ce tun aukuwar masifar ta dukufa wajen gano musabbabin hadarin da hanyoyin kare aukuwarsa gaba; kuma ta gano ya zama dole mutanen gangaren su kaura.
Source: BBC Hausa
Title :
Adadin Mace-Mace Yanata Karuwa A Saliyo
Description : Gwamnatin kasar, Saliyo ta ce yawan adadin wadanda suka mutu sakamakon ibtila'in zaftarewar laka a Freetown babban birnin kasar ya haura...
Rating :
5