Komawa gida da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi a ranar Asabar bayan kwashe sama da wata uku yana jinya a Landan za ta taso da batutuwa daban-daban.
Shugaban, wanda ya fice daga kasar ranar takwas ga watan Mayu domin yin jinyar cutar da ba a bayyana ba, ya mika mulki ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.
Tun daga lokacin da ya bar kasar, mukaddashin shugaban kasar ya gudanar da ayyuka da dama da suka hada da rantsar da sabbin ministoci da bai wa manyan jami'an rundunar soji umarnin komawa Maiduguri don tunkarar Boko Haram, da sauransu.
Rashin tsaro
Daya daga cikin manyan matsalolin da Shugaba Buhari zai taras ita ce ta rashin tsaro a kusan kowane bangare na kasar.
Tun bayan tafiyar shugaban kasar Burtaniya kungiyar Boko Haram ta kara kaimi wurin kai hare-hare a arewa maso gabashin kasar musamman a jihar Borno.
Kungiyar ta kai hare-hare kunar bakin wake da dama, musamman a Jami'a Maiduguri da ma wasu yankuna na jihar Borno.
Sai dai abin da ya fi jan hankali shi ne harin da ta kai wa ma'aikata da ke hakar man fetur inda ta kashe da dama daga cikinsu sannan ya yi garkuwa da wasu.
Hakan ya tilasta wa mukaddashin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo tura manyan jami'an rundunar soji birnin Maiduguri domin dakile hare-haren 'yan Boko Haram. Amma har yanzu ba a saki ma'aikatan da ke hakar man ba.
Haka kuma akwai matsalar sace mutane domin karbar kudin fansa musamman a hanyar Kaduna zuwa Abuja, da ta matsafan kungiyar badoo da ke Lagos da sauransu.
Source: BBC Hausa
Title :
Abubuwan Da Buhari Ya Tarar A Nigeria
Description : Komawa gida da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi a ranar Asabar bayan kwashe sama da wata uku yana jinya a Landan za ta taso da batut...
Rating :
5