Barbara Gattuso lokacin tana da shekara 30 da wani abu ta fara ganin ta fara juya wa mijinta baya game da harkar jima'i. "Na daina yi masa magana kan lamarin, domin ban damu da jima'i ba," a cewarta.
Tsawon shekaru Gattuso, wadda yanzu ta kai shekara 66 ta yi wayon boye wa mijinta don ka da ya zo mata ta ki tara wa da shi kai tsaye; sai ta rika kwanciyar barci da wuri, sannan ta farka kafin ya tashi.
"Bayan wani lokaci hakan al'amarin ya kasance, ko me ke faruwa a nan? Ina son mijina, mun yi auren jin dadi, tare da samun kyawawan 'ya'ya; ko me ke faruwa?"
Matsalar ta sha'awa ce. Duk da cewa mafi yawan mutanen da suka dade da aure za su tabbatar da cewa karsashin sha'awa kan dusashe tsawon lokaci, Gattuso ba ta ma da sha'awar tarawar jima'i ko kadan. Ba ma ga mijinta kadai ba; ba ta ma sha'awar kowa.
Masana tantance tasirin kwakwalwa kan dabi'ar jima'a sun yi ikirarin cewa irin wannan sauyin bijirowar sha'awar jima'i al'amari ne da aka saba gani, musamman ga mata in sun fara tsufa.
Wasu kuwa na ganin raguwar karsashin sha'awa ciwo ne; sakamakon rashin daidaiton sinadarai a kwakwalwa. Ta yiwu yanzu a samu maganin cutar.
A ranakun 3 da 4 ga Yuni, Hukumar kula da ingancin abinci da Magunguna ta Amurka (FDA) za ta tattauna da kwararru su bayar da shawar ko amincewa kwayar Flibanserin a matsayin maganin zaburar da son jima'i na mata "female Viagra" don masu larura su yi amfani da shi ko a jefar da shi a kwandon shara.
Matsalar ta raba kan masana gida biyu, inda wadanda suka amince da masu adawa suka jajirce.
Matsalar kewayar sakonni
Ko mene ne ke kawar da sha'awar jima'i, kuma yaya maganin Flibanserin zai taimaka? Ba mata kadai ne ke kyarar jima'i da sun fara tsufa ba; shaharar gagai samfurin 'Viagra' wani tabbaci ne kan hakan.
A cewar mai barkwanci George Buirns: "Jima'in mai shekara 90 kamar jikqa igiya a ruwa ne." Sai dai yanayin matsalar ya bambanta a tsakanin jinsi (maza ko mata).
Akwai dalilai uku da ke haifar wa mata rashin son jima'i: sha'awa, sha'awa da sha'awa
"Akwai maganar da ake fada a likitanci cewa matsaloli uku ne ke kashe sha'awar jima'i karfin mazakuta, karfin mazakuta da karfin mazakuta," a cewar Stephen Stahl, masanin tasirin kwakwalwa kan dabi'u da ke Jami'ar California a San Diego. "Sannan akwai dalilai uku da ke haifar wa mata rashin son jima'i: sha'awa, sha'awa da sha'awa"
Hakikanin abin da ke kashe sha'awa al'amari ne da ya boyu ga masana kimiyya, ko da yake sun fahimci cewa yana da alaka da zagayen sinadarai.
Daya daga mahangar ita ake kira mutuwar gaba ko mazakuta (HSDD) - a mata kuwa ana yi wa lamarin lakabi da dusashewar sha'awar jima'i sakamakon kin kullewar goshin kwakwalwa da ke yin tarin ayyuka a kullum, kamar tunawa da tura sakon ranar haihuwa ko warware matsalolin aiki.
Sakamakon zagayen sinadarai, wadanda ke tarairayar zaburarwa da annashuwa ya kasance a tauye.
Tun da gaigai din Viagra ya samu nasarar warkar da matsalar jima'in maza (ba tare da ambaton garabasar kamfanin da suka sarrafa shi ba), wasu sun yunkura wajen samar da irin wannan kwayar maganin ga mata, amma wadda za ta shawo kan matsalar kwakwalwa fiye da kafar al'aura.
Flibanserin na daya daga jerin wadanda ke kan gaba.
Da farko an samar da maganin da ke shawo kan dugunzumar damuwa, wanda aka gano tasirinsa kadan ne a kan yanayin mutane. Sai dai matan da aka yi gwajin kwayar magnain a kansu sun bayar da rahoton illar da ba a zata ba; zakuwar son jima'i.
Alamun aikin Flibanserin na nuni da daidaiton sinadaran da ke kewaya kwakwalwa, wato dp[amine da noradrenaline da serotonin.
"Muna jin cewa ko ana daidaita musu zama ko a maye gurbin abin da bai daidaitu ba, ta yadda za su ci gaba da kewayawa," in ji Stahl.
"Tabbas akwai yiwuwar yana taimaka wa mata wajen kauce wa cibiyar zagayen goshin kwaklwalwa da ke tauye sha'awar jima'i."
Bijiro da sha'awa
Duk da cewa kwayar maganin an ajiyeta a gefe a matsayinta na mai kawar da dugunzumar damuwa, saboda takaituwar tasirinta, an sake bunkasata don bijiro da sha'awa ga mata da ke fama da mutuwar kafar al'aura (HSDD).
Sai dai an ci gaba da bibiyar gwaje-gwajen, inda mata suka ruwaito cewa ana samun karuwar "gamsuwar jima'i," sun dai kasa tabbatar muhimmin tasirinta wajen bijiro da sha'awar jima'i.
Sakamakon hakan Hukumar FDA ta ki amincewa da maganin a shekarar 2010.
Ku san a iya cewa Ba'amurkiya kan yi jima'i a kalla sau uku a wata; idan mai fama da larura ba ta yi jima'i sau uku ba, shin ko wannan na nufin kwayar maganin ta gaza?
Nazarin da aka kara yi ya tabbbatar da cewa tana kara zaburar da sha'awar jima'i daga bisani, ko da yake tasirinta ya yi bazata.
"Matsalar dai ita ce, yaya za a kimanta ci gaban da aka samu? Tambayar da Susan Scanlan ta yi, wato Shugabar kun giyar fafutikar kare lafiyar jima'in mata ta Even The Score campaign, wadda ta ciri tuta wajen samar da maganin mutuwar al'aura (HSDD).
(Abin da ya kamata a lura shi ne ta yiwu kamfanoin sarrafa magunguna ya biya Scanlan wani kudi ta ja zugar fafutikarta). Ta yi nuni da cewa tarairayar sauyi ta yi karanci. Kusan a iya cewa Ba-Amurkiya kan yi jima'i akalla sau uku a wata; idan mai fama da larura ba ta yi jima'i sau uku ba, shin ko wannan na nufin kwayar maganin ta gaza?.
A gaskiya matan da ke amfani da kwayar maganin Flibanserin sun bayar da rahoton mu'amalar jima'i sau biyu da rabi cikin kwanaki 28, in an kwatanta da daya da rabi (1.5) na matan da ke fama da mutuwar al'aura (HSDD), wadanda ba sa shan maganin.
Tabbas, wasu daga cikin masu matsalar da aka yi gwajin a kansu sun samu tabbacin gyaruwar lamuran. Gattuso ta shiga jerin wadanda aka yi wa gwajin a shekarar 2011.
Da farko an ba ta makwafin maganin sarrafa tunani (placebo), abin da ta ce bai yi aiki ba, duk da cewa ta yi kokarin zaburar da sha'awar jima'inta.
Sai dai bayan gwaji an ba ta damar yin amfani da maganin gaske. "Cikin makonni kadan na yi matukar samun sauyi," in ji ta.
"Na kan tashi cikin dare in rungume maigidana. Kasancewar kusancin kud-da-kud da sha'awar makalkale wa juna ya zama 100 bisa 100."
Sai dai daya daga cikin abin damuwar shi illolin da ke tattare da nasarorin sun hada da juwa da layi da tashin zuciya. Ko da yake Scanlan ta yi nuni da cewa matsalolin ba su taka-kara sun karya ba, in an kwatanta da na 'Viagra' da sauran magungunan shawo kan mutuwar gaba.
"Bari mu bibiyi wasu daga cikin illolin da ke tattare da magunguna 26, wadanda aka amince maza su yi amfani da su don maganin matsalar mutuwar mazakuta," in ji Scanlan. "Mun ji akwai bugun zuciya da makanta da mutuwar fuju'a da kuma wanda ya fi jan hankalina shi ne, raunin mazakuta."
Wasu kuwa na fargabar in an amince da Flibanserin za a ingiza mata su rika neman maganin matsalar da kamata ya yi a ce sun warwareta ta hanyar tuntubar mai bayar da shawarar zamantakewar ma'aurata maimakon likita, ko shawo kan matsalolin da suka danganci jibga wa kai dimbin aiki ko dugunzumar damuwar.
"Idan aka yi batun sha'awa, dangantakar ma'aurata na da muhimmanci, yanayi muhimmi ne, daukacin halin da aka samu kai, wanda ya hada da fasalin bayyane da na boye duk suna da muhimmanci," a cewar Cynthia graham, babbar malama a fannin kula da lafiyar kwakwalwa ta Jami'ar Southampton da ke Birtaniya.
Akwai wadanda ke jin cewa watsi da Flibanserin zai haifar da rudanin neman magani mafi nagarta.
Ko da a hakan ma ta yarda cewa magani zai yi matukar taimakawa a nau'ukan yanayin. "Ina jin cewa wasu mata na fama da matsalar sha'awa, karshe dai sai an samo kwayar maganin matsalar matan.
Sai dai akwai bukatar a tabbatar kwayar maganin na da amfani a likitance, kuma akwai bukatar sanin illolin da ke tattare da ita," in ji graham.
Wasu na fargabar cewa watsi da Flibanserin zai haifar da rudanin neman makwafin maganin mafi nagarta.
Source: BBC Hausa