A can kasar Indiya kuma an haifi wani jariri da juna biyu, inda binciken likitoci ya bayyana cewa mahaifiyar wannan jariri ce ta yi rashin sa'ar inda tagwayen 'ya'yan ta daya ya shige cikin daya
Likitoci masu amfani da na'ura wajen daukar hoton cikin jikin mutum sun bayyana cewa, sun gano wata halittar ta mutum a cikin cikin jaririn tun a farkon watan Yulin da ya gabata, wanda shi kan shi wannan jariri yana cikin mahaifiyar shi 'yar shekaru 19.
Bayan haihuwar wannan jariri a ranar 20 ga watan Yuli, wani asibiti mai sunan Bilal Hospital a gundumar Thane dake babban birnin Mumbai na kasar Indiya, sun yiwa wannan jariri tiyata inda suke cire wannan juna biyu dake cikin shi.
Wani kwararren likitan yara Thorat, wanda ya yiwa jaririn tiyata, ya bayyana cewa, juna biyun dake cikin jaririn namiji ne kuma tsayin shi ya kai inci bakwai da kuma nauyi na giram 150.
Babu wata damuwa ko matsala da ta ke tattare da mahaifiyar wannan jariri da da jaririn na ta kuma su na cikin koshin lafiya da kulawa a asibiti, a cewar wata likitan mata Nicahali da ta labartawa manema labarai.
Source: Naij Hausa
Title :
An Haifi Wani Jariri Da Juna Biyu
Description : A can kasar Indiya kuma an haifi wani jariri da juna biyu, inda binciken likitoci ya bayyana cewa mahaifiyar wannan jariri ce ta yi rashin s...
Rating :
5