Daga Hausa Times
Mai alfarma sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya nuna damuwarsa matuka game da yadda shafukan sada zumunta na zamani (social media) ke karkatar da hankalin dalibai musamman 'yaya mata
A cewarsa sun gano a yanzu mafi akasarin dalibai musamman yan mata na kwashe mafi yawan lokacinsu a shafukan sadarwa na zamani irinsu Facebook, 2go, WhatsApp da su Instagram da sauransu.
Yana mai cewa wannan dabi'a babbar aibu ce musamman ga yara mata wadanda sune akewa kirari da iyayen al'umma.
Sarkin wanda yake jawabi yau Lahadi a wajen bikin rufe gasar karatun Al'qurani ta kasa kashi na 7 a Sokoto ya nemi dalibai da su bada himma wajen yin abunda zai amfanesu kamar karatun Al-qurani da san'a da koyon ilimi.
Hausa Times ta ruwaito sarkin ya baiwa wadanda suka fafata a gasar su 89 kyautar Naira dubu 10-10 kowanensu a yayinda ya bawa wacce tayi nasara a gasar, Husna Nura daga jihar Katsina kyautar N100,000.
Haka kuma Gwamnatin Sokoto ta bawa dalibar kyautar kujerar Hajji da N150, 000 da firiji da sauran kyaututtuka.
NAN ta ce jihohi 22 ne suka fafata a gasar ta bana wacce akayi tsakanin makaruntun mata kuma Gwamnatin Sokoto ce ta dauki nauyi.
Hausa Times ta kuma ruwaito an raba kyaututtuka ga sauran daliban da sukayi nasara daban daban a gasar.
Kula da ilimi da tarbiyyar 'yaya mata abune da ya zama wajibi domin sune ginshikin al'umma idan suka gyaru al'umma ta gyaru hakanan idan sun baci. inji mai alfarma sarkin musulmi
Ya kara da jan kunnen iyaye da su sanya ido sosai kan 'yayansu musamman su rage salwantar da lokacinsu a yana.
Title :
Yawaitar mata a shafukan sada zumunta na zamani abun damuwa ne matuka– Sarki Musulmi
Description : Daga Hausa Times Mai alfarma sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya nuna damuwarsa matuka game da yadda shafukan sada zumunta na...
Rating :
5