Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasonjo ya yi ikirarin cewa tun da farko Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Marigayi Sani Abacha ya yi niyyar hallaka shi tare da Marigayi Shehu Musa 'Yar adua.
A wata hira da ya ya jaridar PUNCH, Cif Obasonjo ya ce, mutanen Abacha sun yi amfani da guba ne wajen kashe Mariagayi Shehu 'Yar adua amma shi a bangarensa, Allah Ya tsira tar da shi daga sharrin mutanen Abachan a yunkurin hallaka shi.
Ya ce, wasu mutane biyu wadanda ya ce ba zai bayyana sunayensu ba, sun tabbatar masa da cewa Abacha ya nuna cewa ba za mu fita daga kurkukun da ya bayar da umarnin garkame mu ba bisa zargin kifar da mulkinsa da aka yi mana a wancan lokacin.
Title :
Yadda Abacha Ya Kashe Shehu 'Yar adua - Obasonjo
Description : Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasonjo ya yi ikirarin cewa tun da farko Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Marigayi Sani Abacha ya yi niyyar...
Rating :
5