Jihar Kelantan da ke karkashin ikon Jam’iyyar Islama a kasar Malaysia ta amince da dokar yi wa mutanen da suka karya wasu daga cikin dokokin shari’ar musulunci bulala a bainar jama’a.
‘Yan Majalisun Jihar suka amince da matakin a karkashin dokar shari’a, inda duk wasu manyan laifuka na karkashin dokokin Tarayya ne a kasar.
Jam’iyyar Islaman kasar na ci gaba da matsin lamba wajen ganin an aiwatar da dokokin addinin Islama baki daya da suka hada da datse hannu ga mai laifin sata da kuma jefe mutum.
Mataimakin ministan Yankin Mohammed Amar Nik Abdullahi ya ce kotuna ne za su yanke hukuncin inda ya kamata a aiwatar da hukuncin.
Kusan kashi 60 na al’ummar Malaysia musulmi ne, kuma kasar na da tsarin kotuna biyu da suka kunshi wadanda ke bin tsarin boko da kuma na Islama da yawanci suka fi mayar da hankali ga matsalolin gado da sakin aure, ba tare da yin bulala da jefe masu laifi ba.
#rfi_hausa
Title :
Wata Jiha a Malaysia za ta fara aiki da hukuncin bulala
Description : Jihar Kelantan da ke karkashin ikon Jam’iyyar Islama a kasar Malaysia ta amince da dokar yi wa mutanen da suka karya wasu daga cikin dokokin...
Rating :
5