An gurfanar da wasu 'yan Mata 3 a gaban wata kotu da ke birnin Bulawayo na kasar Zimbabwe, bisa zargin yi wa wani fasto da ya je gidansu don bin bashin da suka karba a wajensa fyade.
Mai gabatar da kara ya shaida wa kotu cewa 'yan Matan sun hada baki ne suka yaudari faston zuwa dakinsu inda suka danne shi a kan gado suka yi masa fyade.
Daya daga cikin 'yan matan ta shaida wa kotu cewa ba su rike shi da nufin fyade ba, sai dai don su tabbatar masa cewa shi ma namiji ne kamar kowa, kuma yana da sha'awa.
Dangane da bayanan da wadannan 'yan mata suka yi wa alkalin kotun, sun bayyana cewa, shi dai wannan fasto ya dade yana bata musu rai, ta hanyar zuwa yana leka su a bandaki idan suna wanka, yana nuna wai shi mutumin Allah ne ba ya jin sha'awa ko da ya kalli tsiraicinsu.
Don haka ranar da azal ta kai shi gidan su don bin bashin da ya ce yana bin su, shi ne suka shirya masa tsiya.
Mai gabatar da kara ya kara da bayyana cewa, ranar 14 ga wannan wata na Yuli ne da maraice misalin karfe 7 na dare wanda ya ke kara ya je gidan da 'yan matan suke zaune da nufin karbar bashinsa, amma sai daya daga cikinsu ta ja shi zuwa cikin dakinsu.
"Suna shiga ne sai wata daga ciki ta kama madaurin wandon sa ta kwance, nan da nan kuma suka tura shi kan gado, daya ta hau kansa, wata kuma ta dauko kwaroron roba, yayin da dayar ta kama wasa da gabansa."
'Yan matan dai sun ce, sun shirya yi masa tsiya ne kawai ba wai fyade ba, kuma sun tabbatar masa cewa, yana sha'awar su, domin ba tare da bata lokaci ba, suka rikita masa kwakwalwa.
Alkalin kotun dai ta sa an kulle wadannan 'yan mata har sai zuwa 7 ga watan Agusta, bayan an aika da fasto asibitin kwararru, inda aka binciki lafiyarsa.
Ko a farkon watan nan ma sai da wani malamin makaranta ya kai karar wasu dalibai mata 3 da suka yi masa taron dangi suka yi masa fyade da karfin tsiya.
Title :
Wasu 'Yan Mata 3 Sun Yi Wa Fasto Fyade
Description : An gurfanar da wasu 'yan Mata 3 a gaban wata kotu da ke birnin Bulawayo na kasar Zimbabwe, bisa zargin yi wa wani fasto da ya je gidans...
Rating :
5