Rundunar Sojan Sama ta Nijeriya ta tabbatar da cewa wani jirgin yakinta ya yi hadari a Maiduguri inda ya Fada cikin wani tafki sai dai kuma babu wanda ya rasa ransa a yayin hadarin.
Kakakin Rundunar, Olatokunbo Adesanya ya ce jirgin ya yi hadarin ne a lokacin da yake aikin tattara bayanai daga sama game da shirye shiryen mayakan Boko Haram. Ya ce tuni aka kafa wani kwamiti zai binciki musabbabin hadarin.
Title :
Wani Jirgin Yakin Sojan Nijeriya Ya Yi Hadari A Maiduguri
Description : Rundunar Sojan Sama ta Nijeriya ta tabbatar da cewa wani jirgin yakinta ya yi hadari a Maiduguri inda ya Fada cikin wani tafki sai dai kuma...
Rating :
5