Wata kotun majistare a jahar Kano ta sa a tsare wani tsoho mai shekaru 74 mai suna Ashiru Sulaiman a bisa zargin yi wa jikar shi fyade.
Ana tuhumar Sulaiman ne da yi wa Jikar ta shi mai shekaru 4 fyade da kuma yunkurin yin haka ga wata ‘yar makotanshi mai shekaru 5.
Rahotanni sun bayyana cewa dattijo Sulaiman ya dauki yaran biyu ne zuwa cikin ginin kotun shari’ar musulunci da ke Rijiyar lemo, inda ya aikata aika aikar akan jikar shi.Yayin da yake yunkurin aikatawa ‘yar makotan ta shi ne aka kama shi hannu dumu dumu.Wani mai suna Sulaiman Muhammad shi ya shigar da kara wajen ‘yan sanda.An garzaya da jikar asibiti, inda aka gano cewa ta samu raunika.Da aka zayyano masa laifin shi, dattijo Sulaiman bai musa ba.Laifin ya sabawa sashe na 283 na kundin dokar Penal Code.Alkalin kotun, mai shari’a Aisha Muhammad Yahaya ta bayarda umarnin a tsare shi a gidan kurkuku zuwa ranar 30 ga watan nan yayin da za a ci gaba da sauraran karar.
Title :
Tsoho Mai Shekaru 74 Ya Yi Wa Jikar Shi Mai Shekaru 4 Fyade a Kano
Description : Wata kotun majistare a jahar Kano ta sa a tsare wani tsoho mai shekaru 74 mai suna Ashiru Sulaiman a bisa zargin yi wa jikar shi fyade. Ana...
Rating :
5