Shugaban Amurka, Donald Trump zai tallafawa Nigeria da gudunmuwar Dala miliyan $121 domin tallafawa wadanda rikici ya ritsa dasu a yankin Arewa maso Gabas.
Mukaddashin Daraktan ayyukan agaji na Amurka, Rob Jenkins ne ya bayyana haka a jiya Asabar.
Yace Amurka zata fitar da Dala miliyan $639 domin baiwa yankunan dake fama da matsananciyar yunwa sakamakon rikice rikice kamar yankin Arewa maso gabashin Nigeria, da Somalia, da Kudancin Sudan da Yemen.
Hausa Times ta ruwaito, Mista Rob na kasafta kudaden da cewa Nigeria zata samu Dala Miliyan (DM) $121, Yemen kuma keda DM$191, Kudancin sudan keda DM $199 a yayinda kasar Somalia keda kusan DM $126.
Trump ya kuduri aniyar bayar da tallafin ne bayan tattaunawa a taron shugabannin kasashe 20 masu karfi a duniya (G20) da akayi a Hamburg, Germany
Hausa Times
Title :
Trump Zai Tallafawa Nigeria Da Dala Miliyan $121 Don Yakar Yunwa
Description : Shugaban Amurka, Donald Trump zai tallafawa Nigeria da gudunmuwar Dala miliyan $121 domin tallafawa wadanda rikici ya ritsa dasu a yankin Ar...
Rating :
5