Masu fashi da makami sun hana mutanen Zaria sakat,Ko jiya dai an tare wasu a kan hanyar Zaria zuwa Kano,
Shekaran jiya Mutanen Samarun Zaria su ka wayi Gari da labari mai ban takaici na wani ‘Dan acaba da aka kashe a hanyar Shika. Haka dai aka iske gawar wannan mutumi nan a kwance.
Da safiyar Ranar Talata dai ne mu ka ji labari daga wadanda ke zaune Garin Shika cewa 'Yan fashi sun yi ta'asa. A cikin daren Ranar Litinin kimanin karfe 12:00 zuwa 1:00 aka yi wani fashi. Kwanakin baya ma dai wasu ‘Yan fashi sun tare hanyar zuwa Garin Shikan.
Haka kuma dai mutanen Garin Zabi da ke kan hanyar Kano su na cigaba da ganin fitina don kuwa masu fashi da makami sun hana hanyar sakat. Ko a jiya dai mun samu labari cewa an tare wasu a wurin.
Ku na da labari kwanan aka yi fashi daidai hanyar da ke kan Samaru zuwa Garin Shika. Sai Hukuma ta dage na domin kare lafiyar Jama'a.