MAITAMA SULE 1929-2017
Takaitaccen Tarihin Dan Masanin Kano
Daga Aliyu Ahmad
An haifi Maitama a Shekarar 1929, a unguwar Yola, cikin garin Kano. Maitama shi ne na uku a jirin 'ya'yan gidansu, Rabi, wacce ake kira Yaya ta Zage, Maimuna wacce ake kira Yaya ta Bichi.
An sa masa suna Yusuf, saboda sunan Mahaifin Madakin Kano Mahmudu, shi Madaki yana kiran shi Abbana. Sunan Maitama kuwa an sa masa shi ne saboda Galadiman Kano Yusuf, saboda an yi amfani da makamai sosai lokacin basasar Kano. Akan yi wa duk wani mai suna Yusuf lakabin Maitama.
Madakin Kano ya yi wa Mahaifin Maitama, Abba Sule Danmuri, mukamin mai kula da dukkan al'amuransa na gida da kula da Dawakai. Maitama, yana dan shekaru 4 mahaifiyarsa Hauwa, wacce ake kira 'Yarkayi ta rasu. Ita Allah ya yi ta ne mace mai ban dariya, mai raha, ba ta fushi, shi ya sa duk bukin da ya tashi ita ake kira ta yi ta magana a gidan buki, halinta da iya maganarta Maitama ya gado.
Madakin Kano ya saka Maitama a makarantar Elimintari ta Shahuci a cikin watan Janairu, 1937, dama kafin a kai su makarantar boko, suna yin karatun kur'ani a gida. A ka'ida shekaru hudu ya kamata a yi a elimantari, amma saboda hazakar da Maitama ya nuna shekaru biyu kawai, ya yi aka ba shi damar daukar jarabawar zuwa gaba. A wannan lokacin ne Maitama ya fuskanci kalubalen da bai taba fuskanta ba a rayuwarsa.
Domin a wannan gabar ne Madaki Mahmudu, mai daukar dawainiyarsa a rayuwa ya rasu cikin shekarar 1939. Aka bar kujerar Madaki, tsawon shekaru biyu, ba'a nada kowa ba, har sai a shekarar 1941.
Gaba daya dawainiyyar Maitama ta koma kan Mahaifinsa Abba Sule, wanda a wancan lokacin kuma ba shi da karfin da zai iya daukarta. Sai da ta kai Abba Sule, ya saida duk wani abunda ya mallaka har da suturunsa na sawa dan ya dauki dawainiyar 'ya'yansa, a lokuta da yawa haka suke kwana da yunwa. Ranar da suka samu dan abin daren gasashehen rogo ne za su ci su kwanta.
A karshe Maitama ya shiga makarantar Middle, a wannan datsen an kai matsayin da Maitama ko suturar da zai sa ba shi da ita, kayan makaranta kawai sune kayan sa wansa.
A shekarar 1943 Maitama ya shiga kwalejin Kaduna, yana dan shekaru 13. Maitama, ya kammala karatunsa na kwaleji cikin shekarar 1948, ya kuma kama aikin Malanta, a makarantar Middle ta Kano.
Maitama sun tsaya zabe da shi da tsohon Malaminsa a makaranta, Malam Aminu Kano, wannan zabe ya gudane a Central Office, wannan abu ya faru ne a 1954.
Lokacin da aka fadi sakamakon zaben Malamin, zaben ya bada sanarwar cewa Maitama ne ya lashe wannan zaben. Ana fadar haka Aminu Kano, ya juyo ya cewa Maitama, ina taya ka murna, saura in kaje kuma ka ba mu kunya. Maitama ya cewa Aminu Kano, "Yallabai wallahi, ba zan ba ka kunya ba".
Suka riko hannun juna suka fito tare, wanda suka fara gamuwa da shi shi ne Ado Bayero, inda ya rike hannun Maitama, ya nufi inda magoya bayansa suke, ya ce sun ci zabe.
Ya zama ministan tama da karafa, duk a wannan janhuriya ta farko. Bayan faduwar janhuriya ta farko, ya dawo gida Kano, inda ya rike mukamin kwamishina mai kula da kananan hukumomi a gwamnatin Audu Bako. Ya rike mukamin shugaban hukumar sauraren koke-koken, jama'a ta kasa a gwamnatin Murtala. Ya tsaya takarar shugaban kasa, a jam'iyyar NPN, amma Shagari ya kada shi a zaben fidda gwani. Ya yi wakilin Nijeriya, na dindindin, a majalisar dinkin Duniya
Maitama Sule ya rasu ne a yau Litinin (3-Yuli,2017) a kasar Masar.
Muna fatan Allah ya yi masa rahama.
Rariya
Title :
Tarihin Marigayi Maitama Sule ( Dan Masanin Kano)
Description : MAITAMA SULE 1929-2017 Takaitaccen Tarihin Dan Masanin Kano Daga Aliyu Ahmad An haifi Maitama a Shekarar 1929, a unguwar Yola,...
Rating :
5