Daga Naij Hausa
-Fayose yace 'Ta Buhari tazo karshe'
-Shugabancin Najeriya ba na tsofaffi bane
- Fayose ya dade yana sukar Buhari tun tafiyar shi Ingila jinya
Gwamna mai jayayya da APC, na jam'iyyar PDP, na Jahar Ekiti, Ayodele Fayose ya siffanta Buhari da 'gawa ta ki rami, inda yace 'Daga yau ta Buhari ta Kare’
Ya kuma kara da ‘yan Najeriya sun yi babban kuskure a zaben Buhari da sukayi a matsayin Shugaban Kasar su.Ya bayyana hakan ne a wata lakca da ya gudanar a Jami’ar Benson Idahosa dake Jahar Benin ranar Juma’a. Yace lokaci yayi da matasan Najeriya zasu tashi domin jagorantar harkokin kasarsu.Ya kuma dau alwashin a karkashin shugabancinsa, babu mutumin da zai fito takarar ciyaman din majalisa in ya haura shekara 50, sannan duk wanda ya haura 35 ma ba zai zama kansila ba.Ya ce ‘ni ina da jayayya saboda ina yin abubuwan da mutane basa yi saboda basu da karfin halin da zasu yi, kuma suna tsoro. Jayayya dole ce a mulkin dimokradiyya, dole mu zama masu karfin hali, don duk wanda bai da jayayya to matsoraci ne.’
Ta Buhari tazo karshe daga yau. Ba zai yiwu mu cigaba da gwagwarmaya da yaran mu don mulkin da ya kamata yanzu yana hannun su.
Title :
Ta Buhari Tazo Karshe - Ayo Fayose
Description : Daga Naij Hausa -Fayose yace 'Ta Buhari tazo karshe' -Shugabancin Najeriya ba na tsofaffi bane - Fayose ya dade yana sukar Buhari ...
Rating :
5