Sojoji sun kubutar da masu hako danyen mai da aka sace a tafkin Chadi
DAGA HAUSA TIMES: Rahotanni daga jihar Borno suna bayyana cewa gamayyar Sojoji da yan sa-kai sun samu nasarar kubutar da ma'aikatan hako danyen man nan na kamfanin NNPC da aka sace a yankin tafkin Chadi,
Bayanai sunce an samu nasarar kwato mutanen ne bayan bata-kashi da akayi tsakanin mayakan Boko Haram din da gamayyar dakarun soji
Hausa times ta ruwaito kimanin mutane Bakwai aka ceto ciki har da wani ma'aikaci a jami'ar Maiduguri.
A dazu ne dai Hausa times ta ruwaito maku an yi garkuwa da masu aikin hako danyen mai a yankin tafkin Chadi. Sai dai har kawo yanzu ba'a bayyana hakikanin adadin mutanen da aka sace ba balle a san ko dakwai ragowa a hannun mayakan ko babu
Majiya ta shaidawa Hausa times cewa an kashe dumbin mayakan Boko Haram din kafin aka samu nasarar kubutar dasu
Title :
Sojoji sun kubutar da masu hako danyen mai da aka sace a tafkin Chadi
Description : Sojoji sun kubutar da masu hako danyen mai da aka sace a tafkin Chadi DAGA HAUSA TIMES: Rahotanni daga jihar Borno suna bayyana cewa g...
Rating :
5