Wata majiya mai tushe ta tabbatar min da cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya murmure fiye da yadda muke tsammani, kuma ana sa ran nan bada jimawa ba zai iya dawowa domin cigaba da sauke nauyin talakawan ƙasar nan kamar yadda ya sha rantsuwar yi.
Majiyar ta ƙara da cewar murmurewar da Shugaba Buhari ya yi har ta kai ga ana sa ran zai iya cigaba da mulkin ƙasar nan na tsawon shekaru goma sha biyar nan gaba, kuma akwai yiwuwar idan ya dawo a samu wasu sauye-sauye a kamun ludayin gwamnatin sa kamar yadda hasashe ya nunu.
Murmurewar shugaba Buhari za ta yi matuƙar bawa ƴan ƙasa mamaki idan har suka ganshi a lokacin da ya dawo gida Nijeriya, sakamakon yadda wasu kafafen sadarwa suke ruruta tsanantar jikinsa wanda a zahirin gaskiya ba haka abun yake ba.
Rariya
Title :
Shugaba Buhari Ya Samu Lafiya Fiye Da Yadda Ake Tsamamni
Description : Wata majiya mai tushe ta tabbatar min da cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya murmure fiye da yadda muke tsammani, kuma ana sa ran nan b...
Rating :
5