Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya fice da ga taron bude sabon ofishin EFCC a Kaduna da akayi yau.
Duk da cewa an roke shi da kada ya tafi Sanatan ya ce ba zai iya zama a wajen taron ba ganin cewa wadansu da suka halarci taron na dauke da guntun kashi a duwawunsu da bai kamata ace wai irin wannan taron ne za su halarta.
Hukumar EFCC ta gaiyaci sanata Shehu Sani wajen bude sabon ofishinta a Kaduna. Shima gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya halarci taron.
“ Ban ga ta inda hukumar EFCC za ta iya gudanar da wani bancike a Kaduna ba idan dai irin wadannan mutane ne za su halarci bude sabon ofishin nata a Kaduna.
Cikin wadanda suka halarci taron sun hada da wakilin Sarkin Zazzau, Sanata Sule Usman Hunkuyi, tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero da dai sauransu.
Title :
Shehu Sani Ya Fice Daga Taron Bude Sabon Ofishin EFCC A Kaduna Dalilin Halartar El-Rufai
Description : Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya fice da ga taron bude sabon ofishin EFCC a Kaduna da akayi yau. Duk da cewa an roke sh...
Rating :
5