Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta sanar da cewa matan aure da yan mata a jihar Barno sun fada tsundum harkar shan kwayoyi gadangadan.
Abin yanzu ya zama ruwan dare ga ‘yan mata da matan Aure.
Shugaban hukumar NDLEA Joseph Iweajunwa ya ce matan aure da ‘yan mata da suke amfani kwayoyi kamar su Codeine da Taramol na aikata haka ne don ko su sami karfin yin aiki ko kuma don kawai burgewa wanda ya zama abin yayi ga mata a jihar.
Joseph Iweajunwa ya ce ana amfani da magunguna kamar Tramol da Codeine domin maganin mura wanda idan aka sha su da yawa yakan saka mutum cikin halin maye sannan kuma dalilin haka ake ta samun rasa rayuka a jihar.
Ya ce a shekarar bara hukumar NDLEA ta kama kwayoyin da ya kai kilo gram 6,759 sannan tsakanin watanin Janairu zuwa Yuni hukumar ta kuma kama mutane 248 wanda suke shan kwayoyi da kuma kilo gram336 na kwayoyi kamar su Cannabis, Tramadol, Diazepam, Exol, Cocaine, Heroin, Rohypnol da codeine daga wajen mutane mazauna garin.
Ya ce hakan ya nuna musu cewa an sami karuwa akan yawan mutane dake shan kwaya a jihar.
Joseph Iweajunwa ya bayana wasu dalilan da ya sa ake samun karuwar masu amfanin da kwayoyi a jihar Borno kamar haka;
1. Tashin hankalin da damuwan da aiyukkan Boko Haram ta jefa mutane ciki.
2. Shigowar Boko Haram jihar Borno wanda ya kawo aiyukkan sojoji da ‘yan banga.
3. Yawan‘yan gudun hijira a sansanonin dake jihar wanda ya jefa mutane cikin wani mawuyacin hali.
4. Yadda mazauna jihar ke samun wadannan kwayoyin.
Daga karshe shugaban hukumar NDLEA ya koka kan yadda hukumar ke fama da rashin kudaden da suke bukata domin gudanar da aiyukkansu.
Ya ce kawar da irin wannan matsalar a jihar ba aikin hukumar NDLEA bane da gwamnati kadai amma na kowa da kowa ne.