Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa'ad III ya yi kira ga gwamnatin tarayya kan ta sake maido da tsarin Amirul Hajji wanda ke jagorantar Mahajjatan Nijeriya a kasa mai tsarki a duk shekara.
Shugaba Muhammad Buhari ne dai ya soke tsarin bayan da ya nuna cewa gwamnati ba za ta sake daukar nauyin wasu wakilai zuwa aikin hajji ba wanda matakin ya rage kudaden da gwamnati ke kashewa da kusan Naira milyan 30 a cikin gida sai Dala milyan daya a can kasa mai tsarki.
Sarkin Musulmi ya nuna cewa ba karamin rawa Amirul Hajji ke takawa ba wajen Jin dadin Alhazai a kasa mai tsarki sannan sake dawo da tsarin ba yana nufin gwamnati za ta ci gaba da daukar nauyin sa ba ne.
Title :
Sarkin Musulmi Ya Nemi A Maido Da Tsarin Amirul Hajji
Description : Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa'ad III ya yi kira ga gwamnatin tarayya kan ta sake maido da tsarin Amirul Hajji wanda ke...
Rating :
5