Rundunar 'yan sandan jihar Legas a Najeriya ta ce ta kama wasu maza guda 42 da ake zargi da luwadi.
An dai kama mutanen ne a wani hotel, bayan da rundunar ta kai wani samame sakamakon samun bayanan sirri kan abun da mutanen ke aikatawa.
Yanzu haka rundunar ta ce za ta gurfanar da su a gaban kuliya ranar Litinin.
Neman jinsi guda a Najeriya dai abu ne da ya saba wa al'ada da addini 'yan kasar.
Auren jinsin guda kuma ya haramta a dokar kasar, tun lokacin da gwamnatin tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya rattaba hannu kan hakan.
Sai dai wasu masu rajin kare hakkin 'yancin bil'adama na cikin gida da waje na sukar irin matakan da hukumomi ke dauka kan masu luwadi da madigo.
Title :
'Yan Sanda Sun Kama Masu Luwadi 42 A Wani Hotel A Legas
Description : Rundunar 'yan sandan jihar Legas a Najeriya ta ce ta kama wasu maza guda 42 da ake zargi da luwadi. An dai kama mutanen ne a wani hote...
Rating :
5