Don Allah Jama'a Ku Duba Kuga Sanfurin Motar da Wani Matashi Ya Kera, A Unguwar Badariya Dake Garin Birnin Kebbi.
Daga Abdullahi Muhammad Maiyama
Wannan ba shine karon farko ba, da ake samun matasa masu basira wadanda suka kware wurin kera abubuwa masu amfani a jahar kebbi.
Amma matsala daya rashin kulawa, dakuma basu tallafi da gwamnatin jahar kebbi keyi, wanda hakan ka iya dakatar dasu, daga karshema zai iyasa toshe basira gameda kere-keren.
Yanzu jama'a mu duba muga yadda wannan matashi yayi amfani da basirarsa, wurin kera wannan motar!
Na tabbata wannan mota ko kasashen waje aka kerota sai taci kasuwa mai tsoka, amma sai gashi sanfurinta ya fito daga 'Yan jahar kebbi.
Ina Kira da babbar murya, ga maigirma gwamnan jahar kebbi, da cewa; Ya kamata wannan matashi ayi kokorin tallafamasa domin habaka wannan kere-kere nashi, ta hanyar aikashi kasashen da suka kware wurin kere-kere. Tare da sauran matasa, domin ciyarda jaharmu dama kasarmu gaba.
Haba Maigirma gwamna, ka duba kaga yadda tattalin arzikin kasarmu ke tangal-Tangal, saboda rashin wata hanyar dogaro da kai da kasarmu ke fuskanta!
Yanzu da ace kana tura matasa kasashen waje domin koyomusu kere-kere, da na tabbata wannan ma kadai zai iya zama silar ciyarda jaharmu, dama kasarmu gaba!
Akwai abubuwa da ya kamata a dinga kerawa cikin kasarmu, kuma gamu da matasa a jahar kebbi masu basira, amma basuda aikinyi, irin wadannan matasa sune ya kamata MaiGirma Gwamna ka wai-wayosu, tare tallafamusu ta hanyar kaisu kasashen sukaci gaba, domin su koyo kere-kere ta yadda zasu ciyarda jaharmu gaba, kuma zasu samu hanyar dogara da kai.
Title :
Sakona Zuwa Ga Maigirma Gwamnan Jahar Kebbi, Alhaji Abubakar Atiku Bagudu.
Description : Don Allah Jama'a Ku Duba Kuga Sanfurin Motar da Wani Matashi Ya Kera, A Unguwar Badariya Dake Garin Birnin Kebbi. Daga Abdullahi Muhamm...
Rating :
5