Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da hutun kwana daya na ranar Talata, don yin jana'izar marigayi Dan Masanin Kano Yusuf Maitama Sule.
Kafin rasuwarsa a kasar Masar ranar Litinin, marigayin ya taka muhimmiyar rawa a fannoni daban-daban a Najeriya, inda ya zamo daya daga cikin mutanen da suka fi fice da kuma kima a kasar.
Babban mai taimakawa gwamnan jihar Kano kan kafofin yada labarai Salihu Tanko Yakasai ya ce an ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu saboda rasuwar tsohon fitaccen dan siyasar.
Hakazalika, a ranar Talatar ne za a yi jana'izar marigayin a mahaifarsa da ke jihar Kano bayan an dawo da gawarsa daga kasar Masar wurin da ya yi gajeruwar jinya.
Za a yi jana'izar ne da misalin karfe hudu na yamma a fadar Kano da ke Kofar Kudu a ranar Talatar.
Title :
Rasuwar Maitama Sule: An Ba Da Hutun Kwana Guda A Kano
Description : Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da hutun kwana daya na ranar Talata, don yin jana'izar marigayi Dan Masanin Kano Yusuf Maitama Sule. Ka...
Rating :
5