- An jefa kori'ar yarda ko rashin yarda da dawowar Rahma Sadau' jarumai da yawa maza da mata sun jefa kuri'ar amincewa ko kin amincewa da dawo da Rahma Sadau masana'antar hausa fim.
- Alasan Kwalli (Bakin wake) shine mai shugabantar kungiyar amatsayinsa na shugaban jaruman kannywood.
NAIJ.com dai ta samu labarin cewa Sani Danja yana daga sahun gaba na masu nuna goyon bayan dawo da jaruma Rahma Sadau. Domin acewarsa masana'antar kannywood ta sami koma baya tun bayan da aka kori Rahma Sadau.
Domin Rahma jarumace mai tarin masoya a Arewaci da kudancin kasar nan. Wasu mutane sun daina kallon hausa fim sabida sun rasa Rahma Sadau. Kuma ba abin burgewa bane ace uba ya kori yarsa daga masana'anta.
Duk da yake Rahma tayi laifi kuma ta amsa tayi laifi, ya kamata a yafe mata. Domin mu ma muna yiwa Allah laifi kuma ya yafe mana. Inji Sani Danja.
Amma daga bangaren mata Nafisa Abdullahi ta jefa kuri'ar kada adawo da Rahma Sadau. Acewarta Sabida idan aka dawo da ita an nuna son kai. Domin ashekarun baya an kori jarumai irinsu, Kubura Dako, Safiya Musa, Maryam Hiyana, Ummi Nuhu da sauransu, amma har yanzu ba'a dawo da su ba. Har wasu suka yi aure. Inji Nafisa Abdullahi.
To ana nan ana saka kuri'a Rahma Sadau ta dawo ko kada adawo da ita.
madogara: naij.com/hausa
Title :
Rashin Adalci Ne Indan Aka Dawo Da Rahma Sadau Harkan Fim - Nafeesat Abdullahi
Description : - An jefa kori'ar yarda ko rashin yarda da dawowar Rahma Sadau' jarumai da yawa maza da mata sun jefa kuri'ar amincewa ko kin a...
Rating :
5