Matashi ya yiwa yar shekara 12 fyade, shima jama'ar gari sunyi wa yarsa fyade a matsayin ladaftarwa
Wani abun ban mamaki ya faru a kauyen Muzaffarabad dake birnin Multan a kasar Pakistan a inda aka kama wani matashi yana yiwa wata yarinya yar kimanin shekara 12 zuwa 14 fyade to sai dai ba wannan ne yafi daurewa mutane kai ba.
Abunda yafi baiwa mutane mamaki shine bayan an sanar da mahukuntan wannan kauye abunda ya faru. Rahotanni sun bayyana bayan jin wannan korafi sai majalisar wannan kauye mai suna Jirga suka yankewa wannan matashi hukunci.
To amma hukuncin shine a dauko kanwarsa yar shekara 14 zuwa 17 duka yayan wannan yarinya shima yayi mata fyade amma kuma a gaban bainar jama'a a matsayin hukunci ga wannan matashi.
Hausa times ta ruwaito haka kuwa akayi a inda katti suka dauko kanwar wannan matashi gaban iyayenta yayan waccen yarinya yayi mata fyade itama.
Sai dai bayan da labarin wannan abun takaici ya bazu har yakai kunnen hukuma nan da nan aka tura yan sanda wannan kauye a inda sukayi nasarar kama mutum fiye da 20 da suke da hannu a ciki.
Kodayake dai shi wannan matashi ya gudu amma dai hukumomi suna cigaba da bincike domin kamo shi. A gefe guda kuma kowanne daga cikin iyalin yan matan sun shigar da kara a gaban kotu bisa zargin yiwa diyarsu fyade.
Ance ko a baya ma wannan majalisar kauye ta Jirga ta sa mutanen gari sunyi wa wata mata mai suna Mai fyaden taron dangi saboda an kama yayanta ya yiwa wata mace fyade
Source; Hausa Times
Title :
Ramuwar Gayya: Ya Yiwa Yar Shekara 12 Fyade, Shima Jama'ar Gari Sunyi Wa Yarsa Fyade A Matsayin Ladaftarwa
Description : Matashi ya yiwa yar shekara 12 fyade, shima jama'ar gari sunyi wa yarsa fyade a matsayin ladaftarwa Wani abun ban mamaki ya faru a kauy...
Rating :
5