A yau Laraba ne aka soma gudanar da wasan kwallon dawaki a garin Bauchi.
A yayin bude wasan, Kungiyar M A SOCIAL MEDIA SUPPORT GROUP ta bi sahun kungiyoyin da suka hallara a filin wasan.
Wasan, wanda gwamnatin jihar Bauchi karkashin Barista M. A Abubakar ta dauki nauyin shirya shi, ya samu halartar masana harkar kwallon Dawaki daga kasashe daban daban da suka hada da Ingila, Canada da sauransu.
Manyan gwanayen 'yan wasan da suka yi fice a wasan kwallon Dawaki, irin su Yalwa Buba, Abullahi Laushi, Abubakar Usman da sauran su suna daga cikin masu buga wasan.
Haka kuma wasan ya samu halartar wakilin gwamnan Bauchi, wato kwmishinan Matasa da wasanni da wasu daga cikin mukarraban gwamnatin jihar Bauchi.
Haka shi ma Mai Martaba Sakin Bauchi Alhaji Dakta Lurwanu Suleiman Adamu ya samu damar halartar kallon wasan. Da sauran masu rike da manyan sarautun gargajiya na jihar.
Dan Majalisa Mai wakiltan Duguri Gwana Hon. Ibrahim Bala Hassan (Walin Duguri) da tawagar sa su ma sun halarci wannan gasa.
Title :
Photos :Yadda Aka Bude Wasan Kwallon Dawaki A Jihar Bauchi Jiya.
Description : A yau Laraba ne aka soma gudanar da wasan kwallon dawaki a garin Bauchi. A yayin bude wasan, Kungiyar M A SOCIAL MEDIA SUPPORT GROUP ta bi ...
Rating :
5