Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta kama wata mata mai suna Omotayo Salawudeen, 'yar kimanin shekaru 39, bisa zargin biyan kudi a kashe mijinta, Alhaji Salawudeen Hakeem mai kimanin shekaru 43 saboda ya yi mata kishiya.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar Olafimihan Adeoye, yace matar ta dauki hayar wani tsagera mai suna Osogbo a inda ta biya shi naira 10,000 ya kashe mijin nata saboda ya kara aure. Bayanai sun ce matar ta gayyaci tsageran ya buya a cikin gidanta har zuwa lokacin da mai gidan nata marigayi Hakeem ya dawo gida.
Majiyar mu ta nakalto mana cewa margayin yana dawowa ya kwanta barci sai matar ta sanya matashi (pillow) ta danne masa fuska a yayin da tsageran da ta dauko haya ya fito daga inda ya buya ya sokawa mijin nata wuka a kirji kuma a nan take ya mutu.
Kwamishinan ya cigaba da bayyana cewa bayan da matar ta fita tana kururuwar neman dauki bisa karyar cewa wasu makisa sun kashe mijinta sai daya daga cikin yan'uwan margayin Engineer Salawudeen Jimoh ya garzaya ofishin 'yan sanda dake unguwar ya sanar da su halin da ake ciki.
Majiyarmu ta samu rahoton asirin matar ya tonu ne bayan da rundunar 'yan sandan ta dukufa yin bincike game da faruwar lamarin. Yanzu haka dai kwamishinan yan sandan yace suna cigaba da bincike akai kuma zasu gurfanar da wacce ake zargin a kotu da zaran sun kammala.
Title :
Photos: Wata Mata Ta Biya Dubu Goma An Kashe Mijinta Saboda Ya Yi Mata Kishiya
Description : Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta kama wata mata mai suna Omotayo Salawudeen, 'yar kimanin shekaru 39, bisa zargin biyan kudi a ka...
Rating :
5