Wani magidanci dake zaune a Layin 'Yan Kaji a cikin garin Jos, ya koka da halin kuncin rayuwar da ya samu kansa a ciki, saboda rashin karfin daukar dawainiyar jariran da Allah ya arzuta shi da su har 3.
Wadannan jarirai da dukkan su mata ne kari ne kan wasu ukun da wannan bawan Allah yake da su, wanda yanzu yaran sa 6 kenan a haihuwa 4.
Ko da yake, mahaifan wadannan yara ba su yi bakin cikin haifar su ba, amma halin da suka samu kansu sun kasance abin tausayawa matuka.
Malam Mahmud ya ce, tun bayan aikin da aka yi wa matar sa Aisha a babban asibitin koyarwa na Jami'ar Jos, inda aka ciro wadannan yara, suka fuskanci matsalolin rayuwa da jarabawa. Domin hatta madarar da ake ba su kari kan ruwan nonon da suke sha sai da ta fara gagara, saboda a kwana 3 suke shanye gwangwani guda.
Halin kunci da jarabawar rayuwa ta sanya dole su bayyana halin da suke ciki, don ko za su dace wani ya tausaya musu su samu wani tallafi daga wajen jama'a. Ko da kuwa da abin shayarwar su ne.
Malam Mahmud wanda karamin dan kasuwa ne ya ce, "Dawainiyar na da yawa gaskiya, kuma hakki ne a kaina in kula da cin su da lafiyar su, da ta sauran 'yan uwansu."
Da fatan jama'a za a tausaya kuma a taimaka da abin da Allah ya hore.
Don karin bayani sai a tuntubi lambar Malam Mahmud Badamasi 0803 389 3828
Allah ya ba da ikon taimakawa, amin.
Daga Zuma Times Hausa
Title :
Photos: Wani Magidanci Ya Koka Da Dawainiyar Shayarwa Bayan An Haifa Masa 'Yan Uku
Description : Wani magidanci dake zaune a Layin 'Yan Kaji a cikin garin Jos, ya koka da halin kuncin rayuwar da ya samu kansa a ciki, saboda rashin k...
Rating :
5