Wani magidanci ya yi wa matarsa mai dauke da juna biyu mugun duka a garin a Argungu dake jihar Kebbi.
Mijin mai suna Hamisu ya yi wa matarsa Ubaida Sani duka ne bayan ya ba ta maganin zubar da ciki ta ki ta sha, wanda hakan ya sa ya yi mata duka.
Yanzu dai Ubaida Sani tana kwance a asibitin garin Argungu kuma 'yan uwanta sun shigar da Kara gaban 'yan sanda domin a bi mata hakkinta.
Yanzu dai abun jira a gani shine matakin da hukumar ta 'yan sanda za ta dauka na ta kama Hamisu ta gurfanar da shi gaban kuliya, domin wani shedun gani da ido ya shedawa RARIYA cewa Hamisu ya ji 'yan sanda na nemansa. Kuma ya ce ba za su iya yi masa ba, ganin yana da manya.
Title :
Photos: Wani Magidanci A Jihar Kebbi YaYi Wa Matarsa Duka Saboda Ta Ki Zubar Da Ciki
Description : Wani magidanci ya yi wa matarsa mai dauke da juna biyu mugun duka a garin a Argungu dake jihar Kebbi. Mijin mai suna Hamisu ya yi wa matar...
Rating :
5