Usman Mu'azu, Hadiza Gabon, Asnanic, M. Sharif Da Sauransu Sun Samu Lambar Yabo A Gusau
...bayan nan Gabon ta ziyarci asibiti domin duba marasa lafiya
Daga Rariya
A ranar Asabar din da ta gabata ne aka karrama wasu daga cikin 'yan fim din Hausa garin Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Lambar yabon wanda kungiyar makaranta Mujallar Fim suka saba bayarwa a duk shekara, wanda kuma shine karo na biyar, daga cikin wadanda ta karrama a wannan karon sun hada da furodusa Usman Mu'azu, Nazifi Asnanic, Rabi'u Rikadawa, Umar M. Sharif, Hadiza Aliyu Gabon da sauransu.
An karrama 'yan fim din ne bisa gudummawar da kowannensu ke bayarya a bangarensa a farfafjiyar finafinan Hausa.
Bayan an gama bada lambar yabon ne jaruma Hadiza Gabon ta je duba marasa lafiya a asibitin Ahmad Sani Yariman Bakura dake Gusau.
Title :
Photos: Hadiza Gabon Ta Samu Lambar Yabo
Description : Usman Mu'azu, Hadiza Gabon, Asnanic, M. Sharif Da Sauransu Sun Samu Lambar Yabo A Gusau ...bayan nan Gabon ta ziyarci asibiti domin ...
Rating :
5