Sanata Ali Modu Sheriff, tsohon shugaban bangare na jam'iyyar PDP, ya musanta cewa ya taya bangaren Ahmed Makarfi murnar darewa kan karagar jam'iyyar PDP, inda yace shi baya ma da wani shafi na tuwita balle har yayi amani dashi, kamar yadda wasu kaaen yada labarai suka ruwaito.Ali Sheriff, yace sun kadu matuka da hukuncin da kotun kolin ta yanke, sannan ya ce rainin wayo ne ma ace wai an musu afuwa kan jayayya da suka yi da shugabancin Ahmed Makarfi.A ta bakin kakakinsa, Mr. Bernard Mikko, yace 'ai ba wai haka nan siddaran muka shiga Wadata Plaza ba kamar wasu haramtattun shuwagabanni, zabe akayi muka shiga muka ci, to don me za'a ce wai an yafe mana kamar munyi ba daidai ba?'
An dai jiyo bangaren Ahmed Makarfi na cewa sun yi yaffiya ga bangaren Sherif din ne tun bayan da kotu ta mika musu ragamar jam'iyyar.Kuma ma dai, kakakin na Ali Sheriff, yace abin takaici ne a ce jam'iyyar su ta PDP ta fada hannun wadanda suke da manyan kesa-kesai a kotunan kasar nan, kan badakala da cin hanci da rashawa da almundahana da kudaden gwamnati lokacin suna kan karagar mulki.
Daga Naij
Title :
PDP Ta Koma Hannun Barayi - Sanata Ali Modu Shariff
Description : Sanata Ali Modu Sheriff, tsohon shugaban bangare na jam'iyyar PDP, ya musanta cewa ya taya bangaren Ahmed Makarfi murnar darewa kan kara...
Rating :
5