Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo zai ziyarci jihar Zamfara a ranar Talata mai zuwa. Ziyarar dai ana sa ran ta kwana daya ce wadda zai bude wasu ayukka da suka hada da wani titin mota da ya hada da jihar Sokoto, Zamfara da Kebbi. Wanda gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta yi da alkawarin gwamnatin tarayya za ta biyata.
Wannan shine karo na biyu da mataimakin shugaban kasar ya kai ziyara a jihar ta Zamfara wanda tuni wasu masu sharhin siyasa ke ganin bai rasa nasaba da wani sabon kawancen siyasa tsakanin gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari ke kokarin kullawa da Osibanjo.
Haka kuma wasu suna ganin gwamnan jihar Zamfara na yunkurin wanke sunansa ne akan takaddamar da suke faman yi da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) dake zarginsa da karkatar da makudan kudaden jihar.
Tuni dai gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa wannan ziyarar gani da ido ne tare da shedawa gwamnatin tarayya ayukkan da suke yi.
Rariya
Title :
Osibanjo Zai Ziyarci Jihar Zamfara
Description : Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo zai ziyarci jihar Zamfara a ranar Talata mai zuwa. Ziyarar dai ana sa ran ta kwana daya ce...
Rating :
5