By *AYUSHER MOHD*📚
© *NWA*
💥 *NI DA PRINCE* 💥
☄☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
No. 5⃣6⃣
Sun fito shida Farha, ko kallansu bai ba ya wuce
tare da cemata kisameni a mota, Farha ta fito
janye da jaka, ta kuma rataya handbag d'inta, ta
karaso kusa da Fulani tace "Fulani ni zan wuce,
amma zan d'inga lekowa."
Fulani tace "ina zaki?"
Farha tai shiru sai kuma tace " nikaina bansani
ba, yayana ne yace infito." Fulani tai dariya tace
"lalai Farha, kawai dan Salman yace ki fito
shikenan sai ki fito?" Farha ta mike tare da kallan
Ishaq tace " na wuce."cikin rawar murya Ishaq
yace to.. Sannan ta kalli fulani tace "nagode
sosai." Ta juya tai waje Fulani ta bita da kallo
tace "maza, hmmm Allah dai yasa ba hotel yake
shirin kaita ba." Sai kuma ta mike ta saki dariya
ta matso kusa da Ishaq tace "Allah yasa hotel
d'in zai kaita, da alama ya kamata ka tura mana
wannan mai kula da harkokin Salman, ya
tabbatar ya d'auko hotonsu inzasu shiga hotel
d'in."
Ishaq ya kalleta yace " Umma na kula baki damu
da harkata ba, kawai ke kanki kika sani, burinki
kawai inzama Sarki, baki damu da halin da nake
ciki ba."
Fulani ta kalleshi tad'anyi siririn tsaki tace "
maganar Salma ce?"
Ishaq yace " har da ita."
Fulani ta dafa kai tace "oh God! Ishaq dan
kanasan abu nizan je in jawo maka hankalin
abinda kake so? Kaje kayi duk abinda kaga
dama." Tai maganar cikin gatse, Fulani ta d'auka
zai bata hakuri, amma sai jitai yace " yauwa
Umma nagode kwarai." Yanakainan yai waje da
saurin shi, tana kiranshi ko kulata baiyi ba.
Tace " Oh God! mai yaron nan yake tunani?"
Sun d'au hanya Farha sai jansa take da hira,
shidai sama sama kawai yake amsa mata, can
yace "Farha?" Jin yanda ya kirata yasa jikinta yin
sanyi, tace " Naam"
Salman yace " I won't ask you to forgive me, dan
nasan abinda nake shirin yi shine dai dai, koda
kuwa zaki kulaceni, ki zageni, it won't matter,
nafiso na zama bad guy a kan harkata dake,
bazan bari ina kallo halayenki su canza ba, bayan
nasanki sarai."
Farha jikinta yai sanyi ta kuramai ido, tarasa
mezatace, batai magana ba taga sunzo hanyar
airport, kallanshi tai cikin tsoro da mamaki tace "
yayana nasani nayi ma laifi, bai kamata nayarda
har nasama maganin bacci ba, amma yayana this
is not right, karka wulakanta san danake maka."
Hawaye ne ya zubo mata ta share.
Salman shikanshi tausayinta yake, yasani bai
kyauta ba amma bazai bari yana kallo takoma su
fulani ba.
Baice komai ba ya shigaba da tukinsa, Farha kuka
take sosai, ya daure yace" garin nakune bakya
san zuwa kome?" Farha haushi ya kamata ta
d'auka in tana kuka zai tausaya ya fasa tace"
nikaine banasan na rabu da gani." Salman ya sa
signal, yace " Farha kije ki nutsu kiyi tunani, me
kikeso?" Farha ta share kwalla tace " ni
yarinyace? A iya sanina ko matarka na girmeta
amma kace min ban masan me nake so ba?"
Salman ya karasa ciki, ya kira abokinsa, Farha
idanta yai ja, kana ganinta kasan taci kuka,
Salman bai kara mata magana ba, itama haushin
sa yasa taki mai maganar, sai dayaga sun shiga
check out sannan ya juya ya hau mota.
Waya ya d'auka ya mata transfer na kud'i 100
thousand, sannan ya ja mota yai waje.
Ishaq kam bangaren Salma ya nufa direct, sai
wani gyara kwalar riga yakeyi, yana shiga ya kalli
bayin gun yace "Salma fa?" Hanne tace tana ciki.
Ishaq ya kalleta yace " an bani sako ku jira a
waje bari in shiga ciki."
Yana shiga ya saki labulan falon ya fara kallon
part d'in, randa yafara zuwa dayake fada ne
yakawoshi bai kalla dakyau ba, amma irin nashine
kawai dai ya kula furniture's d'in nan sunfi nashi,
d'akin daya tuna Salma ta fito daga ciki wancan
zuwan ya karasa tare da yin knocking.
Salma dake zaune tana gyarama Salman
wardrobe yasa ta mike a hankali tai kofa, ta
bude.
Ganin ba kowa yasa ta fito falon sosai, Ishaq
dake tsaye jikin labule yai sauri ya shige d'akin,
Salma ganin ba kowa yasa ta koma d'akin tare
da rufowa, sai dai batasa key ba.
Tana zuwa wajen gado taji an rungumota ta
baya, murmushi tai tace " My Prince dama
kaine?" Jin kanshin bana Salman ba gashi yayi
shiru yasa cikin mamaki ta kai hannunta kan
hannunsa dake cikinta, inaaaa ba hanun Salman
bane, da karfi ta fizgeta juyo cikin tsananin tsoro.
Wazata gani? Ishaq? Tsoro ne ya kamata cikin
rawar murya tafara baya baya tanacewa " yarima
menene hakan?"
Ishaq ya matso yace " Salma please ki taimakenk,
nikad'ai nasan me nakeji in na ganki, Salma zan
mutu saboda ke."
Salma tace" me kake fad'a? Kamasan me kake
fad'a? Matar kaninka ce nifa? Ko ba matar
kaninka bace ni ai da kunya ka kalli mace
kad'inga mata zancen banza."
Ishaq ya fara matsowa, Salma kam zuciyarta
bugawa kawai take, wayarta ta hanga dake kan
madubi ba damar kiran Salman, ganin yanda
Ishaq ke tahowa yasa cikin tsoro ta d'au pillow
ta tare gabanta, sai dai tana cikin matsawa sai
jinta tai a bango, duka kawai take kaiwa da pillow
cikin fad'a tana cewa "ka fita, zan sa ihu fa?"
Ishaq kam sai daya karaso, ya rike pillow d'in
tare da fizgewa da karfi ya cillar dashi, hannunta
yariko da karfi, Salma ta kaimai cizo, amma ina
ko ajikinsa, ihu tasa sai dai bataga kowa ba, ihu
take sosai, ga Ishaq ya dage so yake yakai
bakinshi nata, sai cemata yake " Salma
kitaimakeni kamar yanda Allah yataimakeki."
Salma ganin yakusa kai bakinshi nata yasa ta
kwallama Salman kira da karfin gaske, jisukai an
bude kofa da karfi kamar za'a balla, Isahq6 ya
juyo dan yaga ko wani d'an rainin hankalin ne.
Salma kam kuka take sosai, Salman ya tsaya a
jikin kofa kamar zaki, idanunwashi sun canza
kala, fuskar nan a murtuke, a hankali Salma ta
bud'e ido, ganin Salman yasa ta fizge hannunta
daga gun Ishaq daya zama gunki, jikinsa sai
tsuma yake, itakam da gudu tai gunsa ta
rungumeshi tana kuka.
Salman kallan ishaq kawai yakeyi kallon dashi
kad'ai yagama tsorata Ishaq jiyai har hanjinsa
kad'awa suke, yama rasa me zaiyi, gashi bai
cinma burins ba, amma ya d'auka hotel suka tafi
da Farha.
☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
No: 5⃣7⃣
Salman cikin zafin rai yad'an daga Salma daga jikinsa yai kan Ishaq, yanda Ishaq yaga Salman yayo kansa yasa yai baya yana cewa " Salman tsaya kaji, ba abinda kake tunani bane, gani nai kamar matarka batada lafiya shine nakesan tai maka......." ai kafin ya karasa jiyai an kaimai naushi da kafa a baki, jikake tim, Ishaq ya fadi, ga inda Salman ya bigeshi yafara jini, Ishaq ya d'ago cikin tsoro dajin zafin bugun ya kalli Salman yace " Salman nifa yayanka ne? Me kakemin haka?"
Salman ya matso inda yake ya shako wuyan rigarsa cikin b'acin rai yakara kaimai naushi, Salma kam tsoro ya kamata, karasawa gunsa tai ganin yanda yake naushin Ishaq, dafashi tai cikin hawaye tace " Prince ka bari please."
Sai a lokacin hankalin Salman ya dawo jikinsa, ya kalli Ishaq da bakinsa sai jini yake, duk fuskarsa tayi jaaa da alama anjima kad'an gun zai kumbura.
Mik'ewa yai daga kan Ishaq d'in sannan yasa hannu ya kamo hannunsa, yai hanyar waje dashi, sai daya fita dashi daga part d'insa yana zuwa kofar ya sakeshi ya nunashi da hannu, ya kuma kasa magana, da alama hannun kad'ai na kula yagama tsorata Ishaq, ga bayi da fadawa sai kallansa suke, suna gulmar abin.
Salman ya rufo kofarsa da karfi yai ciki, Salma kam suna fita ta zube agun ta shiga kuka, meke faruwa kuma? Salman ya bud'e kofar ya shigo, ganinta a zube tana kuka yasa yaji zuciyarshi takara karaya, a hankali ya karasa inda take, yana zuwa ya zauna kusa da ita, ya jawota jikinsa, kuka takeyi shikanshi ji yake kamar yai kukan ga kanshi dake sara mai yana rike da ita yaji kirjinsa ya shiga zafi, ga yau harda bayansa, Salma gani tai yana kankameta da karfi ga sai durkusawa yake.
D'agowa tai cikin tsoro, takalleshi, ganin yanda yake yasa ta rikece, tace "ciwon ne?" Magana take cikin kuka, Salman kam ya kasa magana cikin rud'ewa ta mik'e ta shiga neman maganinsa, sai dai ta rasa shi, a kid'ime ta matso tace " Prince ina maganin?" Ganin kamar baya iya ma magana yasa jikinta ya shiga rawa, kawai tad'au wayarsa ta duba contact, number waziri taga an rubuta a jiki da sauri kawai tai dialing, waziri ya d'aga yace " Yarima ya kake?"
Salma cikin tsoro tace " Waziri nice, ku turo likita d'an Allah Salman ba lafiya."
Yace " ki nutsu Salma me ta sameshi?" Salma ta kalli Salman gani tai ya tintsiri ya kwanta yana murkususu, ai batasan sanda ta yarda wayarba tai kansa, tana jijigashi da jiran sunansa.
Waziri da sauri ya kashe wayar, dama yana zaune kusa da Sarki ne, tunda Sarki yaji ana Salman ba lafiya duk ya rikice, kawai dai yana zaune ne amma gaba d'aya hankalinsa yagama tashi, waziri ya d'aga waya ya kira likitansu, suna gama waya ya kalli Sarki yace " ko jokin ne?" Sarki ya kalleshi yace " kai sauri kaje ka dubashi, amma me ya faru dashi haka?"
Kafin waziri yai magana wanj bafade ya shigo yace waziri da matsala fa? Waziri ya kalleshi yace " matsalar me kuma?" Bafaden ya kalli Sarki sannan yai kasa dakai, Sarki yace " fad'i maganarka ba komai."
Bafaden da gulma ke cinsa yai kasa dakai yace " Ranka ya dade tuba ina kunyar sanar dakai wai an kama yarima mai jiran gado, a d'akin Salman."
Cikin rashin fahimta Sarki yace " ban fahimci me kake san fad'aba, an kamashi kamar ya?"
Waziri daya fahimci me maganar bafaden ta nufa, ya kalleshi yace tashi kaba mutane guri dama can munafirci kazoyi, ka kuma tsumayi hukuncin abinda kai."
Waziri yana ganin mutumin ya fita ya kalli Sarki yace " da alama Isahq ne dalilin tashin ciwon Salman." Sarki ya kalleshi yace " kana nufin d'akin da ake nufi ana nufin gun katar Salman ko me? Indai har ciwo ya tashi alamar ba karamar magana bace."
Waziri yai shiru, ganin haka yasa Sarki ya mike cikin tsananin tashin hankali yace "wani hauka da dabanci ne wannan?"
Waziri yai shiru aranshi yace " Salman kam ai yana ganin abu agun mutanen nan, badama nai magana ko na fad'ama, kar nima abu yashafe ni dan nasan halin fulani sarai."
Jiyai Sarki ya kalleshi cikin tsananin b'acin rai yace " wato ba wannan ne abu na farko da akemai ba kenan? "
Waziri ya d'ago cikin tausayi yace " yazanyi Ranka ya dad'e?"
Jin haka yasa Sarki yai baya tare da girgiza kai zama yai a kujerarsa, a runtse ido, a hankali yace "Salman mena aikata gareka?"
Waziri ya mik'e jiki a sanyaye yace " bari inje gun Salman kila likitan ya iso." Sarki ya mik'e yace "muje tare."
Salma kam duk tagama rud'ewa, banda kuka da rungume Salman ba abinda takeyi, Mik'ewa tai ta shiga duduba drawers tanayi tana hawaye, sai dai sam tarasa maganin Salman, jitai an kwakwasa d'akin cikin sauri ta bud'e, wani mutum tagani, da karamar jaka kamar akwati, ai bata tambayeshi ba kawai tai tunanin likitane tace gashi nan, cikin sauri ya shigo, ganin Salman a wani hali yasa ya shiga bashi taimakon gaggawa, Sarki da waziri ne suka shigo, Sarki yanda yaga Salman ranshi ya kara b'aci ya kuma ci alwashin ba Ishaq ba ko Fulani indai tanada hannu acikin abinda akema Ishaq wallahi bazai kyalesu ba.
Likitan ya dade akanshi kafin Salman ya samu nutsuwa, bacci ne ya d'aukeshi, Sarki cikin tausayin d'an nasa ya matsa kusa dashi, Salma ya kalla dake zaune akasa jikin gadon idanta harsun kumbura jiyai idanunshi naneman kawo kwalla, ace d'anshi da matarsa suna cikin wannan hali shi yanacan akan kujera baisan meke faruwa ba?
Kallan waziri yai yace "akira Ishaq da Fulani su sameni a fada, sannan a duba matarsa a tabbatar ba abinda ke damunta, sannan a kara kiran likitan da akace zai ma Salman aiki aji yaushe zai iso."
Likitan ya amsa da toh.
Sarki ya mik'e har yakai kofa ya juyo yakalli Salma yace " Salma taso inasan magana dake."
Salma ta amsa tare da mik'ewa.
A fali ya zauna, itama taje tare da zama a kasa, ya kalleta yace " Salma ki dubi Allab da matsayina agub mijinki na mahaifi, ki fad'amin meke faruwa tsakaninsa dasu fulani ko ince tsakaninku, tunda ance neman haik'e mike yaso yi."
Salma ta kalleshi hawaye ya zubo mata tace " Abba bansan kezance ba, nadaisan kawai basa kyauata mishi."
Sarki yace " hakan ma nagode tunda har baki karyata zuwan Ishaq bayau hakan ya tabbatarmin yayi abinda akace."
Salma ta share kwalla, ta daure tace " Abba in zamanmu zai zama matsala anan ka amince mu bar nan gidan dan Allah."
Sarki ya had'iyi wani abu yace " Salma bazan bari Salman yabar nan ba, dan kuwa shine magaji na, sai dai na miki alkwari ba abinda zai kara samunku daga ke har shi, kuma duk wanda yasan da hannunshi acikin abinda akamai ba shakka sai ya gamu da fishi na."
Ya mik'e tare dayin waje, Salma tabishi da kallo hawaye ya zubo mata.
By *Ayusher Mohd*📚
© *NWA*
☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
No: 5⃣8⃣
Duk sun fita sun bar Salma agun Salman, hannunsa ta rike kam tana kallansa, bayan magrib taga a hankali Salman yad'anyi motsi da hannunsa, ta matso ta kalleshi tace " Prince!!!"
A hankali taga yafara bud'e idanunsa cikin kuka kuka_ dariya dariya tace " Prince are u alright? "
Salman ya kalleta tare da jawo hannun ta data rike nashi, daf tazo kusa dashi, Salman yasa hannu ya share mata hawaye sannan ahankali yace" wannan matar tawa akwai raguwa, tafiya saurin kuka."
Salma ta kalleshi sannan tasa d'ayan hannunta ta share kwallar data zubo mata tace " bakasan yanda na tsorata bane."
Salman ya mik'e zaune sannan yasa hannu a wuyanta yad'an jawota suka matso daf da juna dan suna iya jiyo numfashin d'ayansu, a hankali Salman yace " yanzu dai na warke ai sai adaina sa idanuwan danafiso a duniya sudaina zubar da hawaye."
Salma ta sa hannu ta rungumeshi, a hankali ya d'agota tare da tsotsen lebenta yace "I luv u Salmah." Lumshe ido tai wasu hawaye ne zuka zubo masu sanyi, murmushi Salman yai ya tsaya yana kallanta, ahankali ta bud'e idanunta,wani kallo tamai da ita kanta batasan tayi ba, ajiyar zuciya yai yace "ahh lalai na yarda matatace vitamin A d'ina da alama har naji karfin jikina ya dawo, Salma cikin shagwaba tace " kai Prince banda zolaya."
Salman yaja kunnenta da d'an karfi har saida tai kara yace " wayace ki d'inga bud'ema kowa kofar d'akin nan?"
Salma tace " Prince dazafi fa?"
Yace "nasani ai,
Laifi kikai ake hukuntaki ai , dabanzo bafa? Wayasan me shashashancan zaiyi?"
Salma ta riko hannunsa, ya saketa ta kalleshi tare da hararrar sa tace "ji kunnena fa yanda yai jaa."
Salman yace " au bama amsa zaki bani ba?"
Salma tace " nafa d'auka kaine, to da aka kwankwasa kuma na duba banga kowa ba, nifa banma san sanda yashigo ba, sannan kai ina kaje?"
Salman yace " daga yanzu kidaina bud'ema kowa sai kinji waye."
Tace naji " amma kai fa ina kaje?"
Yace " ina kuwa naje?"
Ta mik'e tace " anfa cemin kun fita da Farha? Ni ina nan na d'auka wani abu mai mahimanci kake ashe kanacan ka biyema Farha kuna yawo, duk sanda nakawo kaina damaka magana akanta sai naga kamar bazaka ji dadi ba, sai dai nafara tunanin kamar ina cutar kainane nayin shirun danake."
Salman ya kalleta yaga yanda ta had'e rai, yace " oh ni Beauty kema fa ba sauki, irin wannan rufeni da fad'a haka? Kamar wanda nai wani laifi?"
Tace "au wannan ba laifi bane Prince?"
Tafad'a tare da mik'ewa, dasauri Salman ya ruko hannunta, ta fizge tare da cewa " bari in d'auko ma ruwa kasha magani."
Salman ya bita da kallo, yasani sarai tamai kara sosai akan Farha, to amma bata tsaya taji ma ya maidata ba, yana zaune har ta dawo, ta bud'e robar ruwan ta tsiyaya a cup sannan ta b'allo magungunan ta mik'amai, yana kallanta ya amsa yasha, ta rufe rowan zata juya Salman ya riko hannunta, ta jiyo ta kalleshi ta kuma kasa magana, Salman ganin yanda ta had'e rai yasa kawai ya rike kirjinsa yace "ahh Beauty kirjina"
Salma ta matso a rikice tace " jikin ne? Nashina, ko inkira likitan? Wayyo ni?"
Salman ya kalleta yai murmushi yace " kin hakura?" Salma tace "what? Au tsokana ce? Pillow ta d'auka ta makamai ya rike pillow d'in yace " patient ne fa?" Ta zauna tare da cewa "amma nikam Prince tunda kake ka tab'a cema wani sorry ko yi hakuri?
Salman yai shiru yace " badai saboda haka kike ta wani kara had'e rai ba?" Ta juya kai tace " ni na fad'ama? Yai dariya yace " dagaske kuwa saboda hakan ne" Salma ta mik'e tace " nidai ban fad'aba, ammm mai martaba fa yazo."
Salman yace haba? Tace " yazo naji kuma yace a kira Fulani da Ishaq." Salma ya mik'e zaune yace " bari inje Beauty. "
Tace to.
Salman ya mik'e tare da fita.
Sarki kam zaune yake shida Fulani da Ishaq, ya kalli yanda fuskar Ishaq tai luhu luhu dan duka, ya kuma kalli Fulani dan da alama itama yanzu taga fuskar Ishaq d'in ganin yanda taketa kallansa da b'acin rai.
Sarki yai gyaran murya ya sallami kowa ya rage saura su uku, ya kalli Ishaq cikin d'aurewar fuska yace " kai me kajeyi d'akin Salman, cikin ma d'akin matarsa?"
Dasauri Fulani takalli Ishaq, d'akin matar Salman?
Ishaq yai kasa dakai gabanshi sai fad'uwa yake, cikin in ina yace " Abba ni ban tab'a zuwa ma d'akin Salman ba."
Sarki yace " kai ni zakama karya? To dukan fuskar ka fa? Waye yamaka?"
Ishaq yai tsuru_ tsuru yace " uhm uhm...."
Fulani tace " haba mai martaba yazaka tambayi d'anka wai ko ya shiga d'akin matar kaninsa, yama za'ayi hakan tafaru? Ko gulma aka kawoma ai bai kamata ka yarda ba, inma ahi Salman d'in me ya fad'i haka to yayi karya dan kuwa Ishaq yafi karfin yaje kwartanci d'akin sa."
Ran Sarki ya b'aci wato dama duk wani so datake nunamai nasan Salman agabanshi karyane, Sarki ya kalleta cikin b'acin rai yace" kin tabbatar in nai bincike aka tabbatar da hakan duk hukuncin danamai sai ya shafeki, kuma ba matsala?"
Fulani tai shiru ta kara kallan Ishaq zatai magana taji sallamar Salman, cikin kid'ima suka juya duk su biyun , Fulani ta had'iyi wani yawo, Ishaq kam jikinsa ya shiga b'ari, Salman ya karaso ya zauna kusa da Ishaq, ya gaida Abba sannan ya kalli Ishaq sannan ya kalli Fulani ya gaidata, ta amsa a d'am tsorace.
Salman ya kalli Ishaq yace "yaya ya akai kaji wannan ciwon? Badai neman matar wani kaje ba aka ma dukan tsiya?" Ishaq ya kalleshi yana kif kif da ido yace" wani irin neman matar wani kuma?" Salman yai wani mugun murmushi sannan ya kalli Fulani yace " Umma d'azu na kama wani yazo har cikin d'akina yana neman la lata da matata, banga fuskarshi sosai ba amma nasan namai bugu mai karfi, yaza'ayi? da alama sai an tara mutan gidan nan an nemoshi dan bama tunanin zan iya kyaleshi."
Fulani a tsorace ta kalli Ishaq sannan ta kalli Sarki ta kuma maida idanta kan Salman tace " uhmm bai kyautaba kuwa ko waye."
Salman yace "good ashe kin gane umma, ke a tunanin ki ni namijin da zan yafe hakan ne?" Fulani ta kara had'iyar yawo da kyar tace " a'a ammq ya kamata ka sassauta tun balle in wanda yama laifin d'an uwanka ne."
Salman ya kalleta yad'anyi murmushi yace " inafa! Ai in d'an uwa nane ma shine bazan yafe ba, balle wanda ya shigo d'akin nasan shine wanda ya kusan kad'eni a titi matata ta tare."
Ai a tare zuciyarsu ta buga da karfi, Ishaq da sauri ya tsugunna yace " Salman dama ka ganni sanda na kusa bigeka shine ka ki fad'amin ko? Sannan matarka wallahi tunda naganta naji........" dasauri Fulani ta katseshi da karfi tace " ISHAQ"
Sarki kam Salman ya gama burgeshi, gashi ta hanyar sauki yasa Ishaq ya fad'i abinda ya aikata lalai ba shakka wannan inya zama sarki mutane zasuji dadi dan da alama bazai yarda da injustice ba kuma duk inda mutum yakai da boye abu zai sa ya sanar dashi ta hanya mai sauki, kallan Salman yai cikin tsananin so sannan ya kalli Ishaq da duk ya rud'e ya kuma kalli Fulani da ke hararar Ishaq ta gefen ido.