By Ayusher Mohd📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.3⃣8⃣
Salman ya jingina pillow shima ya kwanta, sunyi shiru na d'an wani lokaci, salma dai banda murmushi ba abinda takeyi, can taji salman yace kinsan me? Tace a'a.
Salman yace mahaifina da sarkin daya sauka wa da kani ne, mahaifina Alhaji Sadiq yataso cikin gidan sarauta sai dai tunda bashi zai zama sarki ba yasa zaman yafara gundurarshi, suna tsananin shiri da yayansa sai dai mutane kullum cikin gaima sarki gulmar Abba suke hakan yasa yanemi alfarma yadawo nan wudil garin mahaifiyarsa da zama, a lokacin Abba ya auri fulani dan alokacin 'ya'yanta biyu mata, itadai bataji dadin barin gidan ba, gashi tana fama da laulayi.
Dakyar ta lalabashi yabarta a kano akan inta haihu sai ta dawo wudil, bayan tahowar Abba anan garin ya had'u da mahaifiyata suka fara soyayya mai karfi harta kaisu ga aure.
Fulani taji haushin wannan aure sosai gashi sanda ake bikin ita kuma ta haihu, taji d'adin haihuwar namiji datai, d'an data haifa akasamai ishaq, nan gidan aka kawo mahaifiyata, tana tsananin san Abba, fulani kishi yasa tace sai dai tacigaba da zama a kano Abba yad'ingazuwa can, wannan dalilin yasa basu zauna tare ba.
Umma shekararta 1 da aure ta samu ciki, farin ciki agun Abba ba'a magana, mun shaku da Abba sosai harnakai shekara 9 sai dai umma batasake haihuwa ba sai bari, alokacin ne sarki ya aikoma mahaifina da takarda akan yanasan ganinshi.
Abba yashirya yaje sai dai yana zuwa ya taradda sarki ba lafiya sosai, cikin hawaye ya karasa yace meyasameka yaya? Ba wanda yasanar dani? Yace nasan bamai fad'ama shiyasa natura kazo, Abba yace meke damunka haka? Sarkin yace Abubakar inaji ajikina bazan wuce yau ba, cikin rudewa Abba yatambayeshi dalili? Sarkin ya mikamai takarda tare da kiran manyan mutane masu matsayin a masarautar yasanar dasu Abba yabawa mukaminsa da milki, ba Abba ba kowa yasha mamaki ganin yanada 'ya'ya maza, sarki yace asanda mahaifinmu yabani mulkinnan saidaya sa nad'au alkawarin zan baka kafin yabani, Abba jikinsa yai sanyi yaso yaki amma ganin yayansa na rokonsa yasa ya amsa.
Nida umma muna gida yau tunda umma ta tashi take kwance ba lafiya, in nace a kira Abba sai taki yarda, bayan magriba da Abba yakira sai ta d'aga ta nunamai lafiyarta kalau, nan yasanar da ita halin da ake ciki, ta tayashi murna kafin suyi sallama.
Jikin umma ya tsananta ga Abba kwanansa uku kenan dan washegari daya shirya tafiya sarki yace ga garinku nan, hakan yasa aka rikeshi yazauna.
Ganin umma bata ko iya mikewa yasa na d'au wayarta na fito falo na kira Abba,sai dai harta katse bai d'aga ba, nakirashi yafi sau nawa bai d'agaba, na ajiye wayar naje gun mai gadi na fad'amai, nan danan yakira driver muka wuce asibiti.
Abba kam alokacin suna zaman makoki, muna isa asibiti akai emergency da umma, duk ta rame, anan muka kwana,duk yanda nake kiran Abba bai d'agaba, waahe gari uku, a ranar da yamma aka shirya nad'a mahaifina, alokacin jikin umma yai tsanani, kuka nake sosai.
Wajen karfe d'aya mahaifina ya kira da sauri na d'aga yanacikin mutane, hakan yasa yace ku shirya za'azo a d'aukeku yanzu,dan da yamma za'ai nad'I,nace nad'I?cike da mamaki yace salman? Kaine? Nace Abba umma fa bata da lafiya inata kiranka, yace kuna ina? Nace asibiti yace ok bari azo yanzu a taho daku nace to.
Ba'afi hour daya da rabi ba aka turo mota babba ta d'aukemu, umma kam batasan meke faruwa ba dan bata hayacinta nikuma sai kuka nake, muna isa gidan dan Abba ya ganta kafin mu wuce asibiti, ina zaune rike da hannunta, tace salman? Ahankali na kalleta nace umma kin warke? Tace salman ka kula da mahaifinka, nace naam? Sai dai kafin takara magana naga tana wani abu😰.
salman na zuwa nan yai shiru, salma kam banda hawaye ba abinda take.
Can salman yace na fita da sauri akan in kira wani, ganin Abba na tahowa yasa nai gunsa da gudu na fad'amai, dasauri ya karaso sai dai muna zuwa mukaga umma tace ga garinku nan.
Hawaye ya zubowa salman yace kinsan me? Salma cikin tsananin tausayi da hawaye ta girgiza kai yace su fulani, da ragowar manyan mutane a gabana sukacema Abba wai abirne maganar mutuwar nan tunda sarakuna da manyan mutane suna gidan, a je kawai a mata wanka in ba haka ba mutane zasuce mahaifina da gawa ya fara a mulkinsa, salman ya rike kansa, salma ta mike da kyar ta matso inda salman ya kwanta hawaye na gudu a idonta, salman ya kalleta yace kinsan kuma me? Ta girgiza kai yace Abban ma ya yarda da maganarsu, shine daga baya ganin ina zaune sam bana magana yasa aka kaini paris gidansu farha.
Yana kainan yaji kirjinsa ya fara amsawa, jawoshi jikinta tai ta rungume tana kuka tama rasa me zatace, wace irin rayuwa salman d'inta yai? Tun yana karami an gama b'ata rayuwarshi da bakin ciki? Ganin yafara numfashi sama_sama yasa ta bude jaka tad'aukomai magani ta mike dakyar ta d'auko ruwa yana sha ta koma kusa dashi itama ta kwanta tarr da rungume salman, addu'a kawai takeyi, ahankali salman yaji numfashinsa ya daidaita, baccine ya fara d'aukarsa, salma ta kalleshi tace *I LUV U TOO MY PRINCE* kuma insha Allah I will take care of u😭.
Hmm soyayya oh ni indo nima tausayin salman ne yakamani sai kwalla naji a idona😭
By AYUSHER MOHD📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.3⃣9⃣
Farha ce tagama had'a kaya cikin hawaye ta jawo akwatinta, fulani dake zaune tace farha ke kuma meye hakan? Farha takarasa gunta tasa kuka, fulani tace ke da salman ne? Farha ta d'ago da sauri fulani ta kalleta tace nasan komai farha amma fad'a kuka?,farha cikin kuka tace sam bai damu dani ba matarsa kawai ya sani nikuma bazan juri ganinsu tare ba, fulani tad'anyi wani dariya tace haba farha mata da mijinta? Ai dole ki gansu tare kuwa, farha ta turo baki, fulani tai ajiyar zuciya aranta tace da alama nasamu wacce zata sa salman a koreshi, a fili tace kamar bakida wayau? Keda kika taso a kasar waje har matar data taso anan zata fiki sanin yanda ake jan ra'ayin maza? Farha tace duk nayi, kinsan halinshi ai😪fulani tace nasani to ba sai kibi ta hanyar dazaki shiga tsakaninsu ba? Inta fara zarginsa ko ya fara zarginta aikinga dole su rage damuwa a juna, farha tace wow nagane, fulani tace ko kefa?....
Nikam dariya ma sukaban da alama basu san basa gidan ba😂😂
Sunyi bacci sosai dan sai 4:30 suka tashi, salma ce tafara mikewa sai dai yanzu tafijin karfin jikinta, a hankali ta janye jikinta daga na salman ta mike da kyar tai hanyar toilet tai alwala, ta tada sallah salman ya mike, ya kura mata ido, a ranshi yace Allah nagode maka dakasa salma itace matata😊, Sannan ya mike yai alwala, salma ta dade tana rokon Allah yau kam duk addu'arta ta salman ce, bayan ta idar ta mike tai kitchen.
Kitchen din ta shiga dubawa, taga ba kayan abinci sai wasu ledoji akan dinning nan takarasa ta bude, take away ne, da alama salman dazu dasu ya shigo ta bude d'ayar ledar, kaza ce da dankali, sai dayar kuma lemo.
A hankali tadau ledojin takarasa kitchen ta dauko plates tafara wankewa, salman ya karaso inda take yasa hannu a kugunta tare da turo kansa ta wuyanta, yace beauty me kike? A ranta tace beauty? Ta juyo ta kalleshi da mamaki kafin tai magana ya manna mata kiss a kumatu, yace ba dream bane😉 murmushi tasaki sannan ta maida kanta gun wanke_wanken, tace andaina stubborn d'in? Kara kankameta yai yace sosai ma😊 ta turo baki ta juyo ta kalleshi tace ba wani bayan a wayarka haka aka sa? Yace oh ashe fa hakane, shan yace wait......kefa? Dasauri ta maida kanta tace umm nikam dama d'azu da abinci kataho? Baka fad'amin ba? Ya kwanta a bayanta yace inafa na tuna🤔? Ta gama wanke wanken ta goge dinning d'in sannan ta jera ta kalleshi tace abinci, yazauna tare da kallanta, itama tazo ta zauna a kujerar kusa dashi, ta zubamai abincin, nan suka fara ci,sai dai insuka had'a ido sai duk suyi murmushi, sun gama suka mike, salman ya kalli yanda take d'ingisa kafa, karasowa yai inda take kawai sai jitai ya d'agata da sauri takalleshi 😳 Ya juya kai tare da cewa tunda nina saki d'ingishi I have to take responsibility, tai murmushi tare da cewa ahh ni kunya nakeji🙈 ya fara tafiya tare da cewa toh yaza'ayi? Gashi nikima banasan mace mai kunya 🤔 dasauri ta bude ido, tace naa daina, dariya yasa tare da zama akan kujerar da ita, yakalleta yace wai daga fitata kikai duk wannan aikin?
Tace yayi yawa ne? Ko tayani zakai? Ya kalleta yace ahh sai dai inmiki sannu dan inaji tunda nake ban tab'a rike tsintsiya ba bare shara, salma tace na sani ai basai an kara sanar dani ba☹ ya ja kuncinta kad'an yace umm haka nakeso, tace bafa kayan abinci? Yace toko muje a siyo? Nikaina ina kwad'ayin cin abincinki, tace in kuma ba dadi fa? Yace anya kuwa? Bayan inaji ajikina ta iya? Salma ta mike daga cinyarsa tace yallabai muje? Tafad'a tare da kallansa, salman ya kalleta tare da had'e rai, tace menene kuma? Yace waye yallaban? Tace bafa suna bane☹kawai fad'a nai yanzu, yace au sannan ya mike yai gaba tabi bayanshi da kallo tace oh ni.
Sun shiga mota sun zauna salman ya d'au waya tare da yin dialling sai dai salma dake zaune taji wayarta na ringing awajen radio ta ajiye wayar a tare suka kalli wayar da salman sai dai me? *My Prince* yaga ya fito a jikin wayar, kallansa tai tare da saurin d'auke wayarta, yai murmushi tare da kunna motar.
Sunyi siyayya sannan suka koma gida, a falo suka zauna salman yakalli salma yace jikin fa? Tace da sauki, salman ya sauko kasa sannan yakalli salma dake kan kujera ya miko mata hannunshi, kallansa tai sannan ta mika mai nata,tare da sauka in da yake, sunzauna daf da juna dan rabin jikinta ma a jikinsa yake, hannu yasa ya kwanto da kanta jikinsa, ta gyara kwanciyar tare da lumshe ido, salman cikin magana mai rad'a yace baza'a fad'amin sunan nawa ba? Ta kara shigewa jikinshi, yai gyaran murya yace ahh nikam bansan mace mai kunya, salma tai shiru, ahankali yaji tace my prince🙈 yai murmushi tace ahh nikam banjiba🤔 tad'ago tace Allah kaji☹kiss ya manna mata abaki yace beauty daga yanzu kid'inga kirana haka, tace naam😳? Yace me? Bakyaso? Dasauri tace a'a bafa haka nake nufi ba, yace to me kike nufi? Tace sai dai in muna mu biyu, yace banyarda ba to in muna cikin mutane sai kice salman? Tace ahh ni? Yace to me zakice? Tace to ai in a cikin mutane ne bana fad'ar suna, yace ohh sai kice kai? Tace 🙊 ni? Ban isa ba, salman ya kwantar da kansa akan kujera yace shikenan.
Murmushi tai tare da sako fuskarta inda kansa yake tace zan d'inga fad'a kaifa? Yace wa? Ni? Ke kina tunanin ni zan kasa yin abinda naso? Tace ina fa? Rungumeta yai, salma tai ajiyar zuciya tace prince? Yace umm tace ban iya san abu ba, ina tsoron kar sanka yamin yawa in rasa ya zanyi? Kara kankameta yai dadi yakeji har ransa yace nabada dama kisoni harsai zuciyarki takai yanda bazaki iya rabuwa dani ba, tace I am afraid😞 ahankali ya d'agota yace of? Tace you, yace me? Tace eh, kara rungumeta yai baice komai ba, hawayen dasuka taru a idanta ne suka zubo.
By _```AYUSHER MOHD```_📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.4⃣0⃣
Bayan sunyi magrib, salma tai kitchen, salman ya kalleta tare da zama akan kujera, salma ta matso inda yake tare da mikamai remote tace ai kallo, ni zanyi girki, ya riko hannunta yace ummm sai yau zanci abincin matata kenan? Salma tace umm da alamu, sukai murmushi a tare salma tai hanyar kitchen,har lokacin d'ingishi take, salman yakalleta tausayi ya kamashi,ya taso yazo kusa da ita yace beauty na hakura, tace da me? Yace da abincin, kawai ki dafa mana indomie gobe kya mana girkin, tace me yasa😳? Yace kinga dare ne banacin abu mai nauyi kinsani, tai shiru, can tace to shikenan, ya shafa gefen kanta sannan yai murmushi ya juya.
Salma tai murmushi itama, tare da karasawa kitchen d'in, tafara had'a kayan hadin dazata dafa indomie d'in.
Salman na zaune yana kallo, najib ya kirashi, ya d'aga tare da cewa najib ya? Najib yace ina kuka gudu kai da amarya? Salman yace to d'an sa ido, waya fad'ama? Najib yace yanzu nazo ganinka naga farha ta fito ranta a b'ace ko kulani batai ba shine na tambayi bayin gun sukace bakannan, salman yai tsaki yace to tunda ka gama sa idan sai ka koma d'akinka ai, najib yai dariya yace oh ni prince wato yanzu soyayya ta rufe ma ido bama kunya abun? Salman yace oho dai kawai an wani kawo ma mutum bayi b'angare sam an hana mutum yasamu nashi privacy d'in, najib yace ummm da alama abin yafi karfina lalai salma taciri tuta, salman yace inkaji haushi kayi aure, yanakainan ya kashe wayar, najib yai murmushi yace naji dadi.
Salma ce ta jera had'adiyar indomie datasha vegetables ta ajiye lemo akan dinning sannan ta karaso inda salman yake, ta mikamai hannu,ya kalleta yai murmushi yace kanshi duk ya cikamin hanci🙂 tace um um fa banda kwad'I🤔 ya mike tare da dafo kafad'arta yace muje sai a tantance, sun karasa salman ya zauna tare da nuna ma salman kusa dashi, tai murmushi tare da zama, ta zubamai sannan tad'au plate zatasa nata, hannunta ya rike yace kisa spoon d'inki muci tare, ta kalleshi ya d'aga mata gira ta sa spoon d'inta nan, nan suka faracin abincin, salman na kai lomar farko ya d'ago ya kalleta tare da👍🏼 ta kalleshi yana had'iyewa yace wow delicious, ta d'an harareshi batace komai ba, aranta tace nikam prince yama surprising d'ina da hallayensa da da ban sansu ba, jitai yace what are u thinking? Takalleshi sannan tai murmushi, salman yaci indomien sosai, sannan sukasha lemo suka mike, salman ya rungumeta yace thanks 4 d meal, ta d'ago tace toh😳, yace ahh yakamata in rage ko?
Da sauri tace me? Yace my charm, ta d'ago tasa dariya, yace da alama kina mamaki, wannan salman ne? Anya kuwa? Ta kalleshi tace ni? Inji wa? Yasa hannu daidai zuciyarta yace nan? Tace ni dai banji sanda ya fad'a ba, salman yace dama bake aka fad'awa ba sakon dama ni aka fad'ama, ta kalleshi sannan ta saki wani murmushi.
Kallanta yai yace kada ki kuskura kima wani irin murmushin nan kuma, tace wani murmushi? Yace irin wanda kikai yanzu, tai murmushi tare da kama hannunsa tace muyi sallah mu kwanta, salman ya kalleta sannan suka wuce.
Sunyi sallah sannan suka shiga d'aki, nan fa aka fara kalan kalo, can salma ta daure tare da daukan kayan bacci tai toilet, salman ya bita da kallo, tana fitowa ta kwanta akan karamin carpet d'in dakin, salman ya kalleta sannan yatuna kalaman daya mata randa aka kaita, murmushi yai sannan ya karaso inda take, baice komai ba kawai hannu yasa ya d'agota, gaba d'aya ya d'agata takalleshi tace *my prince*😳 ya kashe mata ido sannan yai kan gado da ita, ya ajiyeta a hankali, ya matso saitin kunnenta yace banace munzama d'aya ba? Salma tad'an turo baki tace ba....bakishi taji a nata, a hankali ta lumshe ido, sannan ya saketa yace beauty munzama d'aya kuma ni yanzu bana tunanin zan iya bacci banjiki a kusa dani ba😉, kallanshi tai tare da murmushi wani sanyi ne ke ratsata, salman ganin tayi shiru yasa yad'an mike dan cire kaya, hannunsa ta jawo,yana tsaye ya juyo ya kalleta, ta lumshe ido tace thanks 4 saying that, ya lankwasar da kansa sannan ya saki murmushi har fararen hakoransa suka fito, salma ta kalleshi aranta tace niya kamata in hana wannan murmushin ai, salman taga ya sunkuyo yaja hancinta yace bari inzo, tace to, salman yakalleta sannan ya kalli hannunsa, sai a lokacin takalli hannunta, dasauri ta sakeshi tare da rufe ido, ya kara sunkuyowa dai dai kunnenta cikin rad'a yace da alama matarnan batasan mijinta ya matsa, salma tai sauri ta murgina, yai murmushi sannan ya bude jaka, anan ya cire kayansa, salma dai dama tunda ta rufe ido bata juyo ba.
By *_Ayusher Mohd_*📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.4⃣1⃣
Salman na gama shiryawa ya hau kan gado tare da jawo salma jikinsa, harta fara bacci, ya kura mata ido shikad'ai yasan me yake tunani a hankali yakai hannunsa gefen fuskarta ya shafa sannan ya sumbaci goshinta, shima ya kwanta, zuciyarshi sai kwad'aita mishi sha'awar salma ya daure ya tuno wahalar dasha, ahankali ya rufe ido,yana tunani baisan sanda bacci yai gaba dashi.
Sai asuba salma ta bude ido, tare da kallan salman, murmushi tasake tare da mikewa, balaifi taji saukin jikin ba kamar jiya ba,tai alwala tana fitowa salman ya bude ido cikin kalar bacci, takaraso inda yake ahankali tace ka tashi? Lumshe mata ido yai alamar eh, tace amma kamar ba masallaci a kusa ko? Naga ba gidaje, ya kalleta sannan yakara lumshe ido alamar eh, tai murmushi tace to ka tashe sai muyi sallar? Yai shiru kawai yana kallanta, ta sunkuyo tace kanaji na? Rigarta ya jawo ta fad'a jikinsa, ahankali yace a taimaken a d'agani nakasa tashi, mikewa tai tace ohh pretending? Yai shiru tare da d'aga mata gira, ta mike tare da kamo hannunsa, ahankali ya d'ago ta taimakamai ya tashi, yana mikewa yace tnx beauty☺, tace oh zaka iya tafiyar ashe, ya kalleta sannan yai murmushi yai toilet ta kalleshi tare da tada sallar nafila, tare sukai sallah sunyi adduo'I sannan salma ta kalli salman tace yaushe zamu tafi? Yace ina? Kin kosa ne? Dasauri tace a'a, yasa dariya yace baki kosa ba? Ta mike tare da kwanciya tace nidai yau inaji tsetse fly ne ya cijeni bacci nakeji, salman ya mike yazo ya kwanta kusa da ita, salma ta kamo hannunsa ta rike tare da kwanciya akan kafadarsa, bacci mai dadi ne yai gaba dasu.
Farha kam tun jiya tashiga d'aki bakin ciki ya hanata fitowa, da safe fulani taje d'akin tace wai farha meye hakan? Farha tace bafa sannan☹fulani tace an fad'amin to shine me? Farha ta kalleta da mamaki tace fulank kinfa san......fulani takatseta tace farha kidaina bani kunya mana, zan miki abu d'aya, zansan yanda zanyi salman yadawo yau ke kuma sai kisan yanda zakiyi ki aureshi.
Farha ta mike tace fulani salman nawa ne tun ina yarinya nasan da haka, ko saurayi nai bana kawo auransa araina salman kawai nake hange, fulani tai murmushin mugunta da alama tasamu wacce zatasa amaida salman kasar waje batare da tayi komai ba.
Salma karfe 9 ta tashi, a hankali ta zare jikinta daga jikin salman tai kitchen, dankali ta fara ferewa nan ta fara had'a kayan potato omelette d'in datake san yi, tana gamawa ta sa tafashen naman da suka siyo na sa, bayan ya tafasa tayanka sirara ta hada da karas da tarugu da albasa tai pepper meat.
Babu abinda kakeji a gidan sai kanshi, ruwan tea ta dafa ta ajiye a dinning,ta gama ta wanke hannu ta wuce toilet, tana fitowa sanye da towel, salman ya bud'e ido, cikin tsoro ta kalleshi😳, tunanin jiya ne ya fad'o mata, salman yai murmushi sarai ya gane, wata sha'awa ce ta tasomai, yq daure bai ce mata komai ba yai toilet, tabishi da kallo sannan tai ajiyar zuciya.
Kaya tasa doguwar rigar material ce ta mata kyau sosai ta tufke kanta bata d'aura d'ankwali ba, salman ne ya fito, ta kalleshi tace muje muyi break, tafad'a tare da matsowa kusa dashi, hannunsa yasa a nata yace harkin had'a mana? Tace eh, yace wooo I think shI yasa naji kanshi a cikin bacci na😎 takalleshi tasa dariya tace ko? Ya maze tace kamar kuma ba haka ba😏, ta turo baki ta kalli gefe, murmushi yai tare da janta, suna zuwa dinning ta bude potato omelette d'in salman yace wow not bad😉 ta hararreshi tare da rufewa, yace to in nace ya burgeni ko da gani zai dadi sai ki kushe shiyasa nima nace haka, tace amma ai.....yace naji amma a bani abinci inaci sai muyi maganar, yafad'a tare da budewa, wuka tasa ta yanka ta d'auramai a plate, yace kai abinnan ya burgeni, naman ta mikomai sannan ta had'amai tea, yace oh karfa dad'I yamin yawa mukoma ince nisai abincin matata🤔, tace nikam bazamu iya zama anan ba?
Ya kalleta tare da sa abinci abakinsa yace tun kafin nai aure naso nabar gidan sarauta sai dai bansan meyasa Abba yake hanani ba, salma tai murmushi tace hala yafisan yaganka a kusa dashi ne, kallanta yai bai magana ba kawai ya cigaba dacin abincinsa, itama shirun tai.
Sun gama ta kwashe kwanuka ta wanke sannan ta taho falo, salman na gamawa wanka ya shiga, salma na zaune a falo tanajinshi yana waya batadai san me yake cewa ba, salman na fitowa ya kalleta rai a b'ace yace ki shirya mu koma, da sauri ta mike tazo inda yake tace my prince😳? Bam gane ba? Ya dafata da hannayensa biyu yace wai fulani ce ba lafiya, salma tace naam? Yai murmushin yake yasan rainin hankali ne in bata da lafiyan bakowa a kusa da ita ne? Wai amma waziri ke cemai fulani nata cigiyarsa😠, salma tasan baiji dadi ba tarasa mai zatace mai itama, can ta daure tace bakomai ai zamu iya zuwa wata rana, salman ya rungumeta sosai yace nafisan inganni daga ni sai ke banasan bayin nan, tad'ago a hankali ta kalleshi tace yazamuyi? Salman a hankali yakai bakinshi nata wani salo yake mata wanda yasa ita kanta ta rikice, batasan sanda tafara maidamai ba, cikin d'akin suka shiga sosai, kai da gani kasan basa hayaccinsu.
Nikam ganin haka yasa nai baya, kar salman ya makomin harara, kofa na rufe musu......🚶🏻🚶🏻🚶🏻
Ishaq ne zaune kusa da fulani yace umma me kike shirin had'awa? Ta kaleshi tace name? Yace kinzo kin kwanta kina wani kiran salman nk banfahimceki ba, ta kalleshi ta nunamai ya kori bayin, nan ya korasu ta mike tace kaifa kanka baya ja, ishaq yace zaki fara ko umma? Fulani tace so nake ya dawo, kasan sunyi tafiya da salma? Dasauri ya mike yace what? Umma yazakumin haka?yazaku bar salman yai ta.....fulani tace ai kajika, to ni so nake ya dawo, akwai shirin damuke da farha, ishaq yace dafatan shirin bai shafi salma ta ba? Tace salmar ka? A ina taxama taka? Yace nidai nasan tawace ba kuma abinda yadameni da wani shirinku,nikaina inasan a kori salman amma kar abin yashafi salmata, fulani ta mike rai a b'ace har zatai masifa sai kuma ta tuna yanzu inta mai fad'a kila yaki bata had'in kai hakan yasa tace to in farha ta auri salman ba sai tasa yasaki salma ba kaikuma kaga ai kasamu chance, ishaq ya washe baki yace kumafa hakane, tace kokaifa?
Nace zancen kuke so😏aikin kawai😗.
Salma kam batasha wahala sosai kamar jiya ba, yau kam tare sukai wanka sannan suka shirya, salma na tsaye jikin madubi tana gyara gashinta, salman yazo tabayanta ya tsaya, takalleshi tacikin madubin tai murmushi a hankali yace sannu beauty, murmushi tai batace komai ba, gashinta ya shafa yace beauty tace naam? Tare da juyowa, yace zan tada mota inzo, tace kacema mai gadi yazo ya fita da sauran kayan abincin da muka siya tunda bamusan ranar dawowar mu ba yace ok👌🏻.
Ya fita a ransa shikad'ai yasan irin bakar maganar daya shirya fad'ama fulani zatai dana sanin sashi ya dawo, yasani sarai munafurcine amma bayasan su waziri susan basa shiri.
By *_AYUSHER MOHD_*📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.4⃣2⃣
Salma ta gama komai sannan ta rufo gidan tare da karasowa gun motarsu, salman na zaune tunda ta fito ya kura mata ido yana kallo, haryanzu a hankali take tafiya, shikam yana mamaki yanda yake jin shaukin san salma, nai tab'a tunanin akwai maccen dazaiji ta a ransa kamar haka ba.
Salma ta bude motar ta shiga, kallansa tai tare da matsowa ta hura masa ido, salman ya kalleta tace tunanin me kake? Ya lumshe ido yace shine ai, tunanin me nake? Tai murmushi tace muje? Ya kalleta tare da tada jan motar.
Sun d'au hanya, wayar salma tai kara, salman ya kalleta tare da kallan wayar dake hannunta, numberce salma ta kalleshi itakam ta gane number dan number kamal ne, a hankali ta d'aga tace yaya kamal? Kamal daga can yace salma ya kke? Salma ta kalli salman tace lafiya, kamal yace to ya gidan? Zatai magana taga salman ya miko mata hannu, alamar ta bashi wayarta, mikamai tai batare da tayi musu ba duk da a ranta batasan yacima kamal mutunci, salman ya kai wayar kumnensa daidai sana kamal yakara cewa salma ya gidan? Kinyi shiru ko dai......salman ne ya katseshi yace d'an rakiya? Kai ne? Haushi ya kama kamal yace malam kanwaa nake nema ba kaiba😠, salman yai murmushi yace d'an rakiya a ina kasamu number matata? A iya sanina baka da ita, kamal ya cije lebe yace meya dameka? Salma dai kanwatace, salman yai dariya yace okay tunda haka ne bari na kira Abba nasanar dashi irin so da kulawar dakake ba kanwarka kaga sai a maka kyauta😏, kamal yace cemaka nai ka fad'amai? Yafad'a tare da saurin kashe wayar, salman yabi wayar da kallo sannan ya cillama salma wayar.
Ta kalleshi tace ka kware a gun iya fad'ar bakar magana, salman yakalleta yace haushi kikaji? Dasauri tace ni? A'a, yace warning namai at least nasan he is smart zai gane mai nake nufi, salma ta murmushi ba shakka yanzu tasan salman na kishinta sosai.
Farha, fulani da ishaq zaune a kilisar fulani, farha na zaune a kasa itada ishaq, ta kalli fulani tace fulani sun taho? Fulani tace hb nasan sun taho tunda tun d'azu akama salman d'in magana, da alama yakamata inshiga d'aki in kwanta, farha tace yaya ishaq dan Allah so nake ka nemomin maganin bacci mai karfi, ishaq yace dafatan ba salma zaki ba ba? Tace haba yaya ina na isa? Yace zan turo akawo miki yanzu, ta kalli fulani sukai murmushi.
Suna isa gida sukai b'angarensu, bayi nata gaidasu, salman na shiga ya wuce toilet, ya watsa ruwa tare da d'auro alwala, yana fitowa itama tashiga tai wanka tai alwala, hanne ce tai knocking tasanar dasu an kawo abinci, salma dake tsaye ta kalli salman, ya jawo ta jikinsa ya rungumeta tana daga tsaye, salma tace abinci? Yace not now, ni abinda naci d'azu mai dadi bai bar cikina ba, salma tai murmushi, salman ya kamo hannunta ya zaunar da ita, sannan ya kwanta akan cinyarta, ta shafa kansa tace bacci? Yace eh beauty, tace tunda ka yi sallah, salman yace beauty? Tace naam? Yace bana tunanin zan iya bacci ba'akusa dake ba, salma ta kara shafa kansa sannan tazo daidai saitin kunnensa tace naji dadi, murmushi yai tare da lumshe ido, ita kuma tana shafa sumar kansa a hankali.
Salman bacci yake sosai, salma ta kura mai ido tana kallanshi, itakanta tasan sanda takema salma yamata yawa, tana zaune tana tunane_tunane har itama tafara bacci, sai wajen 5 salman ya mike tare da kallan salma data jingina da gado tana bacci, mikewa yai ya gyara mata kwanciya, tare da rufa mata bargo sannan ya fita.
Salman kam yana fitowa, yaga wasu fadawa biyu a kofarsa, suna ganinshi suka taho da sauri, suka gaidashi, yace menene? Sukace fulani ce tace musanar dakai tana jira, kallansu yai yace kuce ta jira inada uzuri tukun zan shigo😏, yai hanyar mota ya barsu anan, suma suka juya dan kai sako, fulani ta kwanta a gado ta daddage tana kakaro numfashi irin wacce takejin jiki d'in nan, tad'auka zataga salman, sai dai jitai ance wai yanada uzuri, bakin ciki ya isheta ta tashi zaune tare dayin kwafa, lalai itama ta kosa ai maganin d'an iskan yarancan.
Salman dama da saninsa ya fita daga gidan, gidan najib yaje Amir ma na gidan, nan suka shiga tsokanarshi wai ya honeymoon d'in nasa? Salman kam murmushi yai yace matsalarku duk jin kwakwaf d'inku yau sai dai ku hakura dan bazakuji komai ba🤔.
Salma bayan ta tashi,ta fita falo taci abinci sannan takira salman, ringing uku ya d'aga tace prince ka fita bakaci abinci ba? Ya kalle najib da Amir da suka matso kusa dashi dan jin kwakwaf, dasauri yace zan kiraki anjima ya katse wayar, salma tabi wayar da kallo tare da mamaki.
salman kam kallansu yai yace da alama nakusa daina zuwa nan tunda kun koma 'yan sa ido, dariya sukai sukace yarima kaga yanda kafara canza wa kuwa? Salman yace bansan iskanci, ba wani canzawa, Amir yace ga hasken Amarci nan😃 salman ya girgiza kai tare da mikewa yace mu fita ko? Sukace kai ya kamata dama an dade.
Salma kam duk gidan ba dadi haka tai tajinta, takosa salman ya dawo, waya tad'auka kamar ta kirashi sai kuma ta fasa tunda shi yace zai kirata.
Salman kam sunje yawo sai 9 sannan ya kamo hanya, waya ya d'aga yakira salma, da sauri ta d'aga, salman yace kinjini shiru ko?tace ina kashiga? Yace ina tare dasu najib ne sun takuramin, tai murmushi tace ka taho? Yace eh ganinan, kinyi missing d'inane?tai shiru, yace ohh da alama dai, tace kaje dubiyar? Nima inasan shiga amma bansan zuwa ni kad'ai, salman yai wani murmushi yace nakusa isowa nan da 5 mins ki fito sai mu shiga tare tace to sai ka iso, nan sukai sallama ta mike tare da d'an gyara fuskarta ta yafa mayafi ta fito.
Daga nesa ta hangoshi shima haka tun daga nesa sukema juna murmushi a hankali suka karaso kusa da juna, salman ya kalli salma, sannan ya kalli bayin dake biye da ita ya d'an sukunyo kad'an yace har naji relief dana ganki, murmushi tamai mai kashe zuciya, shima murmushin ya mata suka karasa b'angaren fulani.
Farha ta had'a juice d'in abarba ta zuba maganin bacci tun d'azu suna jiran salman sai dai salman shiru hakan yasa tasa a fridge, tai d'aki tana kokoni.
Jin sallamar salman yasa ta fito da sauri, sai dai tai turus, ganin salman da salma a kilisar fulani su biyu, salman yasa hannunsa a kugun salma tana ture hannun tana cewa prince a b'angaren fulani muke fa🙊? Salman yace to sai me? Ya matso daf da ita yace u are my wife, farha ta cika tai fam, tayi gyaran murya tare da karasowa, atare suka kalli gun salma ta had'e rai ganin farha, shima salman d'in fuska ya d'aure, farha kam aranta tace kyalesu,kin manta...hakan yasa ta saki murmushi takaraso tace yayana? Ina kashiga? Salman ya kalleta yace farha dama kinanan? Tad'an bata rai tace yaya yazaka cemin haka🙁? So kake intafi? Salman yace ba haka nake nufi ba, ina umma? Takalli salma tace sannu in_law, sannan tace yaya muje tana d'akinta, salman ya kalli salma yace beauty muje ko? Salma tai murmushi tare da d'aga kai, farha ta maimaita beauty? Tasan beyi karya ba amma kishi duk ya kara cika ta.
Suna shiga d'aki sukaga fulani a kwance cikin bargo, dama tunda taji sallamar salman tai saurin rufuwa, salman yakaraso kusa da ita da sauri, yace umma? Jikin ne? Fulani ta saki numfashi tare da d'aga kai, salman yace ayya sannu, har magana bakya iyayi? Ta kasa dakai, salman zai magana yaji muryar ishaq yana cewa umma kina d'aki ne? Yafad'a tare da bankad'a labulen d'akin,ganin salman da masoyiyarsa yasa ya had'iye maganar dayake shirin yi, yakalli salman yace ashe ka iso? Umma sai nemanka take, salman kam ba shakka yasan pretending ne daga yanda yaji ishaq yai magana daya shigo, amma a fili yai murmushi yace ba dole in dawo ba tunda umma ta matso tanasan ta ganni, da alama dai tafisan taganni akanka, ishaq yacd ban gane ba? Salman yace ni danake wani garin? Tunda tasa akirani ai kaga ta kosa ta gannine, ishaq ya d'aure fuska, salman ya kalli ishaq yace umma najin jiki yaya, ishaq yace sosai ma, salman yace ayya, dama haka ne, in mutum ya dade bai yi cuta ba ai da alama sai ya duba ibadunsa, ishaq yace bangane ba, salman ya kalli fulani sannan yace dama ba kowa bane zai gane😏, ran fulani dake kwance ya b'aci wato da ita yake ko wa? Abinciki ibadunsa? Sannan ta matsu ta ganshi? Salman ya kalli ishaq yace yaya ka kula da umma plz kar mu sake wani rashin😞 salma kam kallan salman kawai take tana mamaki mutum irinshi, sai magana cikin magana yake kwaba musu kuma fuskarsa d'auke da murmushi.
Farha ce tad'an taba fulani, salma na kallanta, salma sai ji tai fulani cikin dakucewar murya tace salman inasan magana dakai, salman ya kalleta sannan ya nuna kansa yace ni? Ta d'aga kai, farha da sauri takalli salma tace mu basu guri ko? Salma tace eh tafad'a tare dayin waje, farha tai murmushi.
Salma na fita ta kalli farha sam batasan zama da ita hakan yasa tace ni nayi gaba bansan how long hirar tasu zata kaiba, farha tace to in law, dama haka suke so, salma ta juya tanajin farha tad'anyi wani shewa itadai tai gaba.
Salman na zaune farha ta kawojuice, salman ya kalleta sannan ya kalli fulani yace ya akai? Fulani takalleshi tace salman kayi hakuri nasan kaji haushi danasa ka dawo,salman yace haushi? Wa? Ni? Fulani ta tsani rainin hankalin nan, tadaure tace to kasha lemon mana ko kana tunanin nasa ma wani abu ne? Salman yace wai umma meke damunki? Ban gane kinsa wai abu ba? Fulani ta zubo da kwalla, tace salman na sani bana kyautamaka kayi hakuri dan Allah, salman ya kalleta tare da kallan farha data zuba mai juice d'in tace yaya nina had'ama special, ya amsa tare da kurbar kad'an yace farha bansanki da haka ba shine kika ki d'aukowa tun matata tananan? Tace laa wlh mantawa nai, akwai dayawa inzaka tafi zan bada akaimata ko ibika dakaina in kaimata, salman yace gwara ki hada d'in dai bawai ki bini ba, yafad'a tare da shanye na cup d'in.
Farha ta kalli ishaq sukai wani murmushi salman ya kalleta yace meye.....sai dai ganin dishi_dishin daya fara yasa yai shiru, ai bai kara magana ba ya tun tsere agun, farha tasaki dariya suma haka, nan ishaq ya taimakama farha suka kai salman d'akim farhan suka kwantar.
Salma kam tana d'aki a tsaye, ganin har 11 shuru ba salman tsoro ya fara kamata kawai ganin text tai a waya, "am sry beauty, zanyi dare ki kwanta".
Da mamaki takara maimaita text din, hartayi cilli da wayar sai kuma ta d'auko, tare da kara karanta text d'in, zanyi dare? Ki kwanta? Salman d'in? Nan rayuwarsu ta jiya da yau tashuga fad'o mata, ta tuna a yanda tasan salman ba abinda zai zaunar dashi acan,tuno sanda farha ta taba fulani tai sannan shewar dataji farha tayi, dasauri ta jawo mayafita wajen 11:30 tai waje, su hanne basu masan tafita ba.
Farha kam tanacan tana murna harta hango an fad'ama sarki salman ya kwana da ita, ai ba makawa sai aure.
Nikam dariya ma taban dasauri nabi salma ganin tana zuba sauri.
*Masoya littafin nida prince kuyi hakuri plz jiya da yau bansamu na turo 2 pages ba kamar yanda nasaba, hakan ne yafaru saboda wani uzuri nawa.*
*Mutane sunmin complain akan hakan, kuyi hakuri amma insha Allahu gobe zan cigaba da turo 2 pages.*
Ayusher Mohd📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.4⃣3⃣
Salma na zuwa tai hanyar d'akin fulani, bayin suka tambayeta,salma ta kallesu yace farha fa? Suka nuna mata hanyar d'akinta, salma ta kallesu sannan tai d'akin farhan, batasan meyasa jikinta ke bata farha ce ke shirya wani abu, salma takarasa jikin kofar tare da knocking, farha da ke kwance kusa da salman ta kalleshi sannan ta mike, tace waye? Salma bata amsa ba, hakan yasa farha tai tunanin ko fulani ce, farha ta bude kofar.
Ganin salma yasa ta zaro ido tare da janyo kofar, sai dai kafin takarasa rufewa salma ta hankad'a kofar da karfinta,😰😳 ganin salman a kwance ya baje yasa jikinta ya d'au rawa, gashi an cire mai riga an barshi da vest, wani mugun kishi ne ya taso mata, ta shiga d'akin rai a b'ace, farha kam jikinta sai b'ari yakeyi tai hanyar kofa da alama so take ta fita, salma na ganin haka tasa gudu ta rigata zuwa kofar ta datse da makulle sannan ta zare makullin, ta watsama farha wani kallo sannan takarasa gun salman.
Cikin kishi ya tabashi tace malam mike, tana fad'a hawaye na zubo mata, jin salman yayi shiru yakuma cigaba da baccinsa yasa haushi ya kamata ta jijigashi da karfinta kamar mahaukaciya tace malam ka tashi nace, sai dai salman taga ya koma duk abinnan datake wai bacci yake, tsoro ya kamata kardai mutuwa yai, kallan farha tai dake rakube a jikin bango tana tunanin abinyi, salma ta karaso gunta tana zuwa ta kalleta tace me ya sameshi😠? Farha ta hadI'ye wani yawo tace me yasameshi kuwa banda soyayyarmu da muka tuno? Batai auni ba taji salma ta kifa mata mari, farha ta rike kuncinta tace are u crazy? How dare yo.....salma ta kara mata wani ta d'aya kuncin, farfa ta zabura itama takai hannu, salma tai caraf ta rike hannun, tace baki kai matsayin marina ba, farha tace what? Salma ta kalleta tace farha karkiyi tunanin abinda kike yi tsorone yasa nake kyaleka a'a tausayin ki nake akan kina san maso wani, kuma bari in fad'a miki salman nawa ne wannan kalmar ki ajiyeta a cikin zuciyarki, farha kam jitake kamar ta mutu, salma ta kalli salman sannan ta kalleta tace magani kika samai ko? Farha ta fizge hannunta tace babu wani namiji dayakai matsayin insamai magani,sannan salman shi yakawo kanshi d'akin nan saboda ni, zancen salman nake ne wannan hasasshenki ne kawai, kuma kiyi gaggawar barmin d'aki yanzun nan.
Salma ta kalleta tasa dariya tace farha yanda naga alama kamar kanki ba d'aya ba, kinaso kicemin salman neman mata yake ko me? Sannan ke da ake nema kece idanki biyu shikuma mai neman har ya gama biyan bukatarsa ya kwanta? 😅 me kike tunani? Ni yarinyace? Ko kuwa 'yar kauyen dabatasan komai ba? Farha ta ce oho wannan matsalarki ce amma nidai kibarmin d'aki, salma ta riko wuyanta ta kaita bango tace zan buga miki last warning koda wasa kada ki kuskura ki kara had'a mijina da mazinaci, dan wlh I won't tolerate that.
Salma na gama fad'ar haka ta sake farha tare da karasawa gun salman, duk yanda ta jijigashi bai mekeba, haka kuma duk yanda taso ta d'agashi ta kasa, hawaye tasa tana jijigashi sai dai ina.....?salman baisan ma tana yi ba, gashi ba damar tanemi taimakon wasu kar a gane.
Salma ta sauko daga daga kan gadon, ta kalli farha tace is not a bad idea hakan da kikai, farha dake tsaye rike da kugu tace what? Salma ta karaso inda take tace canjin gurin kwana, farha tace mekike nufi😡? Salma tace ahhh me nake nufi? Nufina kibar mana d'akin mu kwana, farha tace me kika ce? Salma tace ohhh baki ganeba? Nufina ni da mijina😏 da alama ciwon fulani yasa mijina cikin damuwa shiyasa ya nemi mukwana a b'angarenta, farha tace ke me kike tunanin yi? Salma ta jawo hannunta tace kije ki kwanta ko a kusa da fulani ne mu zamu rufe d'aki🙂.
Farha jitai kamar ta shake salma ta kashe wani bakin ciki ne ke yawo akanta, a iya tarihin rayuwarta tana tunanin yaune rana ta farko da aka tab'a ci mata mutunci irin na yau, haka ta fita daga d'akin cikin tsananin bakin ciki.
Salma tai ajiyar zuciya tace dama inada zafi haka? Tafad'a tana kallan salman?
Karasawa tai ta kwanta kusa da salman ta shige jikinsa wasu zafafan hawayene suka zubo mata, ba shakka wannan abun da fulani aka had'a plan d'in amma wannan wace irin tsana ce? Kara shigewa jikisa tai tace *I WILL PROTECT YOU MY PRINCE*.
By AYUSHER MOHD📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.4⃣4⃣
Farha da gudu tai d'akin fulani tana hawaye, fulani kam harta fara bacci, ta mike zaune tace waye wannan?farha ta karasa cikin d'akin, fulani ta kunna fitila, ganin farha yasa tace farha ke kuma menene? Farha kam kuka take, fulani tace meye hakan zakizo kisani a gaba kina min kuka? Farha tace fulani salma ta ruguzamin plan d'ina😭, fulani tace ban gane ba? Wace salman? Farha nan ta shiha zayane mata sai dai bata fad'a salma ta mareta ba😛, ran fulani ya b'aci ta kalli farha bakin ciki da haushin salma yakamata, farha tace yanzu ni da wani idon zan kalli yayana? Fulani ta zuciya tace to ko kin hakura da auransa? Farha tace ban hakura ba, zuwa zanyi gobe infad'ama sarki ya auramin salman ai yayan mahaifinane, fulani tai tsaki tace ke a tunaninki sarki zaiji maganarki yabar ta d'an daya haifa? D'an ma kuma salman? Farha tace fulani yazanyi to? Fulani tace kibari yanzu gobe kiga mai shi salman d'in zai yi, farha tace to, fulani tace ki kwana anan gudun magana tace to.
Salma kam ta dade batai bacci ba, tunani sun cika mata kwakwalwa, sai can cikin dare batasan yanda akai bacci yai gaba da ita ba, hartai sallah, salman bai farfad'o ba, ta shiga tasbihi, sai 8 sannan salman yai juyi, a hankali ya bud'e idansa tare da sa hannu a kai, jin kan yamai nauyi, salma dake zaune tana tasbihi ta mike da sauri tare da hawa gadon, salman ya mike zaune tare da kallan d'akin, me ya kawoshi nan? Dream ne? muryar salma yaji, ta taba shi tace prince ka tashi? Salman ya kalleta sannan ya kara kallan d'akin, dasauri ya diro daga kan gadon ya kalli salma yace me muke anan? Ta kalleshi ta daure sannan ta kakaro murmushi tace kamanta? Jiya anan muka kwana ai😊salman ya kalleta yace what? Sannan ya ka kalleta yace anan? Tace eh mana yai murmushi yace Do u expect me to believe that? Yafad'a yana nuna kansa, kallansa tai takasa magana, agogon bango dake d'akin ya kalla, 8am? Nan ya tuno shidai yasan an kawomai juice daga nan bazai iya tuna komai ba, dasauri ya matso kusa da salma, ya rike kafad'unta yace beauty? Hawayen datake b'oyewa ne suka zubo, ya kalleta yace me yafaro? Ki fad'an gaskiya, salma ta kalleshi tace ba abinda yafaru, salman ya rungumeta a jikinsa yace bakyaso raina ya b'aci ko? Ta d'aga kai yace amma karki manta nace mu daina b'oyema junanmu komai, salma tai shiru can tace maganin bacci aka sama, dama jikinshi ya bashi yai ajiyar zuciya yace anso amin sharri kenan? Ganina anan ba riga, salma tai shiru, salman ya kara kankameta yace and u protect me ko? Salma dai hawaye ke zubo mata, d'agota yai yasa harshe ya lashe hawayen dake zuba a idanunta, salma kam lumshe ido tai.
Salman ya kalleta bayan ya gama yace beauty banason hawaye su dinga zubowa daga kyawawan idanun nan naki, ta bude ido a hankali tana kallanshi, yace don't worry this time I will take care oh them, ya fad'a tare da saketa yace mu fita bazan iya sallah anan ba, salman yad'anyi gaba tare da zura rigarsa, a zahiri ji yake zuciyarsa kamar zata fashe dan bakin ciki, amma yana tunanin in ya nuna gazawarsa ya salma zatai? Wayasan jiya ya tai? Hamdalla yai, lalai shikam yaji dadi samun mata kamar salma sai an tona.
Sun fito harsunyi hanyar fita salman ya kalli salma yace beauty muje muga fulani, ta kalleshi tace da saffen nan? Yai murmushi yace ke kina tunanin jiya sun yi bacci? Tunda kin wargaza musu plan? Kasa tai da kanta, nan sukai d'akin fulani.
Ai kam fulani da farha tunda sukai asuba basu samu bacci ba suna zaune suna tunanin me zasu shirya gaba, salman yai knocking fulani tace waye? Salman bai magana ba ya tura kofar, fulani na zane a kan kujera farha na gefenta kad'an, salman yai murmushi ba shakka tare suka had'a, bai taba tunanin farha haka take ba, kallan kofa sukai a tsorace farha take kallan salman amma dayake fulani ta kware tace salman shigo mana, kofa ya kalla tare da cewa beauty ki shigo mana, salma ta shigo d'akin, salman ya kalli fulani yace umma da alama miracle ya faru? Tace name fa? Yai murmushi yace hmm jiya mun kwana anan saboda ke ashe ke kuma sauki har ya iso jikinki😊 fulani ta maimaita kalmar, mun kwana? Lalai yaron nan, salman ya kalli fulani tace baki tambayeni ya kwanan jiya ba? Fulani ta daure tace ya kwanan jiya? Salman yace eh to ba dadi dai, wasu miyagun mutane ne suka kawo min hari? Fulani ta kalleshi da mamaki, salman yai murmushi tare da kama hannun salma yace karki damu umma, ai matata jarumace ita tai yaki dasu, fulani ta makama salma harara, salma ya kula hakan yasa yace zan isar da sako, fulani tace name kuma🙄? Salman yace ki sanar da miyagun mutanen nan in suka kuskura koda wasa suka kara tunanin aikata abinda sukai, sai kuma yai wani murmushi yace umma bansan mezan musu ba dan wlh I won't tolerate it, ba fulani ba, ba farha ba, itakanta salma sai data kalli salman jin yanda ya karara maganar.
Ya kalli salma tare da mikewa yace beauty muje ko? Yafad'a tare da mika mata hannu, mikamai hannu tai cikin sanyin jiki ta mike, sun fara tafiya harsun je kofa su farha da fulani sun kafe kamar gunki, salman ya tsaya sannan yace ahhhh, tare da juyowa farka kam zuciyarta tagama tsinkewa, salman yace umma kisanar da mutanen nan duk Wanda ya taba matata sai kuma ya furzar da iskar bakinsa, yai kwafa kawai yai waje, salma suna fita ta rungumshi,salman ya d'agota yace beauty menene? Tace wait...1 min, salman ya dagota yace muje kin manta mijinki baiyi sallah ba? Takalleshi tace wani irin warning ne wannan? Ni wlh kamar ni kakewa, duk na tsorata, yai murmuhsi yace kyalesu muje kinji, tace to.
Farha kam da fulani sun dadw ba wanda yai magana fulani sai fila fila take da maganar daya gama dankara mata, itakam har kasan ranta tsoron salman da kwarjininsa take , farha kam jikinta gaba daya ya kame, itakam tad'aukama ta mutu ne.
Ohhh *SALMAN*
BY AYUSHER MOHD📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.4⃣5⃣
Bangarensu suka karasa salman bai magana ba, toilet kawai ya fad'a yai alwala, bayan yayi sallah ya mike tare da kallan salma dake zaune akan kujera da alama tunani take, murmushi yai sannan ya karaso inda take, a gabanta ya tsugunna ya kamo hannunta da sauri ta kalleshi, yace me beauty take tunani haka? Salma tai murmushi sannan ta ran gwad'ar da kai gefe tace zaka skul ne? Yai tsaki yace eh, ta kankame hannunshi tace prince? Ya kalleta yace ya akai? Mikewa tai daga zaunen datake tad'an d'agashi, ya mike tare da kallanta, kujerar data zauna ta maidashi ita kuma ta tsugunna, salman ya kalleta da mamaki yace beauty menene? Takwanto da kanta kan cinyarsa sannan tace my prince in rokeka wani abu? Ya kalleta yace mene? Tai shiru dan tana tsoron abinda zata fad'a can ta daure tace yanzu muyi karatu, kaji? Ya kalleta yace muyi karatu? Ban gane ba? Salma ta kara gyara kanta tace karatun skul nake nufi? Muyi karatun da gaske kaga muna bata lokacin mu ne, sai alokacin salman ya gane me take nufi wato yadage akan karatunshi, ya kalleta tare da shafa kanta yace bana so😏 beauty, salma ta d'ago tace why? Hannu yasa a lebenta alamar tai shiru, yace beauty banaso inyi wani abun da zai birge Abba, yana kai nan ya mike yai hanyar toilet.
Salma ta mike da sauri ta rungoshi ta baya, tace prince ba dan ka birgeshi nake nufi ba, dan ka gama ka huta nake nufi, salman ya juyo da ita gabansa yace beauty? Salma ta runtse ido tace please 👏🏻,salman ya kura mata ido ahankali ta bud'e idanta, salman yace inace banaso zaki daina min maganar? Salma tai shiru can tace a'a in kace bakaso yau, gobe zan kara tambayarka har sai nai convincing d'inka😕, salman ya kalleta yai shiru, salma idanta yai rau rau tace prince? Salman ya janyeta tare da shiga wanka.
A gun ta tsugunna tai shiru, dolene ta taimaki mijinta, amma ta ina? Shiru tai dan itakanta bata da amsar tambayarta.
Salman a toilet shaya kawai ya sakar ma kansa yai tsaye yana tunani, ruwa ne ke zuba ajikinsa, yasani maganar salma gaskiya ne, amma ina.....bayajin zai yi amfani da shawararta, ya dade a haka kafin yayi wankan ya fito.
Inda yabar salma anan ya tadda ita, dasauri ya d'agota yace beauty meye hakan? Ta kalleshi batace komai ba, sun dade suna kallan juna kafin salman ya daure yace naji, I will think about it, salma ta saki wani murmushi tare da rungumeshi, salman ya d'agota tare dakai bakinshi cikin nata, sun dade suna kaima juna sakonni da harshensu kafin su saki juna, a hankali suka bud'e idanuwansu, salman ya rungumeta tsam a jikinsa wani shauki ke kamashi, salma ahankali tace Thanks, salman yace for? Tace kace zakai tunani at least bakai rejecting ba, salman ya shafo bayanta baice komai ba sannan ya d'agota, takalleshi tace yanzu zaka fitan ai ko? yace eh tace bari induba abinci kafin ka gama, tafad'a tare da dan matsawa, salman ya riko hannunta yace baki fitomin da kaya ba🙁 takalleshi tace ni😳? Yace tunda bakyaso bari na.....dasauri tace a'a inaso, bari ind'aukoma, yai murmushi.
Itakuma ta bude drawer tafara duba kaya, kananam kaya ta d'auko rigar white ce anyi rubutu da dark blue a jiki sai wando jeans, salma ta kalleshi tace sunyi? Dariya yai yace in sun ma beauty nima sunmin, salma ta ajiye kayan akan gado tare da cewa godiya nake da wannan matsayi☺, tafad'a tare da yin waje.
Fulani zaune itada farha da ishaq sunyi shiru can fulani tace ya kamata mu fito da wani plan, ishaq ya kalleta yace umma wai da gaske salma na ita ta wargaza plan d'in namu? Farha ta kalleshi salmana? Tab, fulani itama da kalmar ta b'ata mata rai amma ta daure tace eh mana, ni yarinyarnan ina mata kallan mara wayau ashe green snake ce? Farha tai kwafa ta tuno da marin da aka maka mata, sannan bakin cikinta d'axu da safe salman ko kallanta baiyi ba har yagama jawabensa ya fita, fulani ce ta katsesu da cewa kunyi shiru, ishaq yace kawai musa a kamashi akaishi can wani kauye mai nisa a cillar dashi, farha ta kalleshi tace me kake nufi? Fulani ta harareshi tace kai fa haka kake baka tunani kake magana, ishaq ya zuciya yace ni dama ba'a taba d'aukan shawarata ba😏fulani ta zuciya tace duk shawarwarin naka da basuda kan gado? Ishaq ya hade rai tare da mikewa yace ni zan wuce, fulani tace koma ka zauna dan ban baka umarnin fita ba, ishaq ya kalleta sannan ya harari farha yai fitarsa.
Nace uhmmm🤔
By _*AYUSHER MOHD*_📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
_*This page is dedicated to all members of my group " The Queen Bee" thanks for ur love and care.... love u oll.*_
NO.4⃣6⃣
Salma haka ta zauna har saida salman yagama cin abinci tana kalansa, daya ce taci sai tai murmushi tace ni ba yanzu ba, nafisan in kalleka har ka gama, yace in na kware fa? Tace bazaka kware bama in kuma hakan tafaru sai in baka ruwa😊 tai maganar tare da nuna mai jug d'in ruwa, dariya yai yacigaba da cin abincinsa, bayan ya gama ya mike, salma tace ina zuwa, ya kalleta da mamaki, d'aki tai da sauri, ta d'auko jotting book d'inta sabo ta duba rubutun ciki baifi 3pages ba dasaurI tasa hannu ta yage, sannan ta d'au biro ta makala a littafin ta fito da sauri.
Salman na tsaye yana jiranta ta karaso tare da mikamai, yakalleta yace na menene? Tace na karatunka mana😉, salman yace what? Tad'an turo baki tace a class in anyi wani abun ai zakai jotting, salman yace wa? Ni? Salma tace kai my prince☹ irin wannan dizgi😢? Salman ya kalleta yai murmushi yace hakan ne dizgi? Ta juya baya cikin shagwaba tace eh mana gashinan☹, ajiyar zuciya yai ya juyo da ita sannan ya anshi littafin yace happy? Ta kalleshi cikin tsananin farinciki tace alot😊, ya sunkuyo yamata kiss a goshi ya fita, ta dade a tsaye tare da shafa gun kafin ta shiga ciki.
Salman shikanshi a mota ya dade kafin yaja mota, yana isa gidan najib a waje ya tadda shi, bai fita ba najib ne yashigo, salman ya ja mota sukai skul, sai da sukai parking najib ya kalli salman yace yarima gaskita na yarda aure nacanza mutane😁 salman yace bangane ba? Najib yace da ace da ne da gudu zamu shigo muna tada kura amma yanzu baka gudu da mota nakula, ko dan......salman ya kalleshi yace kodan me? Yace ohh ka manta? First had'uwarku da salma ta hanyarne? Salman ya tureshi yace najib na kula kwanan nan gulma ke cinka dayawa, najib yai dariya yace Ango Ango, salma ya bud'e motar tare da ya fita, najib ya kalli kusa da inda salman ya mike ganin littafi da biro yasa shi wani tsananin mamaki, da sauri ya fito, sai dai baiga salman ba, can ya hangoshi yana tafiya, da sauri ya bishi.
Salman sai dayaje kusa da theater d'in dazasuyi lectures ya tsaya, najib ne ya karaso yace kai wasa wasa kana da sauri, salman yace ina zan tsaya ka bayan kana ganin rana ake, najib ya kalleshi yace muje, salman ya kalli hannunshi yace wannan? Da sauri yasa hannu ya fizge, najib yasa dariya yace najib dagaske ne abinda nake zargi? Naka ne littafin? Lalai in nakane da alama za'ai ruwa da kankara, salman yace to parrot sai kai tayi, na matatane menene? Najib ya bud'e baki yace da alama naka ne da gaske😳 u? Littafi? Ha ha ha .
Salman ya makamai littafin akai ya wuce ciki, to ba najib ba salman gani yai kowa na kallansa da sauri ya d'aga rigarsa yasa littafin a ransa yace yazanyi da beauty🤔?.
Fulani zaune tayi shiru, ta kalli farha tace farha ki bani yau zuwa gobe zan samo mana wani plan d'in farha tai kasa dakai, itadai tafara tsoro sai dai salman ne batajin zata iya hakura dashi, farha ta mike tace to fulani Allah yakaimu goben, fulani ce tace farha kirami hindu( baiwar fulani ce) farha tace to, hindu ta iso tare da tsugunnawa, tace gani ranki ya dade, fulani ta kalleta tace kinsanar da ishaq d'in inasan ganinsa? Hindu tai shiru, fulani tace dake nake, hindu tace nafad'a mai amma yace kiyi hakuri bazai samu zuwa ba, kuma bayasa ran har zuwa gobe zai samu dama, fulani ranta ya kara baci,takalli hindu tace fita, hindu tace to dasauri tai waje, fulani ta rike kanta tace ni? Ishaq? Hannunta ta dunkule, aranta tace da alama sai na lalaboshi.
Salman zaune a aji ana lectures, sai dai wayace a hannunsa yana dane_dane, najib yad'an zunguroshi yace yarima bazakai rubutu a littafin love d'in ba? Ga malan nata bayanai? Salman ya ture hannunsa yace kai rubutun kake? Najib yace yanzu nake tunani da alama gobe zan shigo da littafi tunda matar ka ta sa mu😊 salman ya makamai harara, najib yace kawo naku na love ni sai in muki rubutun, salman yace ka manta kana nufin littafin beauty d'in zan baka kamin jagwalgwalon rubutunka? Najib yace ahhh hmmm ayi hakuri, salman ya juya tare da kallan wayarsa jin karar text, dasauri ya bud'e ganin daga salma ne.
" My prince please concentrate".
Ya kalli text d'in , yace ya akai ta sani? Wani text ne yakara shigowa.
" please "
Salman ya karanta tare da murmushi, sai kuma ya ajiye wayar yad'an d'ago ya kalli malamin amma dayake bai sababa haushi ya kamashi yaga ina... kifa kai yai akan desk d'in.
Salma dake zaune tana breakfask ta kalli wayar tare da murmushi, tun daren jiya tasan yazama dole su kwaci kansu a gidan nan, kuma duk tunanin datai abu na farko daya kamata shine salman ya gama skul........
By *AYUSHER MOHD*📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.4⃣7⃣
Salma zaune take akan sallayar datai sallar la'asar suna waya da Abba, jitai ana mata knocking da karfi, tanaji tasan basu hanne bane, cikin mamaki tace Abba sai anjima tare da mikewa, ta bude kofar ta fita, farha ce, mamaki ya kamata ta kalleta cikin mamaki tace malama lafiya? Farha ta kalleta cikin gadara tace bake nake nema ba😏 salma tace wa kike nema kenan? Farha tace kinfi kowa sani ai, salma tai murmushi tace kinfi kowa sanin baya gidan ai da alamun yanda kika bugamin kofa, farha tace matsalarki, dama abinda yasa na miki knocking so nake kiban d'ayar number yaya na kira mtn d'inshi ya ki dauka.
Salma takalleta baki bud'e tace ke da wa kike magana tukunna? Farha tace au mu 10 ne agun? Salma tace nakula marin jiya bai isheki ba, farha tai wata shewa tace toko zaki kara? Salma tai tsaki tace sai kuma aka samu matsala banda tym d'inki, ta juya ta koma d'aki tare da datsowa.
Farha tai zauna akan kujera ta tuna magajarsu da fulani, datace ki nunamata bakya tsoronta, sannan bakya kara akan san salman, kishi zaisa ta mareki ko ta miki wani abun, ke kuma duk randa ta miki abu ki tabbatar ab'angarentane dan bayinta su gani, in ta mike sai ki kawo kara guna, nikuma sai insamu sarki infad'amai, dan salman na kulaki ta miki duka, wai soyayya kuke, ni dakaina zanba sarki shawara.
Farha bayan tagama tunani tai tsaki tace yau plan d'in beye ba da alama sai na sake wani shirin, ta mike tai waje.
Salma kam a d'aki tsakiwa tai ta rike kafad'a tace what? Number yaya? Lalai farha tagama rainata, ba shakka sai ta d'au babban mataki akanta.
Salman sai bayan isha'I ya dawo, wasu bayi na biye dashi da ledoji manya guda biyu, a falo suka ajiye suka juya, salman ya d'au ledojin tare dayima salma knocking, da sauri takara shafa hoda tasa turare kad'an ta bude kofar tare da sakin murmushi, salman ya kalleta yai ajiyar zuciya, ta kalli hannunsa sannan ta anshi leda d'aya, yana shiha ciki ya ajiye kayan akasa ya jawota jikinsa ya rungume, ta shafa bayansa tace da alama prince d'ina ya gaji, salman yace kai I miss u beauty, jinai kamar na dade ban ganki ba, tai murmushi tace eh mama ka dad'e mana tunda tun safe ka fita☹ salman ya kara rungumeta yace gaskiya kam, ajiyar zuciya sukai a tare sai kuma suka saki juna sukai dariya duk hakoransu suka fito, salman ya zauna akan gadon yace ahh beauty da alama shiga zuciyata kike kima ganin abinda zanyi, tai murmushi tace au shiga ma nake? Nad'auka da a ciki nake🙄? Salman yasa hannu ya jawota ta zauna akan cinyarsa ya mata kiss a baki yace mantawa nai ashe a ciki kike? Salma tad'an mintsineshi a ciki sai dayai 'yar kara tace ashe? Dariya yai shima yasa hannu a cikinta ta d'auka ramawa zai sai taji ya sa hannunsa a cikinta yana wasa dashi, motsi tafara tana ture hannunshi tace please ka bari, wanna fa wayon chakulkuli ne, dariya sukai so sai suka kwanta akan gadon a rigingine, salman ya mike yace beauty taso yafad'a tare da d'agota, ta mike tana kallanshi yace kaya ma siyo miki, tace haba? Yace jawo ki gani, nan ta jawo ledojin, English wears ne kala kala, riga da wando, riga da siket, riga iya gwiwa ta d'ago d'ayan ledar, duk mii siket ne da kanannan riguna wanda ko ciki basu rufeba, da sauri takalleshi tace naji wancan nawa ne amma wannan fa? Salman yace shima nakine 😉
Ta kalleshi tace wannan? Tafad'a tare da d'aga kayan, salman yace eh kuma yanzu zaki kwada d'aya nagani ba🤔 salma tace naam? Salman yace ina jira, salma ta kalleshi ya had'e rai yaci wani magani, tace prince ai.....katseta yai yace in bazakisaba ki barshi, tace ba haka bane, tafad' a tare da d'aukan d'aya harzatai toilet ta tuna da sauri ta dawo jikin kujera tafara kokarin cirewa, tanayi tana kallan salman, sai dai shi ta kula hankalinsa nakam wayar hannunsa.
A hankali ta zura rigar ta kamata sosai, ga rigar bata gama rufe ciki ba, ta kalli siket din tasan ko cinya bazai gama rufe mata ba, takalli salman sai dai fuskarnan a had'e nan ta shiga sa siket, ya maseta d'am hips d'inta sun fito sosai ta kalleta tace kamar kiristiyana? Abinda batasani ba tunda tafara sa kayan salman ke satar kallanta ta gefe, ta tsaya tunanin kayan, batasan sanda salman ya karaso gunba, kanshin turarensa ne yasa ta d'ago, fizge zanin datad'an rufe yai tare da kallanta, yace Woooooo kai beauty kin ganki kuwa? Salma tad'an harareshi tace inafa zan ganni tunda an maidani kiristiyana😞? Salman yasa hannu sai jitai ya d'agata sama, tace prince? Juyi yai da ita sannan ya direta akan gado salma tai murmushi tace my prince? Salman yace umm, tace I am afraid😞 yace for what? Tai shiru can tace ganinake kamar I am too happy ya rungumeta yace bana fad'a miki ki daina wannan tunanin ba? Tace Allah in ina tare dakai mantawa nake da komai, ina tsoron kar farincikin danake ciki ya yanke, kallanta salman yai sannan ya sa hannu a gefen fuskarya ya shafo bakinta,ahankali yakai bakinshi nata, wani salo yake mata itama nan ta shiga maidamai, kan kace me? Duk sun fita hayacinsu, cikin wata murya salma tace i luv u dear, salman cusa kansa a rigarta a hankalI ya zagu mata siket.......nidai kam daga nan nai waje da d'an littafina, kafin salman ya bugo ni da sanda🚶🏻🚶🏻🚶🏻🚶🏻
Ishaq ne zaune a kam kujera ya had'e rai, fulani ta kalleshi tace haba ishaq nice fa? Ya kalleta cikin ko in kula yace nasani ai, tace to naji kayi hakuri, yace nahakura amma in an kiyaue abu biyu, na d'aya kidaina nuna salman ya fini komai, sannan na biyi duk cikin plan d'inmu kar akuskura a tab'amin salmata dan bazan yarda ba ehe, fulani ta tabe baki a ranta tace Allah ya raba bawa da wahala in banda rashin tunani me zakai da matar kaninka? Kanin ma makiyinka? Ishaq ya kalleta yace ke nake jira umma, tace nayarda zan kiyaye duka, mun shirya ai ko? Yai dariya yace yanzu a ina zamu tashi?
................
Nace a inda kuka tsaya🙄😏aikin kawai
By _*AYUSHER MOHD*_📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.4⃣8⃣
Bayan sunyi wanka, suka sa kayan bacci suka kwanta, salma ta kwanto jikin salman sannan tace dear ya makarantar? Ya shafa kanta yace lafiya, tace kasanfa ba haka nake nufi ba, tafad'a tare da d'agowa ta kalleshi, salman yaja kumatunta kad'an yace beauty kenan, salma ta kalleshi batai magana ba, salman yai ajiyar zuciya, salma takalleshi tace badai bakai rubutu ko d'aya ba? Inbakai rubutu ba nasan kaji amma ko? yace badai haka za'a dinga min kullum ba ana sani a gaba ana tambaya, salma tai matso da fuskarta tace ah to, tun kafin in gano mijina bashi da kokari gwara ya nunamin, ko in dinga ma lesson? Salman yai wata dariya tare da mikewa ya zauna yace what? Baida kokari? Yimin lesson? Beauty nakula baki sani ba amma sanda nai karatu a paris bana wuce position 1 to 5, har nagama secondary na, zakice me? Salma tasa dariya tare da rufe baki, ganin salman na mata wani kallo, yace meke nan?baki yarda ba? In d'auko miki ki ganine😎?
Salma takara dariya tare da toshe baki tace bafa haka nake nufi ba, ya had'e rai yace me kike nufi to? Ta daure tace nayarda dakai wallahi, kaima kasani ai duk abinda kafad'a ina yarda, na kuma sani basai an fad'amin ba, salman ya kalleta yace dariyar to tameye? Tace yanda kakeyi ne yasani dariya, yace kefa kika faro maganar, harda wani zancen lesson, salma ta gyara zama ta juya baya tare da rungume hannayenta a akirji, salman yace mekuma akai? Salma tace please kamaida hankali akan karatunka, salman ya kwanta tare da jawota, yace nidai abar maganarnan a d'auko wata, salma tace shikenan zan d'aura gobe, yai murmumushi tare da kara rungumeta, haka sukai tad'an fira kasa kasa,bacci me dadi ne yad'aukesu.
Yau watan su salman d'aya da dawowa, salma kullum sai ta tunama salman zancen karatu, duk da yana sharewa amma azahiri yanajin dadin yanda ta damu dashi, basa zuwa ko ina, tana gida, tayi sa'a kwana biyu farha ma bata shigo ba, salma najin dadi sosai rayuwarta da salman, wani irin so takema salman da ita kanta batasan yawanshi ba.
Yauma tana zaune ya gama gyara d'akinsu dan ta hana kowa shigar musu turaka, ta gyara tsaf tai wanka ta d'auko riga da wando ta saka tayi kyau sosai, tai kama gashinta ta gefe, kallan gashinta tai a fili tace ya kamata in wanke kaina, waya ta d'auka tama salman text tanaso taje wanke kai, salman na gama karantawa ya kirata, ta d'aga tare da sakin murmushi, salman yace beauty ni zan kaiki amma ko? Tai murmushi dama haka take so, tace naga kai kana makaranta, yace mun gama ai, yafad'a tare da kallan malamin dake koyarwa, salma da mamaki tace da wuri haka? Yace hakan ne wuri? Tace shikenan in ka gama sai muje ko? Yace ganinan, salman na kashe wayar ya d'an bugama najib littafin dake gabanshi, yace shugaban sa ido, kai karatu da kyau ni zani gun matata, najib yace zan fad'a mata malam na aji kake fita😛, salman yace in ka samu dama kenan, yafad'a tare da fita ta kofar baya ko ajikinsa.
Salma a baya ta d'ora akan kayanta ta nad'a mayafin kayan ta d'auko flat shoe tasa, agoggo ta duba tace ah why am I so excited? Waya ta d'auka tafara game, bata dade ba salman ya mata waya, da kyar tajira tai ringing biyu ta d'auka, salman yace matar salman ki fito, mijinki na jiranki, salma tai murmushi tace mijin salma ya jira matarshi kad'an gatannan fitowa, tafada'a tare da kashe wayar.
Mikewa tai ta rataya karamar jakarta ta saka wayarta da wallet d'inta ta fito, a hankali ta karasa mota tare da bud'e gaba, ta zauna, salman ya kalleta yai murmushi, yace ahhh naji kanshi matata, salma tace kai prince😟 mota ya tada yace amma dai ba direct gun wanke kan zamu bako? Tace can zamu mana, yace ban yarda ba sai na d'an zaga da matata, tace to ina zamu? Yace ba ruwanki.
Sun fita daga gidan daidai nan ishaq yazo shiga, da mamaki ya kalli motar, salma da salman ya kalla suna ma juna murmushi, wani mugun kishi ne ya turnukoshi, har ya shiga ya fito ya bisu.
Salman kam a 212 yai parking ya kalli salma yace muje? Tace me zamuyi? Yace yunwa nakeji, tace ok, fitowa tai suka shiga salman yasa aka sa musu snacks a takeaway sannan yace asa icecream, nan aka had'a musu suka biya.
Ishaq ya kalli shagon haushi ya kamashi, ganinsu yai sun fito da leda suna tafe kana ganinsu kasan sunyi matching da karshe ga wani farin ciki dake zaune a fuskokinsu, ishaq ya cika yai fam.
Mota suka koma sukai can hanyar aminu kano, sai da sukaje gun fly_over sannan salman ya d'an gangara yai parking, bud'e kofa sukai, salman ya kalleta tare da cewa abani abu inci, nan salma ta mikamai chicken pie da lemo, daga d'an nesa kad'an taga wasu masu saida gurji, jitai yawunta ya tsinke ta kalli salman tace prince bari inje can, salman yace ina? Ta nuna mai gun mutanen data gani, yace inkaiki mana? Tace a'a da kafa zani, yace to nan ta fita, ishaq kam ya baya kad'an yana kallansu, ganin salma ta fito yasa yace da alama sunyi fad'a naji dadi.
Salma kam takarasa gun masu gurji, ta siya, taga gyad'a dafafiya nan ma ta siya, har zata taho taga mai gwaza, tace abani gwaza, nan ta sisiya dadi ya kamata ta juyo tana murmushi, salman ganin yanda take murmushi daga nesa yasa ya fito ya tsaya yana kallanta,ishaq ya kallesu wato ba b'atawa sukai ba? Wani kishi ne ya d'ibeshi ya fizgo mota da gudu yai inda salman yake gadan gadan, salma dake tafiya ta kula da yanda motar ta taso, hannu take nuna ma salman ya matsa, shikam ya d'auka ko wani abun take nufi, tace kamatsa, salman yace naki, sai kin karaso, salma kam ganin yanda motar takusa zuwa inda salman yake yasa ta taho da gudu tare da jefar da ledojin salman ya kalleta ganin yanda take gudu a titi ya kalleta yace beauty? Ishaq yakarajin wani kishi lalai yau zai karasa salman, Kafin salman ya kara wani magana salma ta karaso haka motar ma, salma ta rukeshi sukai gefe, sai dai duk da haka sai da motar ta bige salma.
Ishaq baisan abinda salma take kokarinyi kenan ba, ganin ya bige salma yasa yai parking ya fito da sauri,salman kam suman tsaye yai jiyake kanshi na wainawa, salma ya kalla dake kwance a sume, ga goshinta ya fashe yana zubar da jini, masu gurji ne suka karaso gun ishaq ma haka, salman sai kallan kowa yake amma baisan meke faruwa ba jiyake kamar bashiba, ishaq ya karaso tare da kallan salma idansa ya ciciko, salman ya jijiga sai dai yakula salman baya hayacinsa, yace kai bakaga yanda salma take bane? Dalla malam.....gani yai salman ya rike kirjinsa da kansa wani irin kurkusus yakeyi, mai gurji tace ka kaisu asibiti mana, kar a samu matsala, ai kai kaja, kuna tafiya bakwa kula dana gefen titi? Ishaq ya kalli salma da sauri yasata a mota, masu gurji sukace saura shi, salman sai murkususu yake, nan wani mai rake ya karaso ya taimakamai aka saau amota, asibitin aminu kano yai dasu, shikanshi hawaye yake baiyi zatan abin zaikai haka ba yanzu ga salmarsa itace ba lafiya.
Suna zuwa Aminu kano, akai emergency dasu, salman kam ya fita hanyacinsa dan ba maganinsa, likitocin sun dukufa akansu, ishaq kam kuka yake ya daure ya kira waziri ya fad'amai, sarki kam yanaji jiyai kamar yasa kuka,yana tsananin san salman in wani abun ya same shi yazaiyi?
By *Ayusher Mohd* 📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.4⃣9⃣
Waziri ya kalli sarki yace "bari inje asibitin".
Sarki yace "kana nufin barina zakai anan? Bayan salman da matarsa na asibiti? Wayasan awani hali suke? Waziri yace amma kaga kai bai kamata.....
Sarki yakatseshi da cewa "yanzu kaje ka gunsu, nikuma sai ka sanar dani halin da ake ciki da daddare sai inje dakaina".
Waziri ya amsa sannan ya fita.
Likitoci sun dukufa akan salman da shine ke jin jiki, salma bayan an mata dressing, sai jini da suke tunanin za'a kara mata.
Salman kam sunyi mamakin yanda ya hari ciwo ya kamashi haka, da akamu abin ya dade, da kyar suka shawo kan lamarin kafin su turosu sukaisu d'aki d'aya, dukansu bacci sukeyi sakamakon allurar da aka musu.
Ishaq kam duk ya rikece yana ganin waziri yai gunsa da sauri.
Waziri ya kalleshi yace " ishaq ina salman da matarsa?, ya jikin nasu? Abindai ba babba bane ba ko?"
Ishaq ya rike hannun Waziri yace "Waziri wad'annan tambayoyin sun min yawa, wane kakeso in amsa?"yai maganar tare da zubo da kwalla.
Waziri ya ja hannunshi ya zaunar dashi sannan yace "bari inga likita, dama ba kai yakamata intambaya ba, yahkuri yarima mai jiran gado."
Waziri ya sakeshi yai gun likita,knocking yai daga cikin aka amsa shigo, Waziri ya murd'a kofar tare da shiga da sallama.
Likitan na ganinshi ya mike tare da gaisuwa, waziri ya amsa tare da zama, likitan ya kalleshi tare da zama shima.
Waziri yace " nazo ne inji halin da d'an mu da matarsa suke ciki",
Likita ya mike yace "badai wanda aka kawo da matarsa kake nufi ba? ".
Waziri yace "eh salman da matarsa salma", likita yai shiru can yace " wanda yakawosu bai fad'amana ba hannu kawai yasa akan aiki, sannan a zahiri nayi mamakin yanda akai kuka bari yarima salman d'in ya kamu da heart attack,"
Waziri cikin kid'ima yace "what? Heart attack? Likita ban gane ba?".
Likita yai ajiyar zuciya yace " ka kwantar da hankalinka, ai salman yaro ne dama shi wannan ciwon yana wahalar warkewa ne ga wad'anda suka girma, to Alhamdulila salman yaro ne, saboda haka karku damu, akwai treatment daza'amai sai dai ba'anan ba."
Waziri yace " bangane ba anan ba?"
Likita yace " akwai wani babban likitanmu *DR BILAL*( mijin ilham tsohon littafina), yana zaune a kasar england to ya sanar mana zai dawo nan da wata d'aya, likitane kwararre dan kwarewarshi ce tasa suka rikeshi, inhar yadawo sai aka salman ya dubashi sai yasan meya kamata amai."
Waziri yai ajiyar zuciya yace "to Alhamdulila, salma fa?"
Likita yai murmushi yace wannan ba matsala kanta ne yabugu sai jini data zubar, munason kara mata jini."
Waziri yace " Alhamdulila"
Likita ya sake murmushi yace "amma tana d'auke da juna biyu na wata 1."
Waziri ya saki fara'a shima yace "kai masha Allah, ta farfado ne?"
Likitan yace "eh to yaci ace sun farfado yanzu, muje indubasu a canza musu d'aki,"
Waziri yace to yafad'a tare da mikewa sukai hanyar d'akin da aka kwamtar dasu Salman, Ishaq ma na ganinsu ya biyosu.
Sun shiga sun tadda Salman a zaune rike da hannun salman, idanunsa taf kwalla, Waziri na ganinshi yakarasa da sauri ya dafa Salman.
Salman ya juyo ya kalleshi ya kuma kasa magana, hawayen dake kwance a idanunsa ne suka zubo, mamaki ya kama Waziri tunda yake yau ce rana ta farko dayaga hawayen Salman bashiba hatta Ishaq.
Likitan ya kalli Salman yace ranka ya dade kwanta in dubaka, Salman ya kalleshi yace " ni lafiyata kalau ga wacce nake so inji me kuka mata da ya hanata farkawa?"
Likitan ya karaso kusa da Salma ya shiga dubata, ya d'ago yace "lafiyarta kalau komai nata normal, bansan me ya hanata farkawa ba,"
Salman ya mike yamai wani kallo yace "baka sani ba?"
Likitan yace "zata farfado nan acikin nan da 24hrs in bata farfado ba kafin nan zamu sake running d'in test."
Salman ya zuciya yayo kan likitan Waziri ya tareshi da sauri yace "Salman ka nutsu mana, Salma juna biyu gareta bai kamata a d'inga hayaniya haka ba."
Salman yace "me? Juna biyu? Likita da gaskene?" Salman duk ya rikice, Ishaq wani kishi ya kamashi juyawa yai ya fita da sauri.
Salman yabi Ishaq da kallo, sai dai yau farinciki yasa bashi da lokacinsa amma alkawarine dole ya koyamai hankali.
Salman komawa yai kusa da Salma ya kamo hannunta bakinshi yaki rufuwa yace " Beauty ki tashi please, ki tashi mu kula da Babyn mu, Beauty ki tashi please.....
By *Ayusher Mohd*📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO. 5⃣0⃣
Waziri da likita ganin yanda Salman yake kallan Salma yasa suka fita daga d'akin tare da jawo kofa.
Salman ya kurama Salma ido a hankali yakai hannunsa kan inda aka sa mata plaster ya shafa gun, jiyai jiri nad'an kamashi daga zaune, sauri yai ya kwantar da kansa akan pillow d'in datake, kansa kusa da nata, hannunta ya rike kam.
Tunani yafara yi, wato ishaq shi yaso bigewa?Baiwar Allah azal yafad'a mata, sashi akai? Abinda yafad'omai kenan aransa, yanzu da sun mai asarar cikinsa fa? idansa ne ya kad'a yai ja, a mike zaune ya kalli Salma yace
" I won't forgive them,duk wanda keda hannu a cikin wallahi I won't let them be."
Ishaq kam gida ya wuce cikin b'acin rai yai b'angaren fulani.
Tana zaune acikin kilisa, hankalinta akwance, sai ma farin ciki da take wai ance salman na asibiti da matarsa, itakam jitake ina ma su mutu ko ta huta da ganinsu.
Ishaq ne yai sallama ya shigo da sauri, fulani ta kalleshi tace " yanzu nake nemanka ka tayani murna, Allah ya saukaka mana komai."
Ishaq ya zauna rai a b'ace yace " wani sauki koma? Banda tashin hankalin danake ciki?"
Fulani tace " wani bakin ciki bayan Salma da Salman na asibiti."
Ishaq yai tsaki yace "Umma nikam kibar wannan zancen, ni fa kishi ya ciwoni naso makeshi, amma Salma ta kare shi."
Fulani ta mike tsaye cikin kid'ima tace "mene? Ishaq kasan me kake fad'a kuwa? Ishaq bangane kai kaje make Salman ba."
Ishaq ya share zufa data ketomai yace " bama wannan ba Umma, Salman ya ganni yasan ninai."
Fulani tashiga tafa hannu tace "shikenan na shiga uku, Ishaq yanzu yazamuyi? Me yakaika? Nafad'amaka kad'inga tunani da hankalinka."
Ishaq yace "ni dan Allah Umma kidaina min wannan zancen abinda ke damuna ma ya isheni."
Fulani ta zabura yace "meke damunka? Akwai abinda zai dameka daya wuce wannan?."
Ishaq ma ya mike rai a b'ace yace "haba umma ya kikeso inyi da raina? Ina kallo yanzu Salma zata haifi d'an Salman?"
Cikin mamaki fulani ta kalleshi sai kuma ta had'e rai tace "da kanaso ne Salman d'in yasata agaba yai ta kallo ko me?"
Ishaq yace "ba ciki ne da Salma ba ko 'ya'ya d'ari gareta nidai ina santa bakuma abinda yadameni da wani Salman ko wani da zai kawomin matsala."
Fulani data rikece jin kalamansa tace "me kace? Ciki? Ishaq me kake nufi?"
Ishaq yace "ciki ne da salma yanzu aka fad'a a asibiti, menene?, kema kina tayani kishi ko?"
Fulani ta harzuka tace dalla gafara banza, shashasha, Salma nada ciki inta haifi namiji fa? Kai matanka biyi 'ya'yanka hudu amma duk mata, shine maimakon kai tunanin abin da zai faru gaba shine kakemin zancan wata banzar soyayyarka?"
Sai a lokacin ishaq yai shiru, yanzu in bai haifi namiji ba fa? Kenan za'a iya bashi mulki daga baya aba d'an salman, yazaiyi? Yanda ya tsani Salman d'in nan."
Fulani tazauna tare da dafe kai tace "yau nikam da wani hannu na tashi? Wannan bakin ciki kala_kala?"
Farha ce ta fito da sauri ta kalli Fulani tace " zanje asibiti ance Yayana bashida lafiya," Ishaq yai tsaki yace to salman ya ware, sai dai in Salma zakije ki dubo daganan sai ki tayashi murna tunda sun samu karuwa."
Farha takaraso tace "bangane ba? Karuwa kamar me?"
Ishaq yace "ciki gareta."
Farha tace "mene? Ciki? Bangane ciki ba?."
Fulani dake rike dakai tace " Farha yaz'amuyi Salma dai ciki gareta."
Farha ta zube agun ta d'aura hannu akai ta sa ihu tace " ciki? Shikenan nasan yaya Salman bazai kulani ba, Amma wannan Salmar akwai yar iska."
Nace ko kuma ku ba.....
Salmah kam tana kwance itakam rayuwa mai dadi take acikin baccinta, yau taga fuskar saurayin nan Salman ne suna zaune a bakin ruwa, ta kwanta akan cinyarsa shikuma yana rike da littafin story book yana karanta mata, sosai takejin dadin labarin sai lumshe ido take, Salman ya kalleta yai murmushi sannan ya rufo gefen fuskarta da littafin hannunsa, yakai bakinshi kan lebenta ya sumbata, ido ta rufe cikin murya kasa_kasa tace "in aka ganmu fa?"
Salman yace "menene aciki? Keba matata bace?"
Murmushi sukai ta kalleshi tace "ka cigaba," tai maganar cikin shagwaba nan ya cigaba da karatun.
Sarki yau farin ciki ba'a magana zuciyarshi kamar ta faso, sai dai yana tsakiyar murnar yin jika dazaiyi ta tsatson Salman waziri ya nisa yace "amma akwai wata 'yar matsala, Salman nafama da wani ciwo."
Cikin tsoro Sarki yace "ciwo? Wani iri kenan?"
Waziri yace "yarima Salman na fama da ciwon heart attack."
Cikin rud'ewa Sarki yace "heart attack? Kasan mai kake cewa kuwa waziri?"
Waziri ya tsugunna yace " tuba nake ranka ya dade."
Sarki ya rike kansa, yama kasa magana.
Waziri yace "amma akwai likita, ance inyazo insha Allahu da yardar Allah Salman zai warke."
Sarki yai shiru can yace " waziri kasani yaron nan kaf cikin 'ya'yana ba wanda nakejinshi har cikin jikina irinsa, in wani abun ya sameshi bansan yazanyi ba, da alama ciwonsa ma nine sila."
Waziri yace "ya kake fad'an haka ranka ya dade? Kaine sila?ciwo ne dai daga Allah."
Sarki yace "nasani ciwo me daga Allah amma nasan bakin cikin daya kunsa yana yaro shiya jamai wannan ciwo."
Waziri nan ya shiga bashi baki, sai dai Sarki jinsa kawai yake, can yace "naji waziri yanzu ana isha'I kazo ka kaini inga halin dasuke ciki, waye agunsu?"
Waziri yace "na kira zeenatu tace tana hanya."
Salman ne ya kallin likitan dayazo duba Salma yace "yanaga bata farka ba?"
Likitan yace "karka damu kila itama tanajin dadin rayuwar da takeyi ne acikin baccin, amma zata farka nan bada dadewa ba."
Salman ya kalli Salma cikin tsananin tausayi.
Likita yace "amma ina tunanin za'a kara mata jini kad'an." Salman ya kalleshi yace "akara mata nawa ko leda nawa ne dan kuwa O+ gareni bana tunanin akwai matsala."
Likita yai shiru can yace "amma ina ga kai da bakada lafiya bai kamata aragema jini ba."
Salman yace "jikinka ne ko nawa? Ko kuwa inwani abun yasameta zakai d'au responsibility?"
Likita ya had'iyi yawo yace "a'a ayi hakuri yarima, bansan kalmar zata b'atama raiba."
Salman yamaida idansa kan Salma tare da riko hannunta cikin zuciyarsa yace " Beauty please"
Tunowa yai yakamata ya kira Abban ta, to karkuma ya tada musu hankali, ajiyar zuciya yai yace "Beauty yazanyi?
By *AYUSHER MOHD*📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.5⃣1⃣
Zeena tazo sai dai duk yanda ta roki Salman akan yaci abinci amma yaki, tai fad'an har ta gaji, shikam yama dags akan ta rakashi agwada jininsa su tabbatar zai iya bata, a d'eba asa mata.
Zeena ta kalleshi tace " haba Salman mai yasa kake haka? Kabari gobe in an kira 'yan uwanta sunzo sai a gwadaso asamu wanda yai a kara mata, amma kai baka da lafiya ina kai ina bada jini? Sannan gashi sam kakicin abinci."
Salman ya kalleta yace " Aunty zeena har dake? Nad'auka ke ba halinku d'aya dasu ba, taya zakice gobe in 'yan uwanta sunzo, Salma matatace kuma saboda wani abun dabai gagareni ba bazan nuna mata nafisan kaina akanta ba, abinci kuma inkinga naci abinci to tabbas naga matata taci." Yanakai nan ya fita, Zeena tausayinsa ya kamata, wani irin so Salman kema Salma haka? A da taga ko kallo bata isheshi ba, yaushe abu ya juya haka?.
Salman da kanshi yaje lab d'in suka gwadashi sun tabbatar O+ gareshi kuma zai iya bata, wucewa yai gun likita yace "tashi muje ko?"
Likitan yace "Yarima dan Allah....."
Cikin fad'a Salman ya katseshi yace "Karka bata min rai, inace inason abu to kamin kafin ranka ya b'aci, nagaji da ganin matata a kwance."
Likitan yace "kayi hakuri ranka ya dade amma matarka badan jini bane taki tashi."
Salman yace " Naji, amma wuce muje inka kara mata jinin sai nu jira in ta wuce hours d'in daka fad'a hmm bansan kuma mai zan ma ba."
Salman ya juya, da sauri likitan ya fito sukai shigo da kayan aiki d'akin, an saita komai sai da ba'a fara ba mai martaba ya iso shida waziri.
Salman na ganinshi ya had'iyi wani abu tare da kara d'aure fuska, Sarki ya karaso kusa dashi, waziri ya kalli Zeena dake gaida Sarki yace inkin gama kowa ya fito yabasu guri, tace to.
Kowa ya fita yabarsu su biyu sai Salma dake kwance, Sarki ya kamo hannun Salman ya rike yace "Salman na tsorata danaji ance bakada lafiya na d'auka kaima rasaka zanyi."
Salman ya kalleshi idanshi yai jaa, dasauri ya maida kanshi gefen da Salma take, Sarki yace " Salman meyasa baka sanar dani larurarka ba? Ina zaune bansan halin da d'ana yake ciki ba."
Salman ya kalleshi yace " Ina zaka sani Abba? Tunda mukamin ka yafini daraja? Tunda kake dani ka taba tambaya ta yana tashi? Meke damuna? Naci abinci? Bani da wata matsala dake damuna?"hawaye ya zuboma Salman a ido yacigaba" Kun rufe mutuwar Ummana saboda san mulki, kun turani wata kasar dan bazaku iya kula dani ba, sannan yanzu Abba katambayeni wai zancen ciwo na? Ban fad'ama ba?"
Ya share hawayen dake zubo masa yace " kasan wace irin rayuwa nayi? Kai dai kullum kana zaune akan kujerar mulki sai abinda aka fad'ama."
Salman na zuwa nan ya runtse ido, hawaye suka kara zubomai ya share tare da kallan Salma, yace "zan iya jure komai amma banda a tab'a matata."
Sarki da tunda Salman yafara magana kwalla ta cika taf a idanunsa yasani sarai abinda Salman ya fad'a duk gaskiya ne, amma ya zaiyi? Tunda haka mulki ya gada.
Kafad'ar Salman ya dafa, ya d'ago ya kalleshi cikin tsananin tausayin d'an yace Salman na sani duk wani abu dake damunka laifinane na sani amma dan Allah Salman ka cirema zuciyarka komai ko ka samu nutsuwa, kaduba matarka, ciki gareta ka taimakeni Salman ka cire komai aranka kafin d'anka ya taso da kiyayyata, Salman kayi hakuri akan duk abubuwan dana maka, nasani sarai abin na damunka amma zuciyata inta ganka sai inji tausayinka bazai bari in tada maganar ba."
Salman ya kalleshi yace " So nake ka bani izini ind'au matata in bar gidan, dan banasan zama a cikin gidan, nafisan inda zamuyi rayuwa kamar kowa nida abinda za'a haifarmin."
Sarki ya kalleshi tare da jijiga kai, yace Salman banda wannan, zan iyama komai Salman amma bazan iya barinka nesa dani ba, bayan kaine magaji na."
Salman yace "magaji? Magajin me fa?"
Sarki yace "mubar maganan nan Salman dan Allah."
Salman yace " Abba?"
Sarki ta rike hannun Salman yace "Salman kayi hakuri ka yafema wannan mahaifin naka, yasani yamaka laifufuka da dama, amma ka sani kullum kana ranshi dai dai da minti 1 bai tab'a mantawa dakai ba."
Salman hawate suka kara zubomai, yana tsananin san mahaifinsa yazaiyi? Idansa ya runtse baice komai ba, Sarki yai shiru can yace "ance hatsarine, bakasan waye mai wannan d'anyen aikin ba?"
Salma ya tuno sanda yaga Ishaq amma sai ya daure yace "ban ganshi ba sai dai koma waye I won't forgive them."
Sarki yace "ko ni, sai dai in a rashin sani ne amma in har wanda yai da saninsa ne to bazan yafemai ba ko waye kuwa, I promise you this."
Salman yace "Abba karkai Alkawarin dabazaka cika ba."
Sarki ya dafashi yace "Salman kenan, ai sarki na gari baya magana biyu, amma nikam Salma taji jikine? Naga bata farfado ba?"
Salman yace" nima bansani ba wlh, yanzu dai jini za'a kara mata sai mu jira nan da wasu awanni kad'an mugani."
Sarki yace "da alama d'ana ne zai bada jini?"
Salman yai kasa dakai tare da sosa keya.
Sarki yai murmushi yace "naji dadi Salman da yawancin halayenka irin nawa ne, kasan me?"
Salman ya girgiza kai Sarki yai kasa da murya yace" Sanda inasan ummanka banajin komai, ganinake komai zan iyayi saboda san da nake mata."
Atare suka kwashe da dariya, waziri da zeena da sauran fadawan dake waje suka kalli juna cikin tsananin mamaki, duk cikinsu ba wanda yataba jin dariyar sarki haka, ko salman d'in ma.
Bayan sun tsagaita, sarki ya rungumo Salman yace karka damu d'ana Salma zata warke sumul kamar ba ita ta bige ba, Salman yai murmushi, wani irin farinciki ke ratsatsu, daga Salman har Sarkin.
A gaban Sarkin aka kira likitan ya juna kayan aiki nan aka fara karin jini, Sarki ya shafa kan Salman ya fita.
Hmmmm tsakanin 'Da da mahaifi sai Allah
......