By *AYUSHER MOHD*📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
No: 5⃣9⃣
Salman ya kalli Ishaq yace " ahhh so matar kaninka kake so shine kaje d'akinsa?" Ishaq yace " nifa ba haka nake nufi ba."
Fulani tace " wai Salman meye hakan? Kasa yaro a gaba kanata bugar cikinsa, to bazan yarda ba, nasani sarai Ishaq d'ina bazaije gun wata matar ka ba mai kama da aljanna."
Salman yad'anyi dariya yace "Umma I feel hurt, wato ni ba naki bane bako?" Fulani takalli sarki tai kasa dakai tace "nifa ba haka nake nufi ba."
"Ohhhh nagane me kike nufi, amma umma bakya ganin bai kamata kice nasa yaro agaba ba? Yanzu kamar Ishaq a kira shi yaro? Yafa girmeni?"
Salman ya fad'a yana mata wani kallo.
Fulani kam ta tsani Salman yasata agaba duk ya rikitata haka, bare yau agaban Sarki tama rasa me zata ce.
Ishaq yace" niba yaro bane, nasan kuma duk abunda nakeyi, yama za'ayi kid'inga kirana yaro agaban Salman?"
Sarki yai gyaran murya hakan yasa kowa ya nutsu,cikin b'acin rai ya kalli Ishaq yace "kenan dagaske ka shiga d'akin Salman kaje neman matarsa?"
Ishaq yace " Abba ba haka bane.."
"To ya ya ne? Ko inkira matar tawa ne? Ko kuma kanaso in kara maka dukan dana ma d'azu ne?" Jiyai Salman ya katseshi da wad'an nan kalmomin.
Ishaq ya kalli Salman a rikice yakuma kalli Fulani datake makama Salman harara ta gefe, yai kasa dakai tare da runtse ido.
Salman yad'an tab'e baki ya kalli Sarki, sannan ya kalli Ishaq yace " nikam yaya waye ya kaimu asibiti ranan da mukai karamin accidents d'inan?"
Ishaq cikin zumud'i ya d'auka wani abu ne yace " nine mana, nina kaiku."
Fulani zatai magana Sarki yace " kar inkuskura inkara jin bakinki anan tunda badake suke ba."
Salman yai murmushi yace " Ayya yaya nagode, dabadan Allah yakawo ka ba bansan mezai faru da Salma ba."
Ishaq ya sosa keya cikin farin ciki yace " ai duk lefinka ne, mezaisa ka bari Salma ta tarema, nifa kai........"
Kara Fulani ta saki, hakan yasa Ishaq yin shiru, Salman ya kalleta yace " aya Umma ta shiga wani hali, yazakiyi Umma gashidai Ishaq yafad'i komai da bakinsa."
Ishaq ya kalleta yace "Umma inafa da wayau hauka nake zan fad'amai, karyar Salman ne kawai yana za'ayi yasan nina je bigeshi bayan bai kula ba? Sai dai in yau yake nufi, wannan kuwa ai shiyakamani....."
Fulani mik'e wa tai cikin b'acin rai ta zo kusa dashi ta haska mai mari, tace wlh Ishaq nikam banyi sa'ar d'aba.
Sarki ya fusata yace ke Sakina! Ai duk fadar sai da kowa ya juyo, cikin sanyin jiki Fulani ta zauna Ishaq kam ido yai wuri wuri, Sarki cikin b'acin rai yace "banataraku anan bane kowa yai abinda yaga dama ba, kuma duk abinda kukama Salman dake da d'anki karkuyi tunanin zan kyaleku, ada na d'auka kina kula da Salman, a'a koma bakya kula dashi banyi tunanin zakuma ku had'u keda d'anki ku muzguna ma Salman ba, yanzu da sanda ya bige Salman ya mutu fa? Sannan ko kunya harya samu damar shiga d'akinsa neman matarsa? Gidana yakoma gidan dabobi kenan ko me? To wlh daga shi har ke dakike biyemai sai kun fuskanci hukunci mai tsanani."
Ishaq yasa kuka yace " Abba d'an Allah kayi hakuri nasan nayi laifi, wlh ni tun ina karami da k'in Salman na taso, kullum umma zancenta d'aya ne kar in kuskura in bari Salman ya wuceni akomai."
Sarki ya kalli Fulani datai kasa da ido, da alama itama kwalla ke zubo mata.
Sarki ya kalli Salman sannan ya kalli Ishaq yace " na cireka a matsayinka na yarima mai jiran gado, sannan nakuma bama Salman wannan mukamin."
Fulani ta d'ago ta kalleshi cikin tsananin b'acin rai tace me kake nufi mai martaba? Ishaq shine babban d'anka a tunanina duk abinda yai zaka yafemai tunda shine magajinka kuma ni danake uwar gida, Fulani nice ya kamata d'ana yazama Sarki."
Jitai Sarki yace " ahh namanta, gwara da kika tunamin kema ina sanar dake matsayinki na Fulani na cireshi daga yau......."
Salman yace " Abba!!!"
Sarki yace " kamanta na sanarma bazan yafema duk wanda ya nemi kad'eka ba? Sannan ko kunya Ishaq ya nemi matarka? Kuma duk nasan lefin mahaifiyarshi ce."
Fulani cikin kuka tace" Alhaji ni zakawa haka? In ka cireni daga mukami na nida Ishaq alama ce ta mu mutu kawai, dama nasan ba sona kake ba, amma duk da haka bai kamata kamin haka ba."
Sarki yace " kin d'auka shi kad'ai ne? Nasani sarai in na kauda Ishaq zakiyi tunanin saka Mannir ko wani daga cikin d'anki, bazaki tab'ajin kunyar abinda d'anki ya aikata ba, dan haka na yanke hukuncin dolene kibar nan gidan ki koma can karshen gida( inda ake kai iyayen sarki insun tsufa sosai ) anan zaki zauna."
Salman yace " Abba? Hukuncin kamar yayi tsauri." Sarki bai bashi amsa ba ya kalli Fulani dake kuka sosai tana bada hakuri, sannan ya kalli Ishaq yace kaikuma kashirya kaida iyalanka kubar nan ku koma kasar Egypt dazama kada kuma kadawo har sai in nina bada izinin hakan."
Abba yana gama fad'ar haka ya mike yai cikin gida, Fulani tasa kuka, Ishaq ma kuka yake sosai yana cewa "Salman d'an Allah kataimakemu, ni wlh duk Umma ce, laifina d'aya danafara san Salma wannan kuma Salman kasan ba laifina bane laifin zuciya ne. "
Salman ya kalleshi shikanshi tausayin hukuncin da Abba ya yankr yakeyi.
By *Ayusher Mohd*📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
No: 6⃣0⃣
Salman ya kalli Ishaq duk sai kuma yaji Ishaq d'in na bashi tausayi, Waziri ne ya shigo ya kalli Salman yace " Yarima mai martaba yace ka ciga ciki."
Salman ya kalli Waziri yace " Toh" mik'ewa yai ya d'an bugi kafad'ar Ishaq sannan ya kalli Fulani dake kuka yai ciki, Fulani tabishi da harara tare dacewa" niza'a wulakanta akan wani banza Salman? Wlh Sarki yayi kuskure."
Ishaq ya matso kus da ita ya riko hannunta yace "Umma kitaimakeni kisa abarni akasar nan, ni wlh na tsani wata kasar."
Fulani ta wafce hannunta tace " wato kanka ka sani kad'ai ko? Ni baka tausayin inda za'a kaini? A k'alla in na zauna acan kila sai nayi wajen sati 3 zuwa wata kafin 'ya'yana suzo su ganni."
Jisukai Waziri yace " ku fito daga fad'a ba gurin hira bane, sannan kai yarima Ishaq katabbatar ka shirya d'an gobe zaka wuce, sannan Fulani au hajiya kema ki had'a kayanki yau dan gobe da safe zaki koma."
Yana kainan yai waje, Fulani ta zuciya tace "me? Au hajiya? Sai na ci*********, "
Ishaq ya kalleta yace " nidai Umma yanzu ba lokacin wani zagi bane ya kike so nayi?"
Fulani ta watsamai wani kallo tace " duk ba kaikaja ba d'an rainin hankali, dalla matsamin." Ta fad'a tare da wucewa.
Ishaq ya dunkule hannu ya naushi bango, yace " ni dai rayuwa ta gama b'aci, bansamu Salma ba, bansami mulki ba, garin muma yanzu ya fi karfina."
Shima waje yai jiki a sanyaye.
Abinda zai baka mamaki kafin si fita zancen har ya yad'u agidan Sarki, suna tafiya bayi na kallansu suna d'an gulma.
Salman zaune a gaban Sarki, Sarki yace" hukuncin baiyi ba kome?" Salman ya kara kasa dakai yace "a'a ba haka nake nufi ba sai dai ina ganin kamar hukuncin ya musu tsauri. "
Sarki yai murmushi yace " mutanen da sukaso yin kisa? Da kuma hukuncin neman matar wani? Shine kake cewa d'an wannan hukuncin yai musu yawa? To ko kotu zan kaisu? Sai a banbance wanne yafi tsauri."
Dasauri Salman yace " a'a Abba masan can sai yafi tsauri."
Sarki yace " karka wani damu da wannan, ka maida hankalinka akan karatunka, inka gama kazo ka amshi mahaifinka."
Salman yai shiru.....
Hakan yasa Sarki yace " yaushe zaku fara jarabawa?"
Salman yace " saura sati d'aya."
Sarki yace " good gwara ku gama kafin lokacin da likitan nan zai iso."
Salman yai murmushi tare da cewa " amma Abba taron nad'in daza'amin a bari sai nagama ganin likitan." Sarki ya d'aga kai yace " hakan ma is a good idea."
Sunyi shiru kafin Salman yace "bari inkoma Abba, sai da safe."
Sarki ya amsa mai, nan ya mike yai waje.
Mutane sai tayashi murna suke, shidai tafiyarsa kawai yake ba wanda ya amsawa, b'angarensa ya nufa, Salma na zaune a falo duk da ba kallo takeyi ba amma ta kurama tv ido, hankalinta nakan abinda hanne tace mata wai anba Salman yarima mai jiran gado, batama san sanda Salman ya shigo ba ya tura kofar tare da matsowa saitin wuyanta ta baya yace " me Beauty take tunani?"
Da sauru ta juya d'an tad'an tsorata, tace "haba Prince nafa tsorata. " tai maganar cikin shagwab'a, shima kwaikwayar tata maganar yai yace " nima na tsorata" yasa mata d'ariya tad'an d'akeshi kad'an ya rike hannun tare da d'agota tayo jikinshi, hannunsa yasa a k'ugunta yace " bari mu gani ko Beauty tayi missing d'in mijinta sosai?" Yafad'a yana duba fuskarta, saurin rufe idanta tai, tace " ta ina ake gane wa?" Yace in nuna miki? Ta d'aga kai.
Batai auni ba taji bakinshi anata, sosai yau take maidamai sun shagala sosai, kafin su saki juna, ahankali suka bud'e ido tare dayima juna murmushi, Salman ya kamo hannunta yai d'aki da ita, suna shiga ya rufe kofar ya tsaya ajikin kofar, ta matso kusa dashi tace " Prince baka fad'amin. ......jawota yai yakara kai bakinsa nata, nan suka kara tsundumawa cikin shauki, nikam har yanzu ban manta da korar da Salman yamin ba hakan yasa nai sumsum sum nai waje, tare da kara rufo musu kofar.
Bayan sun gama Salman yad'au Salma ya kaita toilet tace " au toilet d'inma bazan iya zuwa ba ko me?" Salman yace "banaso a wahalar min da baby na." Tace uhmmm.....harzai fita ta riko hannunsa, ya kalleta tare da mata alamar tambaya, itama dakai ta nunamai, ya kara mata alama dakai na bai gane ba, murmushi tai tace " muyi tare, " shima murmushin yai yace "ahhhh yau naji dad'i na.
Sunyi wanka sun fito, Salma ta wuce falo tad'an zubo ma Salman abinci kad'an a plate, ita da kanta tabashi, sai daya gama yasha ruwa sannan ta maida tare da hawa kan gadon, Salman ya jawota jikinsa yace " Beauty akwai matsala fa? " ta kalleshi tace name? Nan ya sanar da ita abinda ke faruwa.
Tai shiru, kafin can tace"Allah yasa hakan ne mafi alkairi." Salman yace "Amin, amma Beauty nifa banasan harkar mulkin nan, duk abi a hana mutum sakewa, ni dake fa sai lokaci_ lokaci ni kuma banasan hakan." Gabanta ne ya fad'i tace "lokaci_ lokaci? Muna gida d'ayan?" Yace" hmm yanzu in akaban me jiran gado, nasan halin mai martaba abubuwa zai d'inga sani, kinga zama na dake dole zai rago."
Salma ta kalleshi jitake kamar tai kuka, sai dai tana tunanin ko bazata ji dad'i ba dolene ta karfafama mijinta, tace " to menene baga waya ba? " tafad'a tare da nuna wayarta, yace uhmmm, ta shige jikinshi tace " bacci nake ji.
Ta dade batai barci ba, har Salman yai bacci, tai shiru tare da kura mai ido itakad'ai tasan meke ranta.
Ishaq kam da Fulani da matan Ishaq bana tunani sunyi barci dan dukansu ba wanda yake farinciki.
By *Ayusher Mohd*📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
No: 6⃣1⃣
Da safe Salman yace Salma ta shirya yakaita gida, bayan ya kaita ya gaisa dasu Abba sannan yajuya ya koma gida, sam bayasan Salma takasance a gida arana irinta yau da gidan zai kasance a hargitse.
Waziri da wasu fadawan ne sukazo suka tsaya a b'angaren Ishaq har sai da matanshi suka gama had'a kaya, kana kallan fuskokinsu kasan tabbas suna cikin bakin ciki.
Fulani kam kuka sosai tai cikin dare sai dai da safe tana zaune tana kallan bayinta na had'a mata kayanta, ita kad'ai tasan bakin cikin dake damunta ga rabuwa da d'anta, matsayinta sannan korarta da akai, kana kallanta kasan bakin ciki ne fal zuciyarta.
Salman yafito yai b'angaren Ishaq, ganin su waziri a tsatsaye yasa shi mamaki, karasawa yai suka gaisa ya tambayesu meke faruwa yagansu haka? Waziri yace" mai martaba ne ya umarcemu da mu tabbatar mun tsaya harsai Ishaq ya bar gidan nan ya shiga jirgi."
Salman ya kalli Waziri yace " haba a tunanina ko ba'a tsareshi haka ba zai tafi dakansa tunda yasan umarni ne ba shawara ba."
Jiyai Ishaq yace " Salman inasan magana dakai." Salman ya juya ya kalleshi duk ya canza a kwana d'aya, binsa yai suka d'an keb'e, Ishaq ya kalli Salman yace " Salman nasani tunda kadawo kasarnan nake muzguna ma, bana kunyar yimaka sharri ko agaban mai martaba ne, ko ba'a fad'aba nasan bai kamata inma d'an uwana haka ba, amma azahiri kai kasan duk inda gidan sarauta yake to tabbas akwai hassada, kyashi da kuma san kai a ciki, sai dai bazan nemi yafiyar ka akan sharrin dana maka ba, dan nasan ko kaine ba shakka hakan zakayi, sai dai zan nemi yafiyarka akan abu biyu, na d'aya bigeka danaso yi, sannan neman matarka danai." Yana kai nan yai ajiyar zuciya idanunsa suka cika taf da kwalla.
Salman ya kalleshi cikin tsananin tausayi, ya runtse ido sannan ya bude tare da cewa" Mubar zancen nan, dana yanzu dana da banasan adinga tunowa, abu d'aya nakeso kasa aranka, a duk inda kake kazama mai so wa d'an uwanka abinda kake sowa kanka, karka manta wannan kalmar hadisi ne sahihi, duk wani abu daya shiga tsakanina dakai nayafe ma."
Ishaq ya kalleshi cikin hawaye ya riko hannunsa cikin kuka yace "Salman please take care of my mother, nasani she is so greedy, amma tunda nake da ita bata tab'a bani shawarar neman Salma ko kad'eka ba, duk da batasanka."
Salman ya dafashi yace " karka damu I will take care of her, amma inkaje can me zakayi?"
Ishaq yace " ban mayi wannan tunanin ba."
Murmushi Salman yai yace " u have to make plan, dan karkaje kawai kace zama zakai kaga dai zama ne bama shekara ba, mayb inka tafi ba dawowa zakai ba."
Ishaq yace " nagode Salman."
Salman dakanshi yakaisu airport da azahar suka tashi, baiji dad'in yanda Sarki ya had'ema Ishaq rai ba dayaje masa sallama.
Yana dawowa gida yatadda Fulani har ta tattara ta koma, yai ajiyar zuciya yace " why am I feeling so empty? "
Salma kam taji dad'in zuwa gidan nan tayi mamakin yanda aka gyara gidan, sam bazakace gidansu ne na da ba, goggo sai janta a jiki take, sun sha hira da Abbanta, nan ya fad'a mata ai kamal ya kusa komawa kasar waje d'an yin masters d'inshi, takalli Abba tace " Abba zanma Salman magana, akwai naga mutanen da ake d'eba na scholarship a gidan Sarki, duk da dai naga 'yan uwane yawanci amma nasan in namai magana zaisa sunanshi"
Abba yace kina ganin ba matsala?
Tai dariya tace " yasan komai Abba ba wata matsala. "
Salma duk yanda taso suyi hira da umma amma abin ya gaggara hakan yasa ta hakura ta koma gun Abbanta.
Sai bayan magrib Salman yazo, sun gaisa da Abba sai daya shigo yaga gyaram gidan da akai lalai komai yayi kyau, Abba ya kara mai godiya sosai sannan yagaudasu umma da goggo, sannan suka fito.
A hanya ne Salma ta sanar dashi zancen kamal, Salman ya mata wani kallo yace " tsohuwar zuma ce ta motsa?" Dariya tai tace " ai kafi kowa sanin ba wata tsohuwar zuma araina, daga sabuwae har tsohuwar mutum d'aya kawai nasani."
Kallanta yai yad'an d'age gira yace "mutum d'ayan dai ko ba'a fad'a ba nasa nine."
Tad'an murgud'a baki tace "irin wannan confidence haka?"
Yace "kinsan nayarda dakaina, no doubt. "
Tace "ahhhh namanta ne, but what can we do? Sai kuma yakasance bakai bane Mr self-assurance?"
Salman ya kalleta yace "ban gane ba?"
Tad'an langwab'ar da kanta batace komai ba.
Salman cikin b'acin rai yai gefe da motar yai parking, ta guntse dariyata tare da maida kanta tana kallan window, Salman yasa hannu ya juyo da fuskarta, yace " Beauty magana nake." Juyowa tai ta had'e rai tace " inaji Mr self-assurance."
Yace " me kike nufi da kalamanki?"
Tace " me nake nufi kuwa?"
Yace " karkisa naje na fasama kamal baki wlh, dama inajin haushi banine first love d'inki ba kar ki kara b'atan rai."
Dariya ta kwashe dashi tace " Prince kanada abin dariya wlh, ni fa matarka ce banasan mud'inga zancen wani kamal inbadai aharkar 'yan uwan taka ba."
Yace " to ai kece kika zo min da magana abaibai."
Salma tace "uhmm nad'auka Mr Prince duk abaibai d'in danai magana zai gane, tunda dai shi ya koyamin."
Salman yace " ohhh dama saboda ni kikai? Band'auka kema kin koyaba ai."
Tace "ina zaune dakai ai dole ne."
Kunnenta yad'an ja tace ahhh, yace " ramawa nai......dariya sukai atare, nan suka wuce gida.
Yau Salman sun gama jarabawa kuma a yau akesa ran za'a kwantar dashi a asibiti danyin treatment, dan yau da yamma akesa ran zuwan Dr Bilal da matarsa Dr Ilham.
Salma ta had'a musu kayansu a akwati, duk yanda akaso a hanata zama acan saboda larurarta amma taki, hakan yasa sarki yace akyaleta, Fulani kusan kullum sai tayi abun marmari ta aikoma Matar Munnir dake da ciki da kuma Salma, Salma kam tsoron ci takeyi sai dai ganin mai kawowar bata take ta zab'a kafin takaima matar munnir yasa ta fara rage kokuntan ko magani ne a ciki.
Farha kam mahaifiyarya taji bakin cikin korota da akai, sai dai yazasuyi? Da Mumyn ta kira Sarki dan tai fad'a sai ya gwaleta yace " yama za'ayi ace yarinya takai shekara 25 amma ba zaku mata aure ba? Sai dai tai ta yawo a gari, wannan dalilim yasa tama daina kiran Sarkin.
By *Ayusher Mohd*📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
No: 6⃣2⃣
Bayan Shekara 3...........
Salman zaune akan dinning shida d'ansa Salim, Salma tazo kusa dashi ta zaune tace " Prince dagaske kake wai?"
Salman ya kalleta sannan ya shafa kan Salim yace " Beauty wai dole ne sai naje wani matriculation? Ni yaro ne?"
Salma tad'an had'e rai tace " yara ne ke zuwa?" Salman ya kalleta zaiyi magana wayarshi tai kara yad'aga tare da cewa " Najib ya akai?" Najib yace " malam Yarima mai jiran Gadon Sarki bawai dan anaso Sarki ya mutu ba sai dan hakan Al'ada ta tsara."
Saki yai yace " kafara ko? In roko ka fara to zan iya taimaka maka da kalangu."
Najib ya kwashe da dariya yace " kaii mutumin akwai iya fad'ar bakar magana, yah zaka shigo kuwa? Su dad zasuzo fa."
Salman yace " kai fa banza ne, meyasa baka sanar dani da wuri ba? Gashi nikuma banda niyar hallatar taron."
Najib yace " haba yarima kafasan yanda Director yabada umarnin kaje saboda akwai kyauta dasuke san baka."
Yai wani murmushi yace" kyalesu so suke suyi neman suna gun mai martaba, ko an fad'a musu ban sani bane."
Najib yace " to yanzu ya za'ayi?"
Salman yace" zanzo bayan an gama sai mu gaisa dasu Dad d'in."
Nan sukai sallama ya kashe wayar.
Salma ta kalli Salim tace" Ma boy jeka akaika gun Fulani tun jiya take aiken nemanka."
Cikin murna yace to.
Yana fita Salma ta harari Salman tai d'aki, murmushi yai tare da mik'ewa yai d'akin, tana zaune akan gado, yana zuwa ya kwanta akan cinyarta, tare da sai ta fuskarshi kan nata, yace " Beauty muje yawo?"
Salma tace " indai bazaka ba shikenan, dama bansan mai martaba yaga baka hallarci taron bane. "
Salman ya shafa cikinta yace " Baby na kinga Mumynki na neman tilastama mahaifinki abinda baya so ko?"
Salma ta shafa kan Salman tace "kaima kasan ba haka bane Abba nasan Umma bazata ma haka." Tai magana amatsayin wai babyn
Ajiyar zuciya yai yace " Babyna I wish mace ce mai kama da Beauty na kinga sai in mata rival, ni dama ban tab'a ganin magajin Sarki da mata d'aya ba sai ni."
Salma tai dariya tare da manna mai kiss a kumatu tace " na daina tambayar tunda an fara zancen rival."
Shigewa jikinta yai tad'an mai shakulkuli ta ciki tace " kar ka matse mana babyn mu."
Yace 3mnt ko? Tace yeah
Turata yai kan gadon tare da jawota jikinsa, yace " Beauty wai sai naje?" Ta girgiza kai alamar a'a tace " Ur choice. "
Ahankali ya kai bakinshi nata............
Ya shirya tsaf ya kalli Salma yace " Zan wuce." Tace sai ka dawo, Allah ya bada sa'a." Yace amin "amma taso muje tare indai kinaso naje."
Murmushi tai ita kanta tanason zuwa, gyara fuskarta tai, Salman yakalleta yace " ni fa banasan zuwa dake gun taro, maza suyi ta wani kallanki, narasa meyasa Abba kwanakin nan yai ta sakamu hallarta taro tare, haushi duk ya isheni."
Dariya tai tace" to ko inzauna?" Yace " yau ni nakeso muje tare saboda nasan kinasan zuwa, koba yau zee zata gama ba itama? Sannan inaso kiga matar da Najib zai aura."
Nan suka gama kintsawa suka fito.
Wata had'ad'iyar Motarsa mai masifar kyau suka shiga, sam yanzu anhanashi fita shi kad'ai, hakan yasa dole akwai mota d'aya da akesa fadawa suke rakashi inda zashi.
Yafara tuki tare da kallan bayanshi ya kalli motar haushi ya isheshi, yai kwafa yace " Who am I?" Salma tace" The Prince!!!!!" Yai wani mugun murmushi yace " Sa belts dear." Tasa tare da cewa me za'ai? Ya kalleta yai murmushi tare kara gudun motar, nan yadinga shiga cikin d'an lungun hanya daya gani, sun rikece suna binshi, sai dai ina, salon da Salman yake musu yasa sun rasa inda yai.
Sai dayaga ya b'acemusu b'at sannan yai wani murmushi, Salma ta tafa mai tace " irin wannan salo?"
Yace "inama ni ba d'qn sarauta bane, da mota zan koya miki mud'inga fita bayan gari muna tsere."
Dariya tai tace " stop Imagine, nikam kuna waya da Dr Bilal?"
Salman yai murmushi yace " guy d'in nan da matarsa sunyi, ba sa'idan kowa akansu, rayuwarsu free."
Salma tai shiru, can tace" amma fa ance aunga rayuwa, sai dai naji dad'in yadda yawarkarmun da My Prince."
Murmushi sukai Salman ya wuce skul d'in dadinshi d'aya bai fad'a ma fadawar inda zasu ba, kuma a iya saninsu bazai je makaranta yau ba.
Anyi taro lafiya Salman an kirashi ya amshi kyauta amma yanajinsu ya sharesu, sai Mannir ne ya amsar mai a matsayin sa.
Salma tayi farin cikin ganin zee, sunsha hira nan Zee take tambayar Salma labarin Kamal, Salma tace yana can naji Abba yace ya samu aiki acan, zee tace lalai.
Ishaq kam yanzu rayuwa tazama saisa saisa, duk da ana tura musu kud'i kuma yana karatu, amma yanzu ya koma shiru shiru, sam bayasan garin, amma ya zai yi?
Fulani kam an shiryu kusam kullum sai ta nemi akai Salim da kuma 'yar gidan Mannir( Zulfa) sun tayata hira.
Farha kam anata shirin bikinta, Salman yace zasuje shida Salma....
...........
After 6years...........
Salman zaune akan kujerar mulki, yana karanta korafe korafen mutane, wazirinsa na yanzu shine ya kalleshi yace "Ranka ya dad'e bai kamata ace har yanzu matarka d'aya ba."
Salman ya bugamai wani kallo yace" in na kara auren kai zaka rik'emin matar? Ko kuwa mutanen dakesan in aure 'ya'yansu suke turoka su zasu zaunamin da ita? ."
Waziri ya had'iyi yawo yace" ya hakuri ranka ya dade ba haka nake nufi ba."
Salman yace " ko ma me kake nufi, sannan ban fahimci wannan takardar ba."
Waziri ya kalli takardar, yace " eh wani babban d'an kasuwa ne yakeso kad'an taimaka mai da sa hannu."
Salman yai tsaki tare da wurgo takardar yace " ina sa mai hannu sai yaje yai ta shigo da kayan da basu dace ba yace nine na bada izini ko?"
Waziri yace "ba haka bane, zai d'inga aiko da kud'aden da kadarori masu yawa ai."
Salman yai murmushin sa yace" bama bukatar kud'insa in bazai abu dan Allah ba ya barshi, sannan kar in kara ganin takardu shigen wannan anan gurin."
Waziri yad'an tab'e baki a zuciyarsa yace " wannan wani irin mutum ne? Yaza'ayi mu tara arziki in baya.....
Salman ne ya katseshi yace jeka na sallameka, waziri ya mike yana fita yai ajiyar zuciya yace" kaiii!!!!!! Haka zan d'inga fama kullum?"
Salman kam yana ganin waziri ya fita ya kira Salma, tad'aga da sauri tare da cewa "My Prince gaskiya I miss u."
Yace "mee too dear, ina Swty na?" Tace gani nan.
Yace " not u new nake nufi, murmushi tai tace gatannan tana barci."
Yace shafamin kanta....tace yaushe zan ganka? Yace yau da aiki amma zan tsagaita inshigo, tace sai na ganka.....
Nan sukai sallama tabi wayar da kallo, ga shi dai yanzu arziki itada 'yan uwanta ba'a magana, ga matsayi na Fulani an batan ga yaransu guda Uku, 1 namiji, 2 mata, sai dai tarage zama da mijinta sosai, yazatai haka rayuwa take ba'asamun komai dole in an samu d'aya a rasa d'aya.
*ALHAMDULILA NAN NAKAWO KARSHEN LITTAFINA MAI TAKEN 'NI DA PRINCE' BANSAN IYA YAWON GODIYA DA ZAN NUNAMA D'UNBIN MASOYANA BA, NAGODE KWARAI DASO DA KAUNAR DA KUKA NUNA MA LITTAFINAN, ALLAH YABARMU TARE........*
*THANKS ALOT ALL MY FANS.....LOVE YOU SOOOOO MUCH*💋
*Godiya ta musamman ga duk 'yan group d'ina, dakuma 'yan uwana writers nagode sosai Allah yasaka da alkairi da zumunci da san da kuka nunamin.*
_*Jinjina Gareku ' yan Nagarta Writer's Association nagode kwarai Allah ya kara d'aukaka*_
My fans sai kunjini a sabon novel d'ina nan gaba........
By *AYUSHER MOHD*📚
© *NWA*