Ma’aikatar jihar Jigawa sun samu hutun kwana daya domin su taya shugaban kasa addu’an samu lafiya
Majalisar zartarwar jihar ta yanke shawarar a zaman ta a ranar Laraba
Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana ranar juma'a,7 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu ga ma’aikatar jihar don a yi ma shugaban kasar Muhammadu Buhari addu’a na musamman a kan kiwon lafiyar shugaban.
Jami'in hulda da jama'a a ofishin shugaban ma’aikatar jihar, Alhaji Isma'il Ibrahim ya sanar da wannan a cikin wata sanarwa a Dutse a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni.
Gwamnatin ta ayyana ranar juma'a a matsayin ranar hutu domin ma’aikatar jihar su samu daman yi ma shugaban kasar Muhammadu Buhari addu’o’i.
A wannan rana, an sa ran cewa duk ma’aikata da dukan al'ummar jihar za su yi addu'a ga Allah Madaukaki ya ba shugaba Buhari lafiya ya kuma dawo da shi kasar lafiya.
Haka kuma ana sa ran cewa za su kuma yi addu'a ga Allah Madaukaki a kan marigayi Danmasanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule cewa Allah ya sa Jannatul Firdausi ne makomarsa.
Title :
Mutanen jihar Jigawa gaba daya za su yi ma shugaba Buhari addu'a na musamman a ranar juma'a kan kiwon lafiyarsa
Description : Ma’aikatar jihar Jigawa sun samu hutun kwana daya domin su taya shugaban kasa addu’an samu lafiya Majalisar zartarwar jihar ta yanke shawa...
Rating :
5