Jim kadan da bayyana sauke duka Kwamishinoni da masu bada shawara da Sakataren Gwamnatin jihar Bauchi da Gwamna yayi ya sanar da nada, Alhaji Mohammed Nadada Umar a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin jihar Bauchi
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Gwamnan, Malam Abubakar Al-Sadique ya fitar yace nadin ya fara aiki anan take.
WANENE MUHAMMAD NADADA
An haifi Alhaji Muhammed Nadada a garin Dambam ta jihar Bauchi a ranar 31 ga watan Disamba,1954.
Ya yi karatunsa a makarantar Gwamnati ta GSS Azare, sannan ya karanci fannin shara'a a jami'ar ABU Zaria kafin daga bisani ya koma kwalejin koyon shara'a ta Nigerian Law School a 1980.
Alhaji Nadada Umar yayi ayyuka a wajaje da dama ciki har da ma'aikatar shara'a ta jihar Bauchi daga 1978 zuwa 1980, sannan ya koma hukumar muhalli da zuba jari ta jihar Bauchi daga 1980 zuwa 1984.
Ya kuma yi aiki da bankin New Africa Merchant Bank Limited daga 1996 zuwa 1999 a inda aka nadashi sakataren Gwamnatin jihar Bauchi daga 1999 zuwa 2006 a lokacin da yayi murabus.
Madogara: Hausa Times
Title :
Mohammed Nadada Umar Ya Zama Sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi
Description : Jim kadan da bayyana sauke duka Kwamishinoni da masu bada shawara da Sakataren Gwamnatin jihar Bauchi da Gwamna yayi ya sanar da nada, Alha...
Rating :
5