Matasa sun ja hankalin Fayoshe da ya maida hankali gun shugabantar da jiharsa a maimakon bata lokaci a abinda baida anfani.
Kungiyar matasa magoya bayan Buhari na yankin Jihar Legas ta nemi gwamna da ya kame bakinsa daga munanan lafuzza da yake furtawa gameda lafiyar shugaba Muhammadu Buhari.
Mai gudanar da lamurran kungiyar, da babban magatakardar kungiyar Mista Waheed Odunuga da Mista Adekunle Aderibigbe, sune sukayi wadannan jawaban a Juma'ar yau a Jihar Legas.
NAIJ.com ta nakalto bayanansu cewa ya kamata ace gwamnan ya fita batun waki'ar da ta auku a shekarar 2015 a baya, kuma ya fuskanci abinda ke gaba na cigaban kasar Najeriya.Tabbas kam shugaba na samun kula game da lafiyarsa a turai , kuma Mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ya tabbatarwa da mutane cewa nan ba da dadewa ba zai dawo kasa a cikin koshin lafiya, sakamakon haka babu bukatar yawo da jita-jitar da fayoshe yakeyi gameda lafiyar shugaban.suka kara da cewa Ya kamata ace gwamnan ya shiga taitayinsa gun kawar da kai daga abubuwan bata lokacin da bazasu kari mutane da komai ba.
Sun shawarci Fayoshe da yayi tunanin sarrafa ma'adanan kasa na jiharsa gun ganin cigaban harkar noma da sauransu don cigaban jihar, hakan shine zai bawa masu hannun jari damar shiga jihar tasa don bunkasa ta.
Zama lafiya da tabbatarda tsaro abune da ya shafi kowanna gwamna a kasa baki daya.
Title :
Matasa Sun Gargadi Gwamna Fayose Da Ya Iya BakinsaGame Da Lamarin Buhari
Description : Matasa sun ja hankalin Fayoshe da ya maida hankali gun shugabantar da jiharsa a maimakon bata lokaci a abinda baida anfani. Kungiyar matasa...
Rating :
5