Manchester United ta amince ta sayi dan wasan gaba na Everton Romelu Lukaku kan kudi fan miliyan 75.
Dan kwallon mai shekara 24 na kasar Belgium ya zira kwallo 25 a gasar Firimiyar da aka kammala.
United, wacce ta dade tana neman Lukaku, ba za ta ci gaba da neman dan wasan Real Madrid Albaro Morata ba.Tawagar ta Jose Mourinho na fatan kammala cinikin dan wasan kafin kungiyar ta tafi Amurka domin atisayi ranar Lahadi.
Lukaku na cikin jerin sunayen 'yan wasa da Mouribho ya bai wa mataimakin shugaban kungiyar, Ed Woodward kafin karshen kakar wasan bara.
A da ana ganin Lukaku zai koma tsohuwar kungiyarsa ta Chelsea ne, wacce ya je daga Anderlecht a 2011.
Mourinho ne ya sayar da dan wasan gaban a kan fam miliyan 28 ga Everton a lokacin yana kocin Chelsea a karo na biyu a shekarar 2014.
Mino Raiola shi ne wakilin Lukaku, kuma shi ne wakilin Paul Pogba, da Zlatan Ibrahimovic da Henrikh Mkhitaryan - 'yan wasa uku da United ta saya a kakar wasan bara.
BBCHAUSA
Title :
Manchester United Za Ta Sayi Lukaku Akan Miliyan 75
Description : Manchester United ta amince ta sayi dan wasan gaba na Everton Romelu Lukaku kan kudi fan miliyan 75. Dan kwallon mai shekara 24 na kasar Be...
Rating :
5