Yadda Man City ta lallasa Real Madrid
Manchester City ta lallasa Real Madrid da ci 4-1 a Los Angeles a wasan sada zumunci da suka buga domin shirin tunkarar kakar wasa ta bana.
Kociya n City Pep Guardiola ya ce Benjamin Mendy wanda ya saya kan kudi fam miliyan 52 ba zai taka leda na mako biyu ba bayan wasan na Amurka.
Mutun 93,000 ne suka kalli yadda City ta samu nasararta ta farko a wasannin shirin sabuwar kaka da kwallaye daga Nicolas Otamendi da Raheem Sterling da John Stones da kuma dan shekara 17, Brahim Diaz.
A rashin Mendy, Danilo ya buga wasansa na farko a filin wasan Los Angeles Memorial Coliseum, inda mai shekara 26 din wanda dan asalin kasar Brazil ne ya buga baya ta gefen hagu.
Ya dai fuskanci tsohon kulob dinsa bayan Man City ta saye shi kan kudi fam miliyan 26.5.
Bbcsport
Title :
Manchester City ta Lallasa Real Madrid daci 4-1
Description : Yadda Man City ta lallasa Real Madrid Manchester City ta lallasa Real Madrid da ci 4-1 a Los Angeles a wasan sada zumunci da suka buga domi...
Rating :
5