Kotun dai ta yanke hukuncin biyo bayan kara da wata kungiyar farar hula mai da’awar adalci “SERAP” ta shigar don bukatar a fito da bayanan karkashin kudurin dokar ‘yancin samun bayanai daga gwamnati da majalisar dokokin Najeriya ta amince da ita.
Kazalika hakan ya biyo bayan fitar da adadin kudi da a ka kwato a baya tun farkon gwamnatin Buhari da ministan labaru Lai Muhammed ya yi.A lokacin dai Lai Muhammed da ya baiyana adadin makudan kudin na Najeriya, Dala da Fam din Ingila; ya ce ba zai baiyana sunayen mutanen ba saboda bukaun lamuran shari’a.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya ratsa kan titi da daf da garin Wuro Dole a kan iyakar jihar Bauchi da Gombe inda motoci su ka tsaya cak da zirga-zirga na tsawon sa’a 3.
Motoci dai daga bangaren Bauchi da Gombe sun dakata a bangare biyu da jiran ruwan mai kukan kura da ya raba babban titin na gwamnatin taraiya ya na rimi wanda zai iya awun gaba da mota in ta nemi tsallakawa.
Ruwan dai ya ratso gonaki ya kirkiri gagarumar hanyar ruwa da ta ratsa titin.
Rahotanni na nuna ruwan sama a ‘yan kwanakin nan ya haddasa rusa gidaje da sanadiyyar mutuwar mutane da dama da ruwan kan dauke.
Taron majalisar zartarwar Najeriya ya yi tsit na tsawon minti daya don karrama marigayi Danmasanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule wanda Allah ya yi wa rasuwa a Masar bayan fama da jinya a ka kuma yi jana’izar sa a Kano.
Majlisar ta nuna kaduwa da rashin marigayin wanda ke sahun farko a ‘yan siyasar tarihi da su ka rage a lardin arewa.
Gwamnatin jihar Kano ma ta ba da hutun wuni daya don juyayin rashin maragayin.
Dattawan Da Suke Raye A Yanzu Ba Mu Da Yawa, Don Haka Matasa Ku Tashi Ku Soma Nuna Taku Hikimar, Sakon Obasanjo Ga Matasan Najeriya.
Nuna Goyon Bayan Kada A Yi Wa Dino Melaye Kiranye Da Sanatoci Suke Yi, Ya Tabbatar Da Zargin Da Ake Yi Na Cewa Majalisa Ta Lalace, Cewar Tsohuwar Minista, Ezekwesili.
Majalisar Wakilan Najeriya na shirin gayyatar tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan, domin bayyana abinda ya sani dangane da badakalar cinikin rijiyar mai OPL 245 na Dala biliyan 1.3 wadda aka fi sani da Malabu.
Ana zargin tsohon shugaban da hannun wajen yarjejeniyar sayar da rijiyar da aka kiyasta cewa na samar da ganga biliyan 9 na danye Mai ga wasu manyan kamfanonin Mai na ENI da Shell a shekarar 2011.
Ministan wajen Saudiyya Adel Aljubeir ya ce takunkumi da kasashen larabawa su ka azawa Katar zai ci gaba har sai Katar din ta sauya manufofin ta.
Dama Daular larabawa ta nanata irin wannan matsayi na ci gaba da matakin na takurawa Katar sai ta bi sharuddan da a ka gindaya ma ta ciki da wanke kan ta daga zargin marawa ta’addanci baya.
Matakin na larabawa ya kawo firgici a tsakanin al’ummar Katar da su ke rige-rigen sayen kayan masarufi don kar su yanke a kasuwa.
Wassu bankunan turai ma sun daina hulda da kudin Katar don rashin tabbas sakamakon takunkumin.
Title :
Kotun taraiya ta Najeriya da ke Lagos ta yanke hukuncin gwamnatin Najeriya ta saki sunayen tsoffin manyan jami’an gwamnati da ta kwato kudi a wajen su da kuma adadin sunayen mutanen.
Description : Kotun dai ta yanke hukuncin biyo bayan kara da wata kungiyar farar hula mai da’awar adalci “SERAP” ta shigar don bukatar a fito da bayanan ...
Rating :
5