Kamfanin sadarwa na Etisalat zai rufe kasuwancinsa a Nigeria ya fita daga kamfanonin sadarwar kasar nan da makonni Uku masu zuwa
Bayanin hakan ya fito ne a yau Litinin daga Babban shugaban kamfanin, Hatem Dowidar. Yace sun mika sanarwar hakan a rubuce ga mahukuntan kasar da sauran masu hannun jari a kamfanin.
Hausa times ta ruwaito cewa kamfanin Etisalat Nigeria ya ciwo bashin Dala Biliyan $1.2 wanda tun a 2013 suka kasa biya.
Mista Dowidar yace duk kokarin da akayi na shawo kan lamarin abun yaci tura saboda haka suka yanke shawarar ficewa daga Nigeriar
Madogara: Hausa Times
Title :
Kamfanin Etisalat Zai Fice Daga Nigeria Nan Da Makonni Uku
Description : Kamfanin sadarwa na Etisalat zai rufe kasuwancinsa a Nigeria ya fita daga kamfanonin sadarwar kasar nan da makonni Uku masu zuwa Bayanin ...
Rating :
5