Maman Aysha
[9/22, 18:32] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣0⃣5⃣➖1⃣1⃣0⃣
Washe gari da wuri na tashi na shirya cikin pink lace nayi dauri me kyau, nasa costume masu kyau, da dauki pink shoe & bag na fice, a motar da KB ya kawo min Mercedes 4matic 240 na tafi, INA zuwa na sami waje na faka motar, tunda na fito Mutanen cikin gun suke bina da kallo har na wuce office dina, Sbd bana shiga harkar kowa acikin wajen. Na zauna befi da 15 mint ba saiga shi ya shigo cikin wasu lafiyayyun suit fuskarsa manne da karamin farin glass din da yake kara masa kyau mikewa nayi nace gud morning sir morning kawai yace ya shiga office, ni kuma na koma na zauna naci gaba da aikina.
12pm
Ina zaune saiga wata kyakyawar budurwa ta shigo da body guards dinta har guda uku at least zataban 6yrs direct kofar office din KB ta wuce da hanzari na sha gabanta bewar Allah baa shiga sai anfada masa, wani kallon wulakanci ta watsa min ke kuma wacece? Kodan naga alamar ke bakuwa ce shiyasa baki sanni ba, aini banida Katanga da shiga office din ina shiga ne duk lkcn danaga dama. Kiyi hakuri nafadamasa Sbd zaki Iya jamin matsala, tsawa ta daka min dalla yimin shiru bansan ya akayi ya kwasoki ba ma, I must talk to him ya zama dole ya koreki wallahi stupid kawai, hayaniyar da yaji ne tasa ya fito yaga abinda yake faruwa suna hada ido naga ya saki wani lallausan murmushi what a surprise? Yaushe kika shigo garin? Da muryarta kamar ta aljanu tace dawowa ta kenan naji kai nake son fara gani, kuma nazo wanan so called sakatariyar taka ta hanani shiga. Yi hakuri mu karasa daga ciki yacewa guards dinta su koma office na biyu su jirata, sanan yace min ke kuma ki kawo mata drinks nace to. Lkcn dana shiga yana zaune kusa da ita suna hira cikin nishadi yanata sakar mata murmushin sa me tsada nan take naji zuciyata tayi zafi, naji gabadaya ba hargitse da kyar na Iya saita kaina naje na ajiye mata tray din a gabanta harna juya zan tafi tace me kk nufi, dawo ki zubamin, da facin rai nace ke baki da hannu ne? Kb ne ya kalleni yace obey her instruction she is my wife to be rasss naji gbna ya fadi, na nemi yawon bakina na rasa da kyar na samu energy n zuba mata, nace gashi hannun ta kawai ta miko ba tare da ta kalli cup din ba Sbd hankalin ta akan waya yake, nayi zaton ta rike na saki cup din aikuwa lemon ya zube ajikin mayafinta. A hanzarce ta mike ta kaimin mari, nayi saurin rike hannun ta me nayi miki da zaki mareni? Inaso ki Sani kowanne mutun yanada daraja, kasancewa ta ina aiki a karkashin mijinki bazai baki damar ki wulakantani ba. Aikuwa wallahi baki isaba saukin wanke min zanyi magana yace karbi ki wanke mata, ba musu na karba na wanke a sink din toilet dinsa saida na kade sanan na bazashi akan table din shi raina a bace na nufi kofa zan fita kawai sainaji tace banza marar asali.......Bata karasa ba ya wanke ta da mari cikin kuka tace akan wanan bastard din ka mareni? Inajin haka na fita da gudu ina kuka, Don't ever call her bastard and walk out from my office ta tsaya tana binsa da kallon mamaki cikin bacin rai yace I say out!! Tana rawar jiki ta dauki mayafinta ta fice tana kuka
Maman Aysha
[10/14, 9:52 PM] Chopy: [9/23, 13:16] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣1⃣0⃣➖1⃣1⃣5⃣
Tana fita ya zauna ya dafe Kansa Sbd be saba hayaniya ba, ya dade ahaka daga baya kuma ya dauki laptop dinsa da key ya fice ya tafi gd.
Zuby kuwa tana fita gdn wata friend dinta rumana ta nufa tana zuwa ta zube a falo tana kuka da sauri tace zuby me yake faruwa kk wanan kukan? Nida adon gari ne rumana, inayin hakuri da miskilancinsa da duk wani wulakanci da yake min Sbd INA masifar sonsa Amma yau har marina yayi Sbd wanan yar iskar yarinyar da aka gano Bata da asali, wacece yarinya kenan? Aysha A TURAKI, meye hadinshi da ita? Wai yanzu itace sakatariyarsa, kuma wallahi na tsani yarinyar kinsan tana da wani irin shu'umin kyau zata Iya kwacemin shi, kuma kinsan irin wahalar Dana sha kafin ya amince zai aureni, gaskiya kam Amma tunda hakane da makirci zaki koreta bada isa ba, yanzu ki kirashi ki bashi hakuri kinsan ance me nema baya fushi kiyita lallabashi har ki samu ya hakura, a hankali sai musan yanda zamu fillowa al amarin. Shiyasa nake sonki my friend har naji zuciyata tayi sanyi bari naje na tafi kinsan da body guards naje company nasa Amma Sbd bacin rai basu San na fito bama , bari nace musu su tafi kawai ni na wuce sai munyi waya to shikenan.
Zaune yake yana ta tunani, Allah sarki aysha rayuwarta akwai abin tausayi a ciki, ace mutun bashi da kowa ita kuma irin destiny dinta kenan, insha Allah zan rike amanarki har zuwa lkcn da zakiyi aure daidai nan phone dinsa ta fara kuka yana dubawa yaga zuby is calling... Kawai sai ya mayar ya ajiye, haka tayi ta kira har wajen 10 missed call, ko tunanin me yayi kuma? Data kara Kira sai ya dauka, ta naji yayi picking saita fara kuka don Allah sweet heart kayi hakuri, bazan Iya rayuwa bakai ba don Allah ka tausayawa rayuwata ka yafe min. Naji zanyi hakuri Amma sai kin gyara halinki, kuma kin bawa Aysha hakuri Sbd kinyi mata cin fuska, to to na amince insha Allah zanzo na bata hakuri gb, is alright Allah ya kaimu goben, bye.
Ni kuwa tunda na koma gd INA daki saida nayi kuka me isata kallama dayace take min yawo a zuciyata "she is my wife to be" dama adon gari yana soyayya? Dama yayi dating matar dazai aura? Amma na tafka babban kuskure dana bari zuciyata ta kamu da sonshi, ya Allah ka cire min sonshi a zuciyata da wanan tunanin wani wahallalan bacci ya dauke ni ban farka ba sai after 4, INA tashi na shiga toilet nayi wanka nayi alwala nayi sallar laasar wata English gown na saka na fita wajen baba mero tace yanzu nake tunanin naje na duba naga ko lpy, Sbd tunda kk shigo banji motsinki ba dariya nayi nace bacci ne ya kwashe ni shiyasa, me kika dafa mana? Abinda kk so nayi miki, kina nufin danwake? Eh kai Amma nagode shiyasa nake kara sonki baba mero, itama dariya take kitchen na shiga na zubo Iya yanda zan Iya ci, sanan na dawo falo inaci muna hira muna dariya, wayata ce ta fara kuka INA dubawa naga Barr Faisal ne, da sallama ta na dauka bayan mun gaisa yace kira nayi naji amsata, Aysha kinyi tunanin? Eh nayi kuma na amince da soyayyarka, alhamdulilla yace, saida, saidai me Aysha? Akwai maganar da nake so na fada maka, amma nafiso muyi face➖face, is OK zanzo in d night, yau kaina yana ciwo ka bari sai gobe, ayya iam sorry my dear Amma kinsha magani? Eh to Allah ya sauwake, bari na barki ki huta sai na kara kira bye. Ina kashe wayar baba mero tace waye wanan din? Sabon saurayi nayi sunansa Faisal, kuma kina sonsa? Sosai ma, ni kuwa sainaga duk duniya ba mutumin da kika dace dashi kamar kabiru, wallahi duk lkcn da nayi sallah sainayi addua akan Allah yasa kabiru ne mijinki Sbd halinku na tausayi da rashin kyamar mutun iri daya ne, Aysha kina da kyakkyawan halin da har yasa nake jinki kamar yata, kullum burina shine na ganki acikin farin ciki, don Allah ki amince ki auri kabiru kinji Aisha. Baba mero kenan, ke kike kidanki kike rawarki, shifa har yanzu be taba cewa yana sona ba, kuma fa yanada wacece yake so har ansa masa rana ma, maganar so kam na Dade da ganewa yana sonki, saidai da kikace ansaka masa rana shine matsalar, Allah yasa haka shi yafi alkairi nace amin
Washe gari
As usual INA office saiga Suleiman PA ya shigo, bayan yaje sun gama da adon gari ya fito sai ya zauna a wajena muna hira saiga ta ta shigo ta dau wanka tayi kyau sosai, INA ganin ta naji gabana ya fadi Suleiman ne yace miss zubaida barka da zuwa, yauwa Suleiman ya aiki alhamdulilla da gadara ta bude office din ta shiga wai wanan zuby din a ina take ne Sulaiman? Yar gdn minister of foreign affairs ce, kuma ita yallabai zai aura in Allah ya yarda, to nazle da tazo jiya fa? Ita kuma yar gdn commissioner of police ce, lbri yake ta bani, Amma gabadaya hankalina baya tare dashi, har saida ya fahinta, sai yayi min sallama ya tafi Mr kabeer ne ya kirani a waya yace nazo yana don ganina inda suka zauna jiya yauma anan suke, dama my Queen ce take so ta baki hakuri akan abinda ya faru jiya, eh hakane, kamar yadda swit heart ya fada miki zuwa nayi na baki hakuri Sbd wallahi nayi regretting sosai don Allah ki yafemin, nace ba komai Allah ya yafe mana baki daya zuciyata tana yimin wani irin zugi da radadi na kishi ban taba sanin son adon gari yayimin mummunar illa ba sai daga jiya zuwa yau, da kyar na Iya cewa zan Iya tafiya? Yace eh, ina juyawa wasu zafafan hawaye suka fara zuba a idona zama nayi na dora kaina akan table na fara kuka sallama naji anyi INA dagowa naga Faisal ne cikin rudani yace wat's wrong Aysha nayi sauri nace ba komai bacci nayi, lpy na ganka anan? Nazo naga Mr kabeer ne akwai wani aiki da zamuyi dashi, to bari na sanar masa, ina fada mishi yace ya shiga Ashe friend dinsa ne
Maman Aysha
[9/24, 12:12] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣1⃣5⃣➖1⃣2⃣0⃣
Yana shiga ya sami waje ya zauna yace Ashe kaida amarya ne? Yace wallahi kuwa, yau ta kawomin visit bayan sun gaisa suka tattana akan abinda ya kawo shi, sanan suka fito a tare har zuby. Ina cikin hada kayana Sbd lkcn tashi dama yayi naga fitowarsu Faisal ne ya karaso inda nake tsaye yana wani lallausan murmushi yace baby tafiya zakiyi? Cikin faduwar gaba nace eh, to muje nayi dropping dinki, thanks yau nazo da mota zubamana ido adon gari yayi yanamin kallon tuhuma, shi kuwa Faisal idonsa ya rufe yama manta da mutane a wajen, haka kawai adon gari ya tsinci Kansa da shiga damuwa, a INA Barr Faisal ya Santa? Yaushe suka fara soyayya? To ko shine yayi dropping dinta rana nan? Zuby ce ta katse masa tunani da cewa mu tafi swit heart cikin shan mur yace OK muje, A tare muka fita dasu saida ya rakani har bakin mota ya bude min na shiga sanan yamin sallama da sharadin zai zaizo bayan sallar magrib.
Tsaye suke ajikin motar sa suna sallama da zuby, amma gabadaya hankalinsa a wajen mu yake zuby ce tace amma na fuskanci Barr Faisal yana tsananin son yarinyar nan, kallo daya zaikai masa Kasan yayi falling da yawa saidai INA tausaya masa duk ranar daya gane bata da asali....enough me yasa bakinki baya shiru? Me yasa kk da taurin kai? So nawa kk so na fada miki maganar nan ta fita daga bakin ki, Karki bari na nuna miki bacin raina Sbd zaki sha wahala be jira driver shi ya bude masa motar ba ya bude da Kansa, kafin kace me body guards dinsa ma suka shiga motocinsu yau da motoci shida ya fito, cikin few seconds sukayi arranging din moticin suka fice daga wajen, itama jiki ba kwari ta bude motarta ta fita da tunanin wulakanci irin na adon gari.
Direct gdn mum dinsa ya wuce yana zuwa ya zube akan ciyarta banda shagwaba ba abinda yake, wash Allah wallahi mum na gaji sannu my son, ai duk lefinka ne da kaki yin aure, da kanada mata da yanzu saita yi maka tausa, sauri yayi ya canja topic din zancen da me aka dafa mana yau mum? Jallop din taliya ce, ya tsani taliya Amma Sbd karya fada ta kara cigaba da zancen yayi aure sai kawai ya basar yace bari naje gd nayi wanka, dama zuwa nayi naga lafiyarki, kuma abincin fa? A koshe nake, to dama inaso na fada maka gobe zan tafi Kaduna, Kasan next WK bikin abokinka kamal Sbd haka zanje mu fara shirye2 idan na tafi gobe sai angama bikin zan dawo, gaskiya mum kinaji da Haj Asiyan nan Ku kunata zumuncnku, mu kuwa haduwa tayi wahala saidai kusan kullum sai munyi waya dashi, kuma time to time INA zuwa nagaida dad dinsu a office, kuma duk lkcn naje Kaduna sainaje gdn kanwarsa ce dai neehal rabon da na ganta tun bata fi 8yrs ba, tab ai yanzu ta zama budurwa, yanzu haka ma likita ce kwanan ta kammala karatun ta, ah dakyau, ni zan wuce idan yaso goben sai sadiq ya kaiki a helicopter dina to shikenan son sainaji ka OK bye mum. Gida ya shiga yayi wanka ya kwanta bacci
Ina shiga gd nayi sallah na shiga kitchen dama yau dambu nake sha'awa sbd azumi nake, ina azumin litinin da alhamis. Tun safe nasa baba mero ta tanadarmin komai kafin na dawo, cikin 1hour nagama danbun, sanan na hada lafiyyayen zobo da yaji kankana, nayi potatoes bols, da paper soup din ostel dake ina sonshi sosai, kara share gdn nayi na gyara kitchen din kamar ma banyi girki ba, na kunna turaren wuta a falon sbd ya kawar da kanshin abincin, sanan na shiga wanka nasa wata orang English gown anyi shaping dinta, tayi min kyau sosai, gashina kuma anyi min twisting dake yanada tsaho ta kwanta min a gadon bayana nayi wanka da turare sanan na fito na karasa hada fruit salad
nasa a fridge
7:15pm
Nasha ruwa na gaji, kuma gashi Faisal yace zaizo kawai saina dauki phone dina nace don Allah yayi hakuri da zuwan Sbd kaina nasha ruwa na gaji gashi kaina yana min ciwo. Duk da ba haka yaso ba Amma Sbd gudun bacin raina saiyace ba matsala.
A kwance nake akan 3seater INA kallon series film din da ake Bollywood me suna Geet, baba mero kuma tana zaune a kasa tana cin dambu Sbd karar TV bamuji shigowar motarsa ba, kawai sai sallamarsa mukaji saida ya Dan jira for some seconds sanan ya shigo purple shirt da white jeans me digon purple ajiki yasa, ina kallonsa nace masha allah, allah yayi hallita anan. waje ya samu ya zauna saida na durkusa na gaisheshi, shi kuma ya gaida baba mero, kallon ta yayi da faraa yace baba mero yau kuma danbu kika yi? Aisha ce tayi wallahi, dake tayi azumi aikuwa akwai Aisha kawo masa, don naga kaima kana sonsa Sbd da kana sawa nayi maka, kallon fuskarsa nayi Sbd inaso na tabbatar da abinda take fada, sainaga yayi murmushi kawai, Amma fa ita yayiwa bani baπ. A nutse na mike nace nan zan kawo maka ko dining? Cikin wata murya ta kasaita yace kawo min nan, a nutse na dauko flaks din abincin, sanan na dauko plate da spoon na bude fridge na dauko guntun zobon dazu da kuma fruit salad duk na Jere a gabansa kum duk lkcn Dana sunkuya zan ajiye kayan saiyaji kamshin turarena ya daki hancinsa, wani irin mayyataccen kallo yake bina dashi, har baba mero ta gane ta mike ta koma dakin ta. Da murya can kasa yacemin ba zakiyi serving dina ba? Da sauri nazo na zuba mishi I tot zaice yayi yawa, Amma sainaga ya fara ci na zuba mishi zobon a cup, yanaci yana kora zoban kana kallonsa Kasan yana enjoying cin abincin, INA satar kallonsa saida ya share dambun Tass, da Kansa ya kara zobon ya shanye, fruit salad din ne yace zai tafi dashi yasha a gd nace to mikewa yayi tare da cewa kya fadawa baba mero na tafi nace to, Bari na rike maka fruit salad bowl din. Saida na rakashi har bakin mota nasa aciki nayi mishi sallama, harna juya na fara tfy saiya tuno da abinda ya kawo shi gdn, cikin unique voice dinsa yace Aysha zo nan INA zuwa yace meye hadiki da Faisal? Da rawar murya nace sona yake, kuma kema kina sonsa? Kai kawai na daga masa, are you sure? Nace yes a hankali, to kuma Elbash fa? Aishi ba soyayya muke ba, kawaidai yana jinane kamar blood sister shi, nima kuma haka nake jinsa. Is alright saida safe, kawai ya shiga motarsa ya tafi.
Maman Aysha
[10/14, 9:53 PM] Chopy: [9/25, 12:10] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣2⃣5⃣➖1⃣3⃣0⃣
Yana zuwa gd wanka yayi ya dauko fruit salad dinsa yasha, sanan ya shiga toilet yayi brush ya hau gado ya kwanta, kyakyawar fuskarta yake hangowa a yanayin daya ganta dazu ya rasa me yasa a yan kwanakin nan yake yawan tunanin ta, dandanon girki dazu ya tunu, meyasa yake jin kishinta sosai? Karfa ace na fara sonta? Wata zuciyar tace kul karma ka soma, Sbd mum dinka bazata taba amince maka ka aureta ba, da wanan tunanin bacci ya dauke shi
Washe gari
Wajen 12 pm mum din adon gari suka tafi kd da sadiq, ina zaune ina aiki Faisal yazo ya sami kujera a kusa dani ya zauna da mamaki nace lpy ka baro wajen aikin ka ka taho nan? Wallahi tunanin ki ne ya addabe ni, na kasa jurewa shiyasa nazo na ganki, wani murmushi ya sakar min yace yau tare zamuyi aikin. Haka ya zauna muna ta hira Sbd caring din da yake nunamin nima yanzu na fara sonsa sosai dagowa yayi yace Aysha nifa har yanzu ban taba ji kince kina sona ba, anya da gaske ana sona kuwa? Hawaye ne ya fara zuba a idona subahanalla me ya faru? Ko mgnr dana fada ta bata miki rai ne? Ko daya, ina sonka Faisal saida inaji ajikina aurena dakai ba me yiyuwa bane, Sbd duk ranar da parents dinka suka San ko ni wacece bazasu taba yarda ka aureni ba. Ban gane ba Aysha, yimin bayani yanda zan fahimta. Kaga yadda ka ganni to haka nake banida kowa, bansan kowa nawa ba, ba wani mutumin da zan nuna maka nace Dan uwana ne kuka sosai yaci karfina.....is OK Aysha ki dena kuka, koma ya kk INA sonki a haka zan samo miki iyayen karya a daura aurenmu, idan yaso koda su dad dina sun gane daga baya kinga kin riga kin zama matata, so duk yanda zasu yi dani bazan sakeki ba. Kallonsa nayi da jajayen idanuwa na nace kana ganin hakan zai yiyu? Yes me zai hana, kuma so nake muyi auren nanda 1 month, Allah ya zaba mana abinda yafi alkairi yace amin, bari na tafi zanzo in d night, nace to Allah ya kaimu tare muka fita nayi masa rakiya muna cikin tfy call ya shigo wayata, ina dubawa naga adon gari hlo sir, shigo ina son mgn dake, nace to Faisal bari na koma daga nan boss yana nemana, is OK saina zo. Da sauri na shiga office din kamshin turaren sa ne ya bugi hancin na sanan sanyin A/C ya biyo baya. Zaune yake akan 3 seater da sallama na shiga bayan ya amsa yayi min nuni da na zauna a kusa dashi, a darare na zauna sanan yace mum dina tayi tfy zuwa kd sai next WK zata dawo, ni kuma bana Iya cin abincin restaurant idan ba ya zama dole ba, so shine nake so daga yau ki ringa zama a gd kinayi mana girki, kafin mum ta dawo kallon kwayar idona yayi Wanda har saida tsikar jikina ta tashi inafat ban takura miki ba ko? Murmushin da nasan yana karamin kyau nayi sanan nace ba matsala to yanzu ki koma gd kawai ki Dora mana abinci Sbd harna fara jin yunwa nace to a tashi lpy.
Ponded yam nayi da egusi soup, sai paper chiken, da kuma kunun aya me kwakwa da madara zuwa 3pm na gama hada komai, sai kawai na shiga wanka na shirya cikin wani boyel sky blue Riga da siket ne, sanan nayi simple make up nayi na fito baba mero sai tsiya take min wai bata gane tsakanina da adon gari ba kodai mun daidaita kanmu ne nace aa wallahi har yanzu be ce yana sona ba, tace amma ya dauko hanya ai, a zuciyata nace Allah ya amsa bakin ki.
Saida ya koma gd yayi wanka ya canja dressing as usual kanan kaya yasa, black jeans da red shirt me tsada, sai flat cover shoe red, tun kafin ya shigo gdn muka jiyo kamshin turaren sa, da fara'arsa ya shigo saida ya Dan rusuna ya gaida baba mero, sanan nima na durkusa na gaisheshi sanan nace bismilla INA gaba yana bina a baya saida mukaje har kan dining nayi serving dinsa sanan na kawo masa ruwa a bowl ya wanke hanunsa yace ni ban Iya wanan katsantar ba, sink din dining area ya nufa ya wanke anan, sanan ya dawo ya fara cin abincin saida yaci yayi dagas sanan na kwashe kayan na dawo muka fara hira, yanzu abin nasa mamaki yake bani Sbd ya daina shareni yana sakar min fuska sosai, saidai saida har yanzu mulki da kasaita suna nan, kuma idan yana magana sai ya ringa wani basarwa phone dinshi ya dauka ya kira mum bayan sun gaisa yace masa ga neehal ma Ku gaisa ta karba Yaya kabeer ina yini yana jin voice dinta yaji gabansa ya fadi, lpy kalau neehal ya gd kuma ya shirye2 alhamdulilla ai zakazo daurin aure ko? Insha Allah, to Allah ya kawo ka lpy amin nagode. Tunda ya fara wayar na shiga tunanin wacece neehal? Me yasa mum dinshi ta matsu da saiya gaisa da ita? Shi ya katse min tunani da cewa Mrs Faisal ya akayi ne? Ko tunanin Faisal din ne? Waima na tambayeki, kin bawa Faisal lbrn ki nace eh, OK to me yace? Nan na kwashe duk abinda yace min na fada masa, wata yar iskar dariya yayi sanan yace shege Faisal, kuma kin yarda da discission din da ya yanke? Nace eh, har yanzu ke yarinya ce Aysha, kuma he is a barrister you can't understand his true color zai kara magana kenan call ya shigo wayarsa hlo OK your Excellency gani nan zuwa. Aysha bari na tafi zamu shiga meeting ne da Excellency, wani shu'umin kallo yayi min yace ina ganin daga can zan wuce gd, gobe da safe ki hadamin break fast da wuri don Allah, zanzo naci kinji beauty nima yau a Dana sunan wata sansanyar dariya nayi da har saida kumatuna ya lotsa nace Allah ya kaimu gbn.
Maman Aysha
[9/25, 22:53] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣3⃣0⃣➖1⃣3⃣5⃣
Tun ranar da mum ta tafi kd kullum adon gari a gdn yake cin abinci, dalilin haka yasa wata shakuwa ta shiga tsakanina dashi da kyar yake tafiya idan yazo.
Yau Friday, ana saukowa daga sallah direct gdn mu ya taho wata farar gezna ce ajikinsa da kudin ta zai kai 150k da bleu zare akayi masa dinkin, ya Dora wata dakyakkiyar hula me tsadar gaske anyi mata Zane da blue and white zare, abinka da farin mutun ba karamin kyau yayi ba, white rice and stew da cose low nayi mishi bayan yagama ya kalleni yayi min lallausan murmushin sa me tsada yace zan tafi Kaduna gobe daurin auran kamal ina ganin sai Sunday zan dawo akwai wani Abu da kuke bukat? Jikina a sanyaye nace ba komai Allah ya kaika lpy ya dawo dakai lpy, yace amin beauty, neehal ce ta fado min rai a zuciyata nace shikenan zaije su hadu da ita, idan kyakyawa ce ma may b ya aureta tunda mum dinsa ba sosai take son ya auri zuby ba, hawaye naji ya fara zuba a idona muna hada ido yace haba my lovely sis, ya kk kuka kuma, ko bakya so kiyi missing din brodanki? Kai na daga masa ohh sorry karki damu Faisal yana nan zan fada mishi ya kula min dake sosai kinji. A zuciyata nace Dan renin hankali ni kai nayi missing ba Faisal ba, kuma ko baka fada ba Faisal kam ai muna tare......katseni yayi da cewa ko zaki bini mu tafi tare? π³ aa Allah ya kiyaye yace amin, lekawa yayi sukayi sallama da baba mero ya bata kyautar kudin da nima bansan nawa bane sanan muka fito na rakoshi har bakin mota.
Da helicopter dinsa ya tafi, gdn su kamal ya fara zuwa dake unguwar rimi bayan ya gaisa da mum dinsa da kuma uwar ango sanan ya wuce hotel din daya kama musu shida body guards dinsa guda biyar da kuma sadi, kowa dakin sa daban sanan sanan dukkansu saida ya bawa kowa 50k. Karfe 8 suka tafi wajen dinner wacece fadar zaruwatta ma bata lkc ne, wani lafiyyayyen boyel yasa maroon da kudinsa zai kai 250k banda daukar ido ba abinda yake hammm me karatu just imaging wato zallar kyau ne ya hadu da daukar wanka, matasan kano sunyi gaskiya da suka sa masa suna adon gari domin kuwa ya yaki yam matan Kaduna wasu harda fada, amma shi besan ma sunayi ba πlol.
Washe gari bayan an daura aure wajen 4pm suka fara shirin tfy wajen mother's eve da Maman ango ta shirya, daidai nan FCT minister ya kira adon gari yace masa yayi winning contract din daya nema, Sbd haka duk yanda zaayi ya tabbatar ya isa abuja b4 8pm Sbd President zai zauna dasu 8:30, aikuwa ba shiri yayiwa ango da mum dinsa sallama ya suka wuce abj, 1 hour a abj tayi musu direct gdnsa nacan ya wuce yayi wanka ya canja kaya yayi shiga ta alfarma sanan ya wuce villa. Bai fito daga villa ba sai wajen 11pm direct gdnsa kawai ya wuce yayi wanka ya kwanta, saidai me? Tunanin aysha ya hanashi bacci kwana dayan da yayi beji daddadar muryarta, haddadan abincin ta da kuma kyakyawar fuskarta da be gani ba da kyar ya samu yayi bacci zuciyarsa fall tunanin ta
Washe gari
Tun wajen 9am ya nufi gdn Aunty Salma, lkcn daya shiga gdn shiru duk yaranta sun tafi makaranta sai yan aikin gdn da suke ta kaiwa da komowa. Wata daga cikin su yayi wa magana tace tun safe bata fito ba, yace me gidan fa tace ya fita, bed room dinta ya nufa direct ya tsaya a bakin kofar yayi knocking tana kwance tace waye? Yace ki bude mana, tana jin voice dinsa ta mike da sauri ta fito Sbd suna tsananin son junan su, what a surprise broda baka fadamin zaka zo ba a tare suka dawo falo nifa yunwa nake ji, kuma naga kamar yau ko break fast dinma bakiyi ba wallahi banida lpy ne, shima me gdn be karya ba ya fita, to ni ya zakiyi dani kenan? Bari nasa marwa ta soya maka Irish, yarinyar tana da tsafta sosai, to don Allah tayi sauri. Meyasa baka fadamin zaka zo ba? Wallahi nima un expected abin yazo min baki tayani murna ba nayi winning contract din nan ta gina estate a maitama, gidajen ministers ne, shine President ya nemi ni mu tattauna yanda abin zai kasance, to Allah ya taimaka yace amin. To ni yanzu wa zaka samomin ta tayani girki kafin na samu sauki, Kasan na shagwaba megida na baya Iya cin abincin restaurant. Inada wacce zansa tazo, idan tayi miki girki mijin naki ma bazai gane bake kikayi ba Sbd itama expert ce, zanyi waya Sulaiman ya sakota a jirgi gb, Amma fa Iya sati daya kawai zan ara miki ita, idan zan tafi tare zamu wuce. Ba matsala ai hakan maka taimaka min Allah ya kaimu goben yace amin
Maman Aysha
[9/26, 22:20] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣3⃣5⃣➖1⃣4⃣0⃣
To Amma yar gidan waye yarinyar da zaka kawomin? Iam her father, mother, broda every thing. Ban gane ba? Nan take ya kwashe lbrna from AtoZ ya fadamata, kai Amma na tausayawa mata, har naji ina sonta tun kafin na Santa. Tunda hakane ka fadamata ta taho yau mana, idan naki fa? Pliss my broda taimaka min, kaga abbansu nana ya samu yayi break gobe kafin ya fita, aike kullum damuwarki kenan abbansu Nana, shikenan bari na kirata
Muna zaune a falo nida baba mero muna break fast, Sbd muma yau bamu tashi da wuri ba, kiransa ya shigo wayata, da sauri na dauka Sbd nayi missing unique voice dinsa yau 2 days bamuyi waya ba, bayan mun gaisa yace na bawa baba mero, suna gaisawa ha hadata aunty Salma suka gaisa dake sun saba sosai don tasha yi mata zaman biki ma idan ta haihu. Saida suka gaisa sosai har suka taba hira sanan yace ta bani wayar, INA karba yace don Allah alfarma nakeso kimin aysha, sister Salma ce bata da lpy shine nakeso kizo ki Dan taimaka mata da girki for 1 wk, idan zan taho saimu taho tare kinji, nace to yaushe kenan zan taho? Yau, nasa Sulaiman yayi miki booking din jirgi, idan kin shirya zaizo ya kaiki airport, ki fadawa baba mero ta tafi gd idan kin dawo saimu dakkota Sulaiman zai baki kudi ki bata nace to, Allah ya kawo ki lpy nace amin.
Jirgin 7pm na shga, Sbd haka 8:15 a Abj tayimin, INA sauka na tarar da driver aunty Salma yazo dauka ta muka tafi. Black Arabian gown ce ajikina, na yane kaina da mayafin rigar. Fadar kyau da haduwar gdn aunty Salma bata lkc ne me karatu kayi imagining kawai. Jiki ba kwari nayi sallama na shiga gdn, akan dining na same su suna cin abinci muna hada ido da aunty Salma kawai saita kware ta fara tari saida ya dauko mata ruwa sanan ya tsirga, wani irin kallo ta Bini dashi da har INA gaisheta amma batasan INA yi ba har saida adon gari yace sis gaisheki fa take, sanan ta dawo hayyacinta ah lpy kalau ya hanya nace alhamdulilla, marwa zo ki rakata daki, INA barin wajen ta kalli adon gari tace da ace ba uwa daya uba daya nake dakai ba da sai nace kawo yarinyar nan gdn nan set up ne,taya zaayi ka kawomin wanan kyakyawar yarinyar kamar ba mutun ba? Wata yar iskar dariya yayi sanan yace wallahi ki rage kishi, Dan nasan duk akan mijinki kike wanan abin, to tanada mijin da zata aura, kuma ita kudi ko kyau baya gabanta ballatana tayi tunanin aurar mijinki, kuma in banda abinki sister ai kema kyakkyawa ce. Ki kwantar da hankalin ki da Allah ki zauna da ita a bisa amana insha Allah ba abinda zai faru kinji my sis, tace to shikenan.
wacece aka kira da marwa ita ta rakani wani daki INA ajiye kayana na fada toilet nayi wanka, sanan nayi sallah, har dakin aka kawo min abinci, Amma saina kasa cin komai tunanin yanda zanyi zaman gdn...sallamarsa ce ta katseni, kamshin sa ya bugi hanci na kan gadon yazo ya zauna yace min ya hanya? Banyi magana ba sai dagowa nayi muka hada ido sanan muka sakarwa juna wani lallausan murmushi a hankali ya furta I miss you my lovely sis, can kasa nace I miss you too, yace da gaske? Faisal bezo ya tayaki hira bane? Basarwa nayi kamar banji abinda yace ba, abincin da aka kawomin ya kalla yace me yasa baki ci ba? Nace na koshi, ohh sorry ashefa bakya Iya cin abinci da daddare ko? Bari na dauko miki ice cream, yana kawomin yayi min sallama ya tafi
Maman Aysha
[9/27, 10:45] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣4⃣0⃣➖1⃣4⃣5⃣
Yana fita da few minutes aunty Salma ta shigo tace aysha bakiyi bacci ba nace eh, don Allah fa kiyi hakuri idan mun takura miki, wallahi mijina ne ba kowanne abinci yake Iya ciba, ni kuma kwana nan ba kowanne abinci nake son jin kamshinsa ba, karki damu aunty Salma ba wani Abu wallahi, to ngd sosai, naji lbrnki a wajen broda I pity you Allah ya bayyana miki iyayanki nace amin. Tun kafin kizo da naji lbrnki naji INA sonki, so don Allah ki saki jikinki ki dauke a matsayin elder sis dinki kinji? Murmushi nayi nace to nagode, to me zaki dafa mana da safe? Duk abinda kk ce, OK akwai komai da zaki bukata a kitchen din, na baki choice kiyi mana duk abinda ya samu, murmushi nayi da har saida kumatuna ya lotsa nace to. Bari na barki ki kwanta saida safe nace Allah ya kaimu. Tabbas aunty Salma tafi adon gari kirki da saukin kai, kyakyawar mata ce Sbd suna tsanin kama da Broz sosai, yau daya na fara ganinta amma sainaji ta shiga raina. Addua nayi na kwanta Sbd tashib wuri zanyi
Ina idar da sallar asuba na shiga kitchen, paper soup din kaji na farayi, sanan na soya doya da kwai da plaintain na dama kunun gyada na kwaba fulawa nayi shawrma, sanan na tafasa ruwa a kettle na zuba a flaks ko wani zaisha tea zuwa 7am na kammala komai, INA fitowa daga kitchen naga yaranta nabil da khairat sun fito cikin shirin su na makrant, marwa ce take kula dasu. Da gudu suka zo suka rungumeni nabil yace ya sunanki? Nace aunty Aysha yace zaki zauna a gdnmu? Nace eh, yace INA sonki aunty Aysha, dariya nayi nace nima INA sonku nabil da khaitat murna suka hau yi, sanan na kama hannun su mukaje na zuba musu abinci sukaci, sanan na wanke musu hannu mu kaje na zuba musu shawarma a lunch box dinsu banda surutu ba abinda sukemin, gabadaya sai tunanin su basma da junior ya dawomin sabo bansan lkcn da hawaye ya cikamin ido ba, daidai nan mum dinsu ta fito da gudu sukaje sukayi hugging nata gud morning mum tace morning my kids, kunci abincin? Eh Aunty Aysha ta bamu, kuma yau da Aunty Aysha tayi mana shawarma da ita zamu tafi sch. Dariya tayi tace dats very gud, Aysha dama kin Iya shawarma nima dariya nayi nace eh, dakyau ko catering kk karanta ne? Aa, OK to kuje Ku tafi karku makara kharat ce tace ni awajen aunty Aysha zan zauna, nace yi hakuri kije khairat idan kin dawo zan kaiki wonder land ki hau mota, nabil yace nima zaki kaini? Nace eh da gudu suka fita suna murna INA dagowa muka hada ido da Maman su ta sakar min murmushin jin dadi tace sannu da kokari aysha. Daki na koma na gyara, itama na shiga na gyara mata room dinta da toilet ita kuma ta gyara part din megidanta sanan nayi wanka nasa wata fitted gown ta wani material green, dinkin yayi min kyau sosai, simple make up nayi na murza dauri me kyau, sanan nasa sarka da Dan kunne nayi wanka da turare na dauko laptop dina na fara kallon wani film da nayi down loading wa men hubbi maqatal. Sai wajen 8 me gidan ya fito ya zauna a dinning ya kwashi abinci, da zai fita aunty Salma tazo tace naje mu gaisa dama ta bashi lbrina tun dare, har kasa na durkusa na gaisheshi shi ya amsa da fara'arsa kuma yayimin godiya. Yana fita tace nazo muyi break, kunun gyada da plantain kawai na Iya ce, aunty Salma tace Aysha akwai abinda yake damunki, ko vakyason zama damu ne? Sbd dazu dana fito naga hawaye a idonki, nace wallahi ina son zama daku akwai kannena wanda ada nayi zaton uwarmu daya ubanmu daya, junior da basma kusan age mate din su nabil ne mu shaku sosai da yaran ni nake musu komai, duk lkcn dana tunasu sainayi kuka nakejin dadi. Eyya allah sarki kici gaba da hakuri insha Allah wata rana sai lbri, nace hakane kam. To me yasa kuma bakya son cin abinci? Nace ba kin ci nake ba, is my nature, dariya tayi tace aiko gashi nan bakya kiba,nima dariyar nayi daidai nan handsome ya shigo, yau kuma danyen boyel ne ajikinsa cream color gashin nan ya kwanta yayi luf muna hada idon na nemi nutsuwa ta na rasa sabd balain kyaun da yayi, karasowa yayi yace gud morning sis tace morning broz, nace masa INA kwana saida ya Dan lumshe ido ya bude sanan yayi murmushin da yake tafiya da imanin yan mata yace lpy kalau ya kwanan bakunta? Nima murmushin na mayar masa har saida kumatuna ya lotsa nace lpy kalau, duk abinda muke aunty Salma na kula damu, Amma saita yi kamar bamu take kallo ba. Ni nayi serving dinsa ya fara cin abincin saidai duk dagowar da mukayi sai mun hada ido, wani irin kallo yake min Wanda yasa wani mugun sonsa yake yawo acikin jinin jikina, har naji bazan Iya jurewa ba, mikewa nayi na koma daki na kwanta na fara tunani saura 2 month ayi bikinsa wasu zafafan hawaye suka fara zuba a idona, ina sonka kabeer, don Allah ka furta kace kana sona, at least ko baka aureni ba zanji sanyi a raina kuka nake sosai banji shigowarsa ba sai kamshin turaren sa daya daki hancina ya salm Aysha meya faru kuma? Don Allah ki fadamin Aysha, ko zaman gdn nan ne bakya so? Nace aa to fadamin don Allah meye matsalar ya karasa maganar cikin tsananin damuwa. A zuciyata nace ciwon sonka ne matsalata, Amma a fili sai nace ba komai iyayena na tuna bansani ba ko sunada rai ko sun mutu, daugoni yayi ya rungumeni a ajikinsa kiyi hakuri beauty kinji, asan is painful Amma addua zakici gaba dayi indai suna raye Allah yayi gaggawar bayyana su nace amin, hankii ya dauko a aljihunsa ya gogemin hawaye sanan ya kuramin ido da sexy eyes dinsa yayi magana da wata irin voice din da ban taba sanin yanada ita ba yace kayimin alkawari bazaki kara kuka ba, dakyar na Iya cewa na daina, sanan yace zanje mu karasa meeting da muke da Mr President ina ganin sai dare zan dawo idan da wani matsalar kiyimin text kinji? Nace to, kuma don Allah ki ware kuci gaba da hirarku da aunty Salma, kada kai kawai nayi. Harya fara tyfy ya jiyo yace ko Dan smiling bazaki yimin ba? Wani lallausan murmushi nayi masa da har saida kumatuna ya lotsa, sanan yace thank you my sis ya fice ya barni da kewarsa da kuma kamshin turarensa
Maman Aysha
[9/27, 14:55] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣4⃣5⃣➖1⃣5⃣0⃣
Shakuwa ce me tsanani ta shiga tsakanina da aunty Salma, wadda har jinta nake kamar blood sister na, na sake da ita sosai har tsokanar juna muke, shima mijinta dake Dan harka ne harshi ake zama ayita hira.
Yauma kamar kullum bayan mun kammala dinner muna zaune anata hira har megdn khairat tayi bacci akan cinyata, nabl kuma INA koya masa h/work saiga adon gari ya shigo, bayan an gaisa yace kwantar da yarinyar nan ki zobomin abinci yunwa nakeji nace to, daki na kaita Sbd tunda nazo gdn tare muke kwana da ita, cusccus akayi wit vegetable soup Dana zuba yace kawomin nan, cin abinci akan carpet yafi dadi nace to yanaci anata hira, nabil yazo ya dameshi sai tsalle yake ajikinsa duk ya hanashi cin abincin ma, yace kai tashi kaje ka kwanta kona Zane ka, banda kiriniya ba abinda ka iya. Dariya aunty Salma tayi tace ai kai ya gado, Sbd ka bani wahala kana yaro, nan ta shiga bamu lbri tace bana mantawa lkcn da muka zauna a London a makotanmu akwai wani yaro, sunanshi selvesta duk ya girmemu, gashi Dan lukuti idan ya kama mutun baya yi masa da wasa Sbd karfinshi super master ake ce masa ga brodana da tsokana kuma idan yayi tsokanar aka dakeshi sai mum tace dole saina fita na rama masa, duk lkcn daka tsokano shi gbn har faduwa yake,Dariya mukasa gabadaya, mijinta yace kai Ashe matsoraciya ce ke, tace wallahi Dan bakaga yaron bane. Adon gari ne yace au ni na manta ma Ashe wayoyina a kashe suke bari na kunna, aikuwa kamar jira suke yana kunnawa calls ya fara shigowa, kuma duk rabi yan matane wasu ya amsa, wasu yayi rejecting kuma don jaraba yana gama amsa wani kiran, wani yake shigowa. Mijin Aunty Salma ne yayi dariya yace ka zama business cenre duk suka kwashe da dariya banda ni da kishi ya cikamin zuciya, wani kiran ne ya kara shigowa da hanzari na dago na kalle shi sainaga yayi wani smiling ya furta zuby can Kasan makogaransa cikin wata sansanyar unique voice dinsa yake mata magana kanajin hirar tasu ta soyayya ce nan take naji kirjina ya cushe, kaina ya fara sarawa tsananin sonsa ya fara yawo acikin jinina, kawai sainaji bazan iya cigaba da zama a wajen ba mikewa nayi nace musu saida safe aunty Salma da tun lkcn da yanayina ya canja tana kula dani tace tun yanzu zaki kwanta? nace eh bacci nake ji to shikenan Allah ya tashemu lpy nace amin
Gani yayi hirar tata bazata kare ba, yace kinga zuby I will call you back later, Ina wani important Abu ne, be jira abinda zatace ba kawai yayi switching off. Dariya babansu khairat yayi yace wato hirar da kuke is not an important issue ko? Anya karbuwar data samu guarantee ce kuwa? Murmushi kawai yayi, aunty Salma tace ai wanan brodan nawa sai a hankali, Amma inaji ajikina akwai yarinyar da zata karya alkadarinka kwanan, kuma you can't denied it. Wata shegiyar dariya yayi yace haba sis kin manta halina, ADON GARI ne fa, aini bana bari son wata ya shiga zuciyata ballatana har ya dameni, nidai zasu soni kuma har zuciyarsu ta nemi bugawa akaina, Amma ni ba wata wadda yarinya data isa na shiga wani hali akanta. Haka kace ko broz? Eh, to shikenan we shall see, mikewa yayi nizan tafi saida safe. Suka amsa da To Allah ya kaimu yace amin
Ni kuwa tunda na shiga daki nake kuka, wani irin son shine yake addabata wanan wane irin rayuwane? Na kamu da son mutumin da besan inayi ba tabbas ko shakka banyi, ciwon son adon gari shi zai zama ajalina, ita kam zuby Allah ya taimaketa tazo duniya a SAA, Sbd ko be aureta ba, zata iya bada tarihin yayi soyayya da ita, ya Allah ka ciremin son mutumin nan a zuciyata don na fuskanci mayaudari ne, yayi amfani da bewar da Allah yayi mishi ya koyamin sonshi, kuma yayi ignoring dina koda wasa yaki ya nuna yana sona, why me kabeer? Me yasa baka tausayi na, me yasa baka barni da bakin cikin rashin iyayena ba, kake kokarin kara jefa rayuwata acikin matsala, wata zuciyar ce tacemin karki zargi kabeer Aysha ki zargi kanki, Sbd shi besan ma kina sonshi ba, kinyi mistake da kika bari sonshi ya shigeki sabda ba yanda zaayi mutun me kudi, kyakkyawa Dan asali me tulin yan mata buhu buhu ya amince ya aureki, dole yar asali zai aura. Saida nayi kuka me isata, daga baya kuma wani wahalallen bacci ya daukeni.
Maman Aysha
[10/14, 9:53 PM] Chopy: [9/28, 11:59] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣5⃣0⃣➖1⃣5⃣5⃣
Gobe ne ranar da kabeer yace zamu koma kano muna zaune muna hira da aunty Salma wajen 5pm, kawai saiga kabir ya shigo, da gudu yara sukayi hugging dinsa dake yana nuna musu so sosai, waje ya samu ya zauna yace kuje a shiryaku mu tafi yawo aunty Salma tace bazakaci abincin ba? Eh yau bana sha'awa, zan sami abinda zanci a rose flower sweet and bakery, nayi karaf nace ka bude a garin nan ne? Aunty Salma tace ai baki Sani ba? Aikuwa ya kamata kije, sabda idan kika shiga na garin nan saiki raina na kano, iya kudin shiga kawai 5000 ne, Ki shirya kuje mana, idan kin dawo zaki bani lbr nace to bari na canja dressing.
Wani hadadden filtex lace nasaka, zanen lemon green da orange color ne ajiki, amma orange din bashi da yawa, rose silk na daura orange nasa sarka da Dan kunne na stones suma orange color, 20k na sayesu, mayafi da shoe&bag ma orange zama nayi nai make up sosai a fuskata sanan na fita, takalmin danasa me tsini ne kos kos din takuna ne ya janyo hankalin su zuwa wajena nan take adon gari yayi mutuwar tsaye, bina yayi da wani irin mayattacen kallo da har naji kafata tana hardewa, da kyar na karasa wajen cikin sanyin murya nace na gama yace OK muje, sis sai mun dawo tace to. Shima saida ya biya kudi muka shiga, haka dokar wajen take, gaskiya kabeer ba karamin me kudi bane, domin kuwa rose flower sweet and bakery dinsa na abuja kadai ya isa ya rikeshi, wato fadar girman wajen ma bata lkc ne, ba abinda babu a wajen, akwai swimming pool, wajen wasan yara ya zuba haddadun motoci irin na wonder land, sai wajen lilo na yara daban, na manya ma daban, akwai wajen game din table tennis, basketball, suluka, volleyball dadai sauran su, akwai lafiyayyen garden da aka kawatashi da hadaddadun shuke shuke irin Wanda ko ranka ne a bace idan kaje wajen saika nemeshi ka rasa, sanan akwai restaurant duk wani kalar abinci ko snacks da abinsha akwai shi awajen, in fact idan kana cikin wajen saika manta a 9ja kake.
Tunda muka shiga wajen muke cin karo da hadaddun yan mata da samari, kai har matan aure baa barsu ba duk Wanda ya kallemu saiyaji mun burgeshi Sbd kyau da kuma dacewar da mukayi, direct wajen wasan yara muka je aka sasu mota suna ta murna mota tana zagayawa dasu, wasu kujeru muka samu muka zauna, kawai saiga wasu yan mata guda biyu sunsha kyau sukayi mana sallama, sanan daya daga cikinsu ta dubi adon gari tace don Allah ka temakeni ka bani koda 1 minut ne na ganka, basarwa yayi kamar beji me tace ba, Mr kabeer don Allah ka taimaka min, cikin fushi yace wai bakiga tare nake da wife dina bane, ban yarda ba, ba matarka bace ai daurin auren babban mutun Wanda yayi suna har a kasar waje irinka bazai boyu ba, da yanzu duniya ta Sani Kai musulmi ne kuma da Allah na hadaka, don Allah ka taimaka ka saurareni. Mikewa yayi suka koma gefe sanan ta fara masa bayani ni sunana juwaira Yusuf, dad dina ne minister of education, ranar da akayi bikin bude wajen nan na fara ganinka, kuma tun ranar na kamu da sonka saidai na rasa yanda zan hadu dakai sai yau. Kneel down tayi don Allah Mr kabeer ka taimaka ka aureni koda ata biyu ne Sbd wallahi INA tsananin sonka, naji Amma ki tashi, Sbd gbdaya idon mutane akanki yake ban damu ba kallona da mutane suke ba shine matsalata ba, ka amince da soyayya ta shine matsala ta, to naji tashi muyi magana, mikewa tayi ta zuba masa ido, kiyi hakuri don Allah idan nace zan aureki nayi miki karya, ban taba sha'awar mata biyu ba kuma insha Allah har abda bazanyi ba, kuma na Riga nayi dating matar da zan aura so INA yimiki fatan alkairi Allah ya baki Wanda ya fini, Tahowa yayi ya barta a wajen tana kuka yana zuwa yacemin taso mu tafi garden nace yaran fa? Daya daga cikin staff dinsa na wajen ya kira yace ya kula dasu khairat idan sun gaji ya rakosu guarding yace to
Wajen sabd shakatwarsa kadai ya tanade shi, sai yazo ake budewa ya gyara wajen sosai muna zuwa ya kwanta akan grass carpet ya lumshe ido, ya Dade a haka sanan ya ya bude a hankali ya kira sunana cikin damuwa yace Aysha me yasa yan mata suke bina? me yasa suke cewa suna sona? Akwai kyawawan samari masu kudi, masu class, wasu dunfini kudi ma Amma me yasa yan mata basa binsu Sani? Why me? Banaso nayi hurting din mutun, amma yan matan da suke sona sunsa dole inayi, what am I going to do? Aysha fadamin meye solution? Me zanyi su dena bina ba tare da na wulakantasu ba? Wallahi dani mace ne, da nikaf zan ringa sawa, cikin wata cool voice yayi magana Aysha fadamin me yakamata nayi? Nace kayi aure, idan sukaga kayi aure zasu Dan rege binka. To wa zan aura? Zuciyata har yanzu batasan zuby, na kasa son zuby Aysha, akwai mutumin daya da zuciyata takeso, saidai abune me wahala aurena da ita ya yuyu. Me yasa? Is a secret, tashi yayi ya zauna ya rike hannuna sanan ya kafeni da wani irin kallon daya saukar min da kasala yace ki tayani da addua Allah ya warware min matsala ta acikin ruwan sanyi, will you? Kai na daga masa Sbd gabadaya jikina ya mutu. Wani lallausan smiling yayi yace mrs Faisal, kuna waya kuwa? Nace eh ai na fada masa ma gobe zamu tafi, kai sorry wallahi na manta na fada miki an fasa tafyar gobe, Sbd me? Kinsan dad dinsu khairat yayi tfy ko? Eh, shine tace na taimaka na bar mata ke zuwa next WK saiki tafi, kai gobe zaka tafi kenan? Nan take naji gabana ya fadi, duk da nasaba da aunty Salma, Sbd shi nake jin dadin zaman garin, Ciwon sonsa zai wahalar dani kenan,,,,,,,,Tunanin Faisal kike ko? Kiyi hakuri ai kuna waya, sati dayan kamar yaune a wajen Allah, muje mu tafi naga magarba ta kawo kai
Maman Aysha
[9/29, 17:37] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣5⃣5⃣➖1⃣6⃣0⃣
Ana kiran sallar magrib muka shiga gd KB yayi alwala ya tafi masallaci nima daki na shiga nayi alwala bayan mun idar da sallah muka fito falo aka debo take away din da mukayi a rose flower sweet and bakery muka baje gabadayanmu mukaci, sanan aka fara hira, sai wajen 10pm Mr kabeer ya mike yayi mana sallama har yakai bakin kofa ya juyo yace lovely sis ba rakiya? Murmushi nayi nace muje na rakaka har bakin mota na rakashi saida yace bude motar ya shiga sanan yace ina fata sati dayan da aunty Salma ta kara miki be bata miki rai ba? Wata yar sansanyar dariya nayi ace ba damuwa 1 WK din kamar yau ne ai. To ya zakiyi da Faisal? Zaki iya coping da rashin ganin sa harna 2 wks? A zuciyata nace wanan mutumin Dan renin hankali ne, kodai ya gane na kamu da sonshi, shiyasa yake min haka? Amma a fili sai nace face dinsa kawai nayi missing, Amma ruhin mu yanan manne da juna, da har nake jin kamar muna tare. Yanayin sa ne ya canja, cikin shan mur yace min gud nyt.
Yanayin yanda ya shiga damuwar nima sainaji banji dadi ba, jiki ba kwari na shiga gdn aunty Salma tace ya tafi nace eh, to zauna muyi wata magna dake nace to da gaske ne kin dauke ni a matsayin blood sister ki? Nace eh, zanyi miki tambaya Amma don Allah Aysha karki boye min komai ki fadamin gaskyr abinda yake cikin zuciyrki nace to, a zaman da nayi daku na sati daya nan, na fahimci akwai soyayya me zafi tsakanin ki da broda saidai kunki Ku gaskanta hakan a junanku, Sbd haka inaso ki fadamin kina sonsa? Kuka na fara eh ina sonsa Amma kuma nasan yafi karfina, nayi kokarin hana zuciyata ta kamu da sonshi, but I fell, ina tsananin sonshi Amma ba yanda zaayi kabeer ya auri marar asali Irina,,,,,sauri tayi ta rufemin baki karki damu shima yana sonki, naga zallar sonki a kwayar idonsa, nafi kowa sanin halinsa Aysha, kuma inaso ki Sani a sanina bayan ni, kece mace ta farko da kabeer yake zama yayi hira da ita cikin sakin fuska, kice mace ta farko da kabeer ya fita outing da ita, sanan kece mace ta farko da Ya nunawa caring, wanan shi ya tabbatar min da cewa he is in Luv wit you, kuma kema kinyi deserving a so ki, kinada wasu qualities da sai an Tara mata dubu baa sami guda goma irinki ba, matsalar ki guda daya rashin sanin iyayenki, wanan kuma bazai hada aure ba indai yana sonki, mun barwa Allah, yafi mu sanin dalilin da yasa yayi haka. Idan ba zaki damu ba inaso ki ringa amsa wayar Faisal a gabn broda kinji? Nace to, zaki iya tafiya saida safe nace Allah ya kaimu
Washe gari
Sai wajen 9am na tashi na shirya break fast, yau kunun gyda da kosai nayi Sbd aunty Salma tanaso sanan na soya Irish da plantain na dafa ruwan tea komawa daki nayi nai wanka, nasa wata English gown peech color nayi fakin din gashina ya kwanta luf a gadon bayana, idan ka ganni saika ce swara ce, Sbd muna kama sosai, saidai ni dimple dina ya fito sosai.
Sai wajen 9:30 ya shigo gdn a dinning ya samemu muna cin abinci, shima yazo yayi joining dinmu ba karamin murna yayi ba daya samu kunu da kosai Sbd yanaso sosai kallona yayi yace kinji dadin ki Aysha, gaskiya Faisal ya more bakida kiwa irin ta yan matan zamanin nan Aunty Salma tayi dariya tace gaji da shi, wanan santi kawai kake wa mutane, sai yau Kasan bata da kiwa daka kwashi koko da kosai? Phone dina ce ta fara kuka, INA dauka cikin sansanyar murya nace hlo swit heart gud morning, morning my dear I hope kin fara shirin tahowa dai ko? Wallahi an fasa tafiyar sai next WK, what? Ke bakya tausayina ne? Baki damu ma da halin da nake ciki ba ko? Aysha ko kin daina sona ne? Kinsan da yadda nayi 1 WK din nan kuwa? Wallahi ina sonka swit heart, I miss you beyond your expectations, ba yanda zanyi ne shiyasa don Allah ka kara hakuri, iam begging pliss! Naji Amma gobe zan taho abj idan yaso ma taho tare, Kayi hakuri don Allah, me gidan yayi tfy, may b bazai kai 1 WK din ba ma, kuma yana dawowa zan taho, bakya so nazo? Inaso mana, banaso kabar wajen aikinka ne to shikenan zan duba na gani, alright, bye take care I miss you, I miss you too.
Cikin nishadi adon gari yake cin kosan, Amma ina fara waya da Faisal yaji ya fita a ransa Amma haka yaci gaba da cusawa, wani irin kishi ne ya addabi zuciyarsa da kyar ya samu yayi controlling Kansa, Amma dayake he is very smart duk kallon da aunty Salma ta kafeshi dashi bata gano wani abu a fuskarsa ba. Muna gama wayar aunty Salma tace Faisal ne ko? Nace eh, ko cewa yayi zai biyoki? Nace eh, to ai da kin kyaleshi yazo, yanada gaskiya fa Aysha, Allah ya taimake shi ya sami finan discission irin ki ai bazai yi da wasa ba, ai komai yayi akan ki be fadi ba bcos you deserve it, wani irin shu'umin murmushi yayi yace sister iam going, nan take naji gabana ya yanke ya fadi, na rasa abinda yake min dadi aunty Salma ce tace tun yanzu? I have a lot to do ko kinsan Mutanen da Suleiman PA ya bawa appointment din ganina sunfi mutun Dari, kuma nayi missing mum sosai I need to see her. Shikenan Allah ya kaika lpy yace amin, kafeni yayi da sexy eyes dinsa yace Mrs Faisal me zance masa idan naje? Tell him dat I really miss him, OK I will, na tafi sai munyi waya nace to Allah ya kiyaye
Maman Aysha
[10/14, 9:53 PM] Chopy: [10/1, 10:44] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣6⃣0⃣➖1⃣6⃣5⃣
Yana sauka a Kano ya tarar da jerin motocinsa sun zo daukar sa, direct gdn mum dinsa ya wuce a Nasarawa GRA yana shiga yaje yayi hugging dinta yace I miss you mum, I miss you too my son, ya sister ka da yaran? Lpy kalau tace na gaisheki ina amsawa, iam feeling Hungary me kk dafa min? Favorite dinka nayi kuma da kaina nayi maka, oh thank you mum may god bless you wit Aljannar firdaus murmushin jin dadi tayi tace amin son. Dakin sa na gdn ya shiga yayi wanka Yasa wata yellow shirt da black jeans Sanan ya zauna yaci abincin, saidai wani Abu daya tsaya masa a rai shine test din girkin Aysha kawai yake son ci, wani irin missing dinta yake, kadan yaci abincin yaji ya fita akansa jinsa yake kamar wani marar lpy, kallon da mum take binsa dashi ne yasa ya waske ya fara wata irin faraa Wato mum har yanzu kina nan da girkinki me dadi, abincin yayi dadi sosai wallahi murmushi tayi irin na manya sanan tace ai kuma bakaci da yawa ba, ah naci da yawa mana kinga fa kadan na rage, to idan ka gama inaso muyi magana dakai, gabanshi ne ya fadi Amma saiya daure yace na gama, dama so nake na tambaye ka lkcn da kaje Kaduna ka gaisa da neehal kuwa? Aa ai bamu hadu ba ma, me yasa? Ai na fada maka duk yanda zakayi ka nemeta Ku gaisa, Wallahi nima naso hakan tafiyar data tasomin zuwa abj ne tasa bamu hadu ba, Amma ita ta ganka ai, Kaine baka ganta ba. Inaso ka Sani har yanzu hanklina be kwanta da zubaida ba, dandai kace ita kk so ne, Amma idan har zakabi umarni na nafiso ka auri neehal Sbd kyakyawar yarinya ce da saika hada yan mata dari baka samu guda daya kamarta ba, kuma gata yar manyan mutane, na Dade inaso naga mun hada jini da familyn Alhaji Abdullahi Idris makarfi, don Allah son kayi hakuri ka cikamin burina. Duk da sanyin A/c dayake dakin saida gumi ya jike shi jagab, zuciyarshi yaji tana bugawa duk duniya ba wacce yakeso yaga farin cikin ta irin mum, yana tsananin gudun bacin ranta ya zama dole kenan ya auri neehal, kallon mum yayi yace to amma mun kun binciketa sosai? Kinsan fa bazata rasa Wanda yake sonta ba, na tabatta zatayi kotanason wani bazata ki auran ka ba, Sbd ba matar da zata Dora ido akan ka bataji ta kamu da sonka ba iam proud of you my son murmushin yake yayi yace Allah ya zabar mana abinda yafi alkairi, Amma don Allah mum karki ma iyayenta zancen tukun, ba komai ne yake burge wasu matan ba, ki bari mu dedeta kanmu tukun, shikenan my son Allah yayi maka albarka yace amin, a gdn ta yau yayi niyar kwana Amma sai ya fasa yayi mata sallama ya tafi gd.
Yana zuwa gd wanka yayi ya kwanta akan gado, Amma Sam bacci yaki zuwa, fuskar Aysha kawai yake gani a idonsa, tabbas yana son Aysha so me tsanani, bazai iya tuna lkcn daya fara sonta ba, shidai kawai abinda ya Sani shine sonta ya Riga ya gama yi masa illa a kowanne bangare na jikinsa, be taba sanin ya so yake ba sai akanta, kuma bazai taba iya rayuwa ba tare da ita ba Aysha ce rsyuwarsa itace farin cikin sa, itace komai nashi yanzu ya zaiyi da mum? Ta Yaya zai fuskanci mum yace bayason neehal Aysha yake so? Ta Yaya zai tunkari mum ya fada mata yarinyar da yake so baa San asalinta ba? Tabbas idan taji lbrn ta bazata taba amince maka aurenta ba wata zuciyar ta bashi amsa, ba abinda yake son gani yanzu kamar aysha, yayi missing cuty face dinta, smiling dinta, wani irin kuka ne me karfi ya kwace masa haka ya zauna saida yayi me isarsa, muryarta kawai yake son ji, kawai sai ya dauki phone dinsa ya fara dialing......
Tunda ya tafi naji gabadaya garin yayi min zafi nayi kokarin na boye damuwa ta Amma na kasa har aunty Salma ta gane halin da nake ciki, yau ko hirar da muka saba munayi na kasa da wuri na koma daki na kwanta tunanin sa ya addabi zuciyata, wasu zafafan hawaye ne suka fara zarya a fuskata, daidai nan phone dina ta fara kara ina dauka yace me kike baiiyi bacci ba Aysha? A zuciyata nace Dan renin sense, shi meya hanashi baccin? Kamar yasan tunanin da nake sainaji yace harna fara bacci saina tuna na taho na barki a wani gari da baki saba sosai ba, sai nake ji kamar na takura miki, kuma nayi wa Allah alkawari zan rike ki bisa amana, zan kula da farin cikin ki har zuwa ranar da zan aurar dake, wanan dalilin ne yasa nace bari na tabbatar da kina cikin farin ciki kafin na kwanta, kuma da alama you're not in d mood, nasan tunanin Faisal ne matsalar ki, so zanzo na tafi dake gobe Sbd bana so na karya alkawarin Dana daukar wa Allah akan zan baki farin ciki, be jira abinda zance ba ya kashe wayar. Wato badan yayi missing dina ya kirani ba? Meyasa baya sona? Meyasa har yanzu ya kasa ganewa iam in Luv wit him? Farin ciki ka Dade da rabani dashi Kabeer, tun ranar dana kamu da sonka na rasa farin cikina kuka ne me karfi yaci karfina dakyar na samu nayi bacci
Maman Aysha
[10/2, 12:53] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣6⃣5⃣➖1⃣7⃣0⃣
Washe gari
Yau ya kama Saturday bamu tashi da wuri ba sai 9am da sauri na shiga kitchen na hada break fast muna gama ci naje na gyara dakina Dana aunty Salma, sanan nayiwa su khairat wanka nima wankan na shiga ina fitowa na shirya cikin wasu English wear's rigar pink ce tanada Dan tsayi, amma bata karasa gwiwa ba sai blue jeans kayan sun kamani sunyi min kyau sosai, kara taje kaina nayi na daure da band ya kwanta a gadon bayana, make up nayi sosai Sbd yau har janbaki nasa me karatu Baku ganni ba nayi kyau kamar a sace ni, idan ba magana nayi ba sai Ku rantse daga kasar India nakeπlol
Ina fitowa naga nabil da khairat sunata kokawa akan ball, rarrashinsu nayi nace suzo muje garden din gdn muyi ball, aikuwa suka biyoni da gudunsu iskace me dadi take kadawa dake lkcn damina ne, da gudu muka shiga garden din muka fara ball da muka gaji da ball din sai muka Fara wasan gudu duk Wanda ya kamani saina cillashi sama na cafe, saina kara zubawa a guje yaran iya karfinsu suke bina Amma sun kasa kamani Sbd gudu nake sosai.
Shigowarsa gdn kenan har yaje bakin kofar falo saiya jiyo hayaniyarsu a garden, kawai saiya nufi wajen rungume hannunsa kawai yayi ya zuba musu ido yana kallonsu fuskarsa dauke da wani smiling da shi kade ne yasan maanarshi zuciyarsa ce ta fara bugawa, ba abinda yakeso irin yajita ajikinsa, a hankali lebensa ya furta I Luv you Aysha.
Kafafuwa na naji sun gaji da gudun, na juya baya naga still suna bina sai kawai na fara Neman inda zan boye musu, ta bayan wasu dogayen Flowers na shiga, ina juyowa naci karo da wata bishiyar fulawa na tafi luuu zan fadi Sbd dama na gaji, lumshe idona nayi INA zuba ido na ganni a kasa, kawai sainaji ni a jikin Abu me taushi kamar auduga, kamshin turarensa ne ya farkar dani daga duniyar Dana shiga a hankali na bude idona muna hada ido ya sakar min wani lallausan smiling dinshi me tsada, bansan lkcn Dana mayar masa ba, kyakyawar fuskarsa na zubawa ido INA kallo, a zuciyata nace kana tambayar me yasa mata suke binka? Abinda suke bi ai ba boyayye bane kabeer, zallar kyaun da Allah yayi maka suke bi, tabbas kabeer kayi gaskiya da kace dakai mace ne da nikaf zaka ringa sawa bcos you are more than handsome kanada kyau kabeer, ya Allah ka mallakamin kabeer, Allah ka taimake ni kayimin wanan gatan, ADON GARI sunan ya dace dashi sosai tabass kabeer adon gari ne da kowacce mace zatayi burin ta mallake shi hawaye ne ya zubo a idona batare da nasan fitowarsa ba.....katse min tunani yayi da cewa ya salm aysha kuka kike? Ko kin bige ne? Nace aa to meyasaki kuka? Ohh sabd na rikeki ko? Iam sorry naga zaki fadi ne shiyasa, da sauri ya sake ni sanan ya zubamin sexy eyes dinsa yace kike fitowa ba dankwali ko? Kuma yanzu idan wani yazo ya ganki a haka fa? Cikin shagwaba dani kaina bansan na iyaba nace wallahi dankalin ne nauyinsa nake ji, yaushe ka shigo garin? Zuwana kenan ko cikin gdn ban shiga ba dariya nayi me karamin kyau sanan nace eyya to mu karasa cikin gdn muna fitowa naga su nabil sai nemana suke da gudu sukazo suka rungume shi suna cewa oyoyo uncle, lkc guda muka shiga cikin gdn aunty Salma tana zaune a falo da mamaki ta kalle shi tace broda yaushe a gari? Ina fata dai lpy? Relax sis every thing is normal, kawai dai nazo na tafi da Aysha ne, abinka da yan uwan da suka shaku da juna, tana jin voice dinsa ta gane acikin damuwa yake maganar. Mikewa tayi ta kama hannunsa suka nufi bed room dinta
For correction or contributions 08067063932
Maman Aysha
[10/2, 20:17] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣7⃣0⃣➖1⃣7⃣5⃣
A bakin gado ta zaunar dashi sanan ta dubeshi tace nasan ko waye kanina, mutun ne me dauriya da zurfin ciki, sanan baka da sa Abu arai, komai da sauki kake daukar sa, kuma na Sani baka iya karya ba kuma baka son meyinta, kallo daya nayi maka na gane kana cikin matsaneciyar damuwa zama tayi a kusa dashi ta dafa kamanarsa sanan tace pliss my broda tell me the truth me yake damunka? Yar gdn senator Abdullahin Idris makarfi mum take son auramin, kinfi kowa sanin yanda mum ta dauka ki Mutanen nan, batason yan uwanta kamar yadda take son Haj Asiya, ba abinda bazata iya yimin ba idan naki bin umarninta. Ni kuma zuciyata Aysha takeso, INA son Aysha so me tsanani, mutuwa zanyi idan ban auri Aysha ba sister, kuma kinsan abin is very complicated iam very sure koba case din neehal mum bazata taba bari na auri Aysha ba indai taji lbrnta, wani irin kuka ya fara me ban tausayi iam confuse sister, iam totally comfuse pliss help me wallahi bansan ya zanyi ba nidai abinda na Sani kawai shine aysha ce rayuwata inhar ban auri Aysha ba to zaku rasani. Itama kukan take tabbas Aysha tafi dacewa dakai akan kowacce mace a duniya, kuma nima INA goyon bayanka, kuma daidai ta shigo da maganar auran neehal ne, da zamu samu a janye wanan maganar da sai indai karfin mu ya kare wajen ganin tayi accepting din Aysha. Sbd haka kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka, ka mika alamuranka a wajen Allah idan har aysha matar kace duk duniya ba Wanda ya isa ya hana, kadai yanzu kayi tunanin yanda zaka soke maganar neehal, zanyi insha Allah, nifa rabona da neehal dinma tun bata fi 8 yrs ba, idan muka hadu a hanya ma bazan ganeta ba, gaskiya nima na manta kamanin yarinyar. Shikenan zamuje mu tafi INA matukar alfahari da samun yar Uwa kamarki, Allah ya raya miki zuria'arki. Kiyi hakuri da dauke Ayshan da zanyi, wallahi na kasa jure rashin ta a kusa dani, tunda na koma na kasa baccin kirki, dariya tayi tace ai na dade da ganoka amma sai kayi disguising dinmu, shima dariya yayi sanan suka fito a tare.
A kitchen ya same ni na Dora lunch ya watsa min wani shu'umin kallo yace zuwa nayi na tafi dake, Sbd Faisal ya matsamin dole saina dawo mishi da matarsa, dariya nayi nace kuma kaga be fadamin ba, dama ai bazai fada miki ba, kuma nima bance ki fada masa ba. Juyowa nayi muka hada ido nayi dariya nace bazan fada ba, me like dafa mana ne? Favourite dinka nake dariya yayi da har saida fararen hakoransa suka fito sanan yace kinsan favorite dina ne? Nace eh mana, to meye? Pounded yam wit egusi soup dariya yayi sosai yace baki canka ba dambu ne favorite food dina, ohhh sorry kuma wallahi baba mero ta taba fadamin, shagwabe fuska nayi nace Amma zakaci wanan dima ai ko? Kai kawai ya daga min ya fice yana dariya. Cikin kankanin lkc nagama komai na jera a dining, duk inda nayi idonsa a kaina yake har muka zo cin abinci, nan ma ya kafeni da ido, sainaji duk na kasa sakewa Dan kadan naci abincin na mike na koma daki, shi kuwa zama yayi yaci ya koshi bayan ya gama ya biyoni har daki yace nazo mutafi, sai alokacin naji hankalina ya tashi Sbd mun saba da aunty Salma sosai har waje ta rakoni ta hadamin shatara na arziki muna zuwa bakin mota naga yanda jikin su yayi sanyi itada su nabil sainaji kamar kar na tafi, kawai saina Dora kaina a jikin motar na fara kuka, dama itama kadan take jira kawai saita karaso ta rungume ni tana kuka, folding din hanunsa yayi ya zuba mana ido yana kallon mu dayaga abin bana kare bane sai kawai ya janye aunty Salma ya maida ita gida, harya dawo INA kuka kama hannuna yayi yasani a mota driver shi ya bude masa ya shiga ya zauna a kusa dani, driver ya ja muka nufi airport.
Muna sauka a kano escort dinsa suka zo suka dauke mu, direct gdna muka wuce muna shiga naga an gyara gdn banda kamshin turare ba abinda yake kallon sa nayi da niyar tambaya, kawai sainaga baba mero ta fito daga kitchen da gudu na tafi na rungume ta nace i miss you baba mero, sanan na durkusa na gaishe ta sanan nakai kayana daki na dawo kallona yayi yace nifa iam hungry ki taimaka ki dafamin light food zanje gd nayi wanka na dawo nace to, nima wankan nayi nasa wata English gown yellow sanan na shiga kitchen nayi masa potatos ball da lemon kankana da madara, na kara saka turaren wuta a gdn. Sanan na dauko wayata na kira aunty Salma mun Dade muna hira da ita sanan mukayi sallama.
Sai wajen 8 pm ya shigo gdn ni nayi serving dinsa yaci abincin banda santi ba abinda yake bayan ya gama muka fara hira, daidai nan Faisal ya kirani INA dauka yace yana waje, nan take gabana ya fadi sainaji bana son fita adon gari yana nan, Amma sai nace masa OK gani nan zuwa. Dagowa yayi yace INA zaki? Faisal ne yazo, dama kin fada mishi kin dawo ne? Eh ya kirani dazu, OK saiki tashi ki je ai, ya maida kallonsa kan phone dinsa, kasa tashi nayi saida ya kara cewa jiranki ake fa, sanan na tashi jiki ba kwari na fice, muna zaune da Faisal yazo ya shiga motarsa ya fice daga gdn, Faisal yace yau me yasami Mr kabeer? Nace me ka gani? Naga ko yayi min magna, kamar be taba sanina ba, murmushin yake nayi nace may b sauri yake
Maman Aysha
[10/14, 9:53 PM] Chopy: [10/3, 12:40] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣7⃣5⃣➖1⃣8⃣0⃣
Yana barin gdna gdnshi ya wuce zuciyarsa banda bugawa ba abinda take yakamata nayi saurin daukar mataki akan soyayya ta da Aysha, idan ba haka ba I will loose her phone dinsa ya dauka ya fara dialing no kamal, duka biyu ya dauka hlo adon gari garin? Lpy kalau ango, tunda amarya ta tare najiga shiru, fushi nake dakai Sbd bakazo kaga dakin amarya ba, kayi hakuri zanzo insha Allah, to Allah ya kawo ka amin, ya lbrn Mutanen gdn? Suna nan kalau, ya neehal ita yaushe ne bikin nata? Ankusa da yanzu tare aka hada ma, mijin da zata aura ne yayi tfy, Amma yanzu ya dawo, Allah sarki shima Dan Kaduna ne mijin? Eh Dr haidar ba, Dan abokin dad dinmu ne alhaji Bashir bakori, shima likita ne yanada asibiti me suna bakori obstetrics $maternity private Hosp, acan neehal take aiki, eyya Allah ya taimaka, Bari na barka haka saida safe to Allah ya kaimu nagode sosai.
Dr marwan friend dinsa ya kira, suna gaisawa yace marwan Kasan Dr haidar Bashir bakori a Kaduna? Sosai ma, he is my friend, don Allah tromin no sa don Allah, me zakayi da ita? Don Allah tromin koma meye zakaji daga baya, OK to zan tromaka yanzu
No tana shigowa ya fara dialing, ana dauka suka gaisa, sanan ya fara masa bayani kamar haka" sunana kabeer M BAGAUDA, mu family friends din gdnsu neehal ne, mahaifiyata tana kokarin hada aurena da neehal, ba tare da saninta ba, kuma nasan kai take so Sbd haka na kira na fada maka kayi saurin yin wani Abu akai, domin kuwa akwai kyakyawar fahimta a tsakanin parents dina da nata, idan har mum dina tayi magana to ba abinda zai hana a auramin ita, Sbd haka Sbd haka kayi kokarin yin wani Abu daga yanzu zuwa next WK, banaso na zama sanadin raba masoya masu tsananin son junansu irinku. Wata sansanyar ajiyar zuciya yayi sanan yace nagode Mr kabeer tabbas neehal ce rayuwata, kuma rabani da ita tamkar rabani da rayuwata ne, insha Allah tun daga yau zan fara daukar mataki, nagode Allah ya saka da alkairi
3days later
Suna zaune da mum dinsa suna hira aka kirata a waya, tana dubawa taga Haj Asiya da sauri ta dauka bayan sun gaisa Haj Asiya tace dama kira nayi na fada miki gobe zaa kawo lefen yarki, kiyi hakuri don Allah na fada miki late, Wallahi abin ne ya taso urgent, muma be fada mana ba sai jiya. Jiki a mace mum tace oh ikon Allah dama kun mata miji ne? Eh anyi mata HAJIYA, ai Dan abokin abbansu ne ma, to Allah ya tabbatar da alkairi tace amin, amma sai kinzo ba HAJIYA tunda abin yazo a kurarren lkci, bikin nan da wata daya zaa saka, so in Allah ya kaimu bikin kyazo, to shikenan Allah ya kaimu.
Kallon shi tayi rai a bace kaji wai lefan neehal zaakai gobe, a zaune yake Amma saida ya mike, neehal din da kike so na aura? Eh wallahi, kai Amma wanan Abu be yimin dadi ba mum, naso na cika miki burinki, naso na auri neehal Sbd na faranta miki mum, Amma Allah yasa haka shi yafi alkairi tace amin son, kaima Allah yayi maka sauyi da mafi alkairi yace amin, bari naje gd amma zandawo da daddare insha Allah, to shikenan saika dawo.
Yana fita ya kira aunty Salma a waya ya fada mata duk abinda ya faru, tayi murna sosai sanan tace zan shigo kano gobe insha Allah, Sbd haka kafin nazo kayi kokari ka sanar da mom maganar Aysha, to shikenan sis nagode.
7:30pm
Ya shiga gdn mum cikin sa sanye da farar jallabiya saida ya durkusa ya gaisheta sanan ya zauna, sun Dade a zaune ba wanda yayi magna, sanan daga bisani ya daure yace mum wata magana nake so muyi dake, go ahead son INA jinka, dama game da zancen aurena ne, tunda Allah beyi da neehal ba, na samu wata yarinyar da nake so, alhamdulilla mum tace, Abu yayi dadi wacece ita? Yar gdn waye? Kuma a wane gari take? Mum ban taba yi miki karya ba, kuma yanzu ma bazan miki ba Amma don Allah mum inaso ki taimaki rayuwata ki amince min da auranta sabd ban taba son mace a duniya kamar yanda nake sonta ba. Sunanta Aysha, a gdn alhaji Ahamad TURAKI ta rayu tun tana jaririya, shi ya bata tarbiya ya bata ilimi daga karshe ya koreta Sbd son zuciya, ataikaice dai a yanzu batasan kowa nata ba, Amma idan kin amince min ni zan aureta haka, tanada tsananin kirki, tanada tarbiya, tanada kyawawan dabiu da kallo daya zakiyi mata kiji kina sonta.........wata mahaukaciyar tsawa ta daka mishi da har saida yayyan hanjinsa suka kada, sanan tace duk abinda take dashi ya tashi a banza tunda bata da asali, idan har kaga auran nan ya yuyu saidai akan Abu biyu, ko bana Raye, ko kuma bada yawuna ba, Amma indai ina Raye ban amince ka auri yarinyar da bata da asali ba da kakkausar murya ta karasa maganar mikewa tayi zata shiga daki yayi sauri ya rike kafarta yana wani irin kuka me ban tausayi don Allah mum ki taimaka min, wallahi Aysha ce rayuwata, idan har ban aureta ba zan iya rasa rayuwata, wallahi mum idan ban aureta ba mutuwa zanyi plissssss! Aikuwa saidai ka mutu, daidai ka auromin Marat asali a yanda matsayin ka yake a Nigeria, gara ka mutu ta zare kafarta ta shigewarta daki. Ya Dade yana kuka a wajen, daga baya ya dauki key motarsa ya fice daga gdn