[10/14, 9:51 PM] Chopy: [9/6, 17:34] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣➖5⃣
Shaharrariyar kuma kyakkyawar matashiyar yar jaridar nace da take tashe ke gafatar da program a gidan television dinsu me suna PYRAMID TV, ba wata bace face AISHA AHAMAD TURAKI. Duk wasu masoyan pyramid TV , ayanzu haka suna bakin TV dunsu suna kallon program din da take bayani kamar haka " Assalamu alaikum jama'a masu kallo kamar yadda kuke gani muna kan titin zariya Road inda muke dauko muku wanan rahoto direct daga wajen bikin bode katafaren ginin nan me suna BAGAUDA HOUSE. Kamar yadda masana sukace sunyi bincike duk 9ja ba ginin daya kaishi tsaho, sboda yana dauke da 500 upstairs a ciki, kuma ba tsawon ginin ne kawai zai birge me kallo ba, shi kanshi design din ba irinsa a 9ja. Duk manyan bakin da aka gayyata har me girma San kano yazo yanzu zuwan me girma governor ake jira.
Faisal na ya kalli sagir abokina ina masifar son yarinyar nan sbd kwarewarta a aiki, tana da confidence ga Uwa uba kyau, dariya sagir yayi sanan yace yanzu kayi magana kace kana son fitinannan kyaunta, to ka fadamata mana. Kai! Ai bazan Iya ba kasan Dan banzan kwarjini ne da ita, Amma indai da gaske kana sonta to dole kayi mata magana idan ba haka ba zakayi son maso wani,,,,,,,,,,muryar tace ta katse musu zancen da suke da cewa jama'a kamar yadda kuke gani me girma governor yazo kuma anfara gabatar da abinda ya Tara mu. Na sami nasarar ganawa da managing director na BAGAUDA trading company limited wato wato the youngest multi billionaire KABEER MOHD BAGAUDA Wanda matasa yan uwanshi ke yiwa kirari da ADON GARI, yallabai gashi yau Allah ya cika maka burinka, har ana bikin bude katafaren gininka da ba irinsa kaf 9ja, so idan bazaka damu ba pyramid TV tanaso tasan duk 500 upstairs din kayi occupying ko kuwa zaka bayar da hayar wasu? Zan bayar da hayar wasu. OK to yallabai wane irin farin ciki kake ji, kuma me zaka ce da masoyanka Wanda suka zo, da kuma Wanda suna nan a bakin TV nsu suna kallon ka? Wani lallausan murmushi yayi farin cikina baxai fadu ba sabd na Dade ina burin zuwan wanan ranar, gashi kuma yau Allah ya nunamin sbd haka tsakanina da Allah sai godiya alhamdulilla. Masoyana kuma ina mika godiyata agareku, nagode da kulawar da kuke nunamin. Wani shu'umin murmushi nayi sanan nace pyramid TV tana maka murna Allah ya sanya alkairi, shima murmushin yayi sanan yace nagode. Jama'a kamar yadda kuke gani tattaunawar da mukayi ce Mr kabeer, dafatan masoyan adon gari da basu sami damar zuwaba suna tare da pyramid TV.
Zee ce ta saki wani ihu yehhh samira zo ki gani yau adon gari yayi smiling, dama yana murmushi? Allah ya mallaka min KB, Allah yasa shine mijina, mama ce tace a hakan kuna nade a gd kullum zaki aureshi? Kina ganin shegiyar yarinyar nan kamar wasa yanzu ba Wanda besan taba, duk wani me fada aji agarin nan sun santa, kamar yadda take gadara pyramid TV ta ubanta ce kuma haka, Amma don rashin zuciya kuna gd saidai kuci Ku kwanta, idan baki wasa ba ita ta aure Kabeer din ai, don naga alama ita yakewa murmushin. Don Allah mama dena fada kar zuciyata ta buga kinsan yadda nake son kabir kuwa?
Maman Aysha
[9/6, 20:13] Amina Yakubu: πππKABEERππ
5⃣➖1⃣π
Bayan an watse daga wajen taron office muka koma, muka karasa kammala wani aiki sanan na tafi. A gajiye na shiga gdn a compound na sami zee tana waya ta kalleni ta tabe baki angama yawon karuwancin an dawo? Duk rahoton da kika dakko dazu na gani, kuma naga kallon da kk yiwa KB, sbd haka idan ma sonshi kike to wallahi ki daina KB nawa ne ni kadai insha Allah ni zan aureshi. Wani murmushi nayi nace nima zan tayaki da addua Allah ya baki KB Yaya zee. Na wuce part dinmu, INA shiga na sami mum a zaune kawai saina fada kanta nace wash wallahi yau na gaji mum, ai naga rahoton da kika dauko very interest Allah ya kara daukaka min ke, amin mum ina junior da basma suna ciki basusan kin dawo ba, anje nayi wanka to kafin suzo su dameni. Mikewa nayi na shiga toilet din dakina nayi wanka nasa wata doguwar riga na fesa turare, sanan na dawo falo naci abinci, sanan junior da basma suka dauko H/work dinsu na koya musu dad ne ya shigo aikuwa da gudu junior ya tafi ya dale shi oyoyo dad, sai kawai basma tasa kuka wai ya rigata kamota nayi haba basman aunty, rabi dashi bazan sayo mishi chocolate ba, idan da sabo mun saba da rigimarsu baka isa kayiwa daya Abu ba kaiwa daya ba. Karasowa Abba yayi ya zauna, sanan nace sannu da zuwa Abba yace yauwa Ummi na, naga aikin ki yana kyau iam proud of you Allah ya kara temakawa nace amin, sanan nayi musu saida safe na kwashi yan rigimar mum junior da basma muka shiga daki.
Washe gari , da wuri na tashi sbd dad a part dinmu yake suna can suna bacci da mum na tashi na hada break fast, na gyara gdn nasa turaren wuta, sanan nayiwa twins din mum wanka na shiryasu muna gama cin abinci nayi dropping dinsu a sch sanan na wuce office. Ina zuwa manaja ya kirani naje office dinsa, dama jama'a ne sun damemu akan sunaso suji matakan da Mr kabeer yabi yayi achieving goal dinsa akan ginin BAGAUDA house, shine nakeso kuje Ku same shi ya fada muku time din da zaku sami damar ganinsa, kinsan irin wanan manyan mutanen anashan wahalar ganinsu, Nace to, office dinsa zamu kenan? Eh, to bari muje. Elbash na samu yana wani aiki, nace idan ka karasa oga ya bamu aiki, wane aiki kuma? Zuwa office din adon gari, tab lalle ya hadamu da aiki kam wanan muskilin mutumin, danma dake zamu shine saukin abin, hammm in din wacece? Shifa wanan da kake gani mata basa gabanshi. Amma wallahi duk kin matansa idan ya ganki saiya jijjiga, sbd ke acikin mata daban kike, sai antara mata Dari kafin a sami guda daya irinki. Basar dashi nayi idan ka gama kayi min magana mu tafi ina office, yace is alright.
A motata muka tafi, saida muka hau lifter sbd a hawa na 200 office dinsa yake. Ba yanda bamuyi da sakatariyarsa ba akan ta barmu mushiga Amma taki, daga karshe muka nemi PA dinsa mukayi magana dashi, sanan yaje yayi masa bayani shine yace mu sameshi ranar Saturday a gd, mukayi godiya muka tafi.
Saturday 4pm
4:30 dot shine time din daya bamu, kuma PA dinsa ya fada mana baya son African time, sbd haka tun 4pm mukaje gdn muna jiran a kiramu shiru, gashi bamu karbi no PA din ba. Muna zaune har 5pm tayi nacewa elbash ko mutafi yace mu Dan kara hakuri dai, na duba naga bayan mu akwai mutane sunfi mutun goma suna jiransa. Kai gaskiya elbash na gaji mutaf.....ban karasa ba naga gate yana bude kanshi jerin gwanon motocinsa ne suka sako kai Wanda yawansu yakai guda 12 kuma duk cikinsu ba ta kasa da 3million, da gudu aka bude masa kofa ya fito, body guards dinsa suka Mara masa baya yana wata tafiya ta kasaita suka shiga ciki. Ya shiga befi da 10 minutes ba saiga PA dinsa ya fito jama'a don Allah kuyi hakuri yallabai yace ba Wanda zai Iya gani ayanzu, sabd ya dawo agajiye yana bukatar hutawa, sbd haka don Allah kuyi hakuri zan karayiwa kowa sbn schedule na ganinsa, wasu daga cikin Mutanen sukace ba matsala, cikin bacin rai nace elbash me yasa wasu masu kudin basu da adalci ne? Wanan ai rashiin sanin mutuncin Dan Adam ne, nidai tpy zanyi mayi waya, yace to shikenan.
2 days later
Yauce ranar daya kara bamu appointment, 11am mukayi dashi ko baccin kirki banyi ba muka tafi Amma Dan renin hankali sai yace muyi hakuri Tuesday mu dawo. Min taho akan hanya mukaga mutane a tare anata hayaniya daidai jikin wani katon kamfani muka tambayi me ya faru? Sukace gubataccen ruwa ake sakar musu daga kamfanin yake Shga musu rijiyoyi da gdajensu yana illatar da Mutanen yankin sosai kuma sun yiwa shugbn kamfanin magana beyi wani Abu akai ba, shine suke zangazanga. Aikuwa nan take na fito da kayan aiki na fara dauka, sanan nayi hira da wasu daga cikin Wanda abin ya shafa. Muna komawa office na watsa, cikin kankanin lokaci gari ya dauka har gwamnati suka shiga maganar sunsa anyi magana da shugaban kamfanin kuma ya bada hakuri yace zai gyara.
Maman aysha
[9/6, 23:06] Amina Yakubu: πππKABEERππ
π➖1⃣5⃣
9pm
Ina kwance a daki dad ya shigo ya kwala min kira rai abace da sauri naje nace gani, me ya hadaki da alhj danladi? me kamfanin maganin sauro, OK na kwashe lbrn abun daya faru na fadamasa, kirana yayi a waya yanata masifa wai anci masa zarafi a gdn TV na, Ashe shine marar gaskiya, is OK jeki Allah yayi miki albarka nace amin
4days later, 5:15pm
Muna kofar gdn Mr kabeer, yau shine zuwanmu na shida kenan. Muna zaune saiga PA yace bismilla mu shiga. Gidan ba karamin girma ne dashi ba, maganar kyau da tsaruwa kuwa abin baa magana saida mukaje bakin falon shiga gidan kawai saigashi ya fito da body guards dinsa oh Suleiman harka kirasu ne? Wallahi kaga wani important meeting ne ya taso min, saidai su dawo gb ya cigaba da tafiyarsa ko be ta kanmu beyi ba. Cikin bacin rai na tari gabanshi me yasa Ku masu kudi Baku da adalci be? Me yasa kuka dauki Dan Adam ba komai ba bayan kuma ko wane mutum da irin baiwar da Allah yayi masa, zuwanmu shida gidan nan bama samun ganinka wanan shi ya nuna cewa bakada cika alkawari bayan kuma cika alkawari yana daga cikin quality na salihan bayi......tasssss ya daukeni da mari ke wacece da zaki zo kina fadamin irin wanan maganar kuma har cikin gdn, yar iska kawai, ko angayamiki ni mata suna gabana, ko kuma angayamiki ina daukar nonsense? Ku fice min daga gd karna kara ganin kafarki a gdn nan. Harya fara tafiya na kara shiga gabansa karkayi tunanin don ka mareni shikenan kaci banza wallahi bashi ka dauka, ko bayanzu ba sainayi maka abinda ya bata maka rai fiye da yanda kayimin, kuma inaso ka Sani ni ba irin yan matan da kake mu'amala dasu bace, kuma dukiyarka ko wani kyaunka baya gabana harkar aiki CE ta kawoni gdnka, kuma don kana gadara kana da kuni baka isa ka wulakanta ni ba, zan kara repeating kaina Marin da kayimin bashi ka dauka kuma wallahi saina rama. Daya daga cikin body guards dinsa ne ya iyo kaina kawai sai naga ya daga masa hanu, sanan ya kalleni cikin bacin rai yace walk out from my house juyawa nayi na kalli elbash da yayi mutuwar tsaye nace zo mu tafi. Raina a bace na shiga gd wanka kawai nayi na gabatar da sallar magriba, nayi karatun kur'ani har akayi isha'i sanan na fito falo su basma sukazo suna tayimin surutu, ni kuwa yake kawai nake sbd duk lkcn dana tuno marin da adon gari yayi min sainji kmr nayi hauka Dan bakin ciki. Dad ne ya shigo da fara'arsa Ummi na, nace naam dad gobe idan Allah yakaimu zakiyi bako, kuma koda wasa ban yadda ki wulakantashi ba nace to yayi mana sallama ya tafi
2wks later
Naje BAGAUDA mall sayayya na fito kenan saiga jerin motocinsa sun danno kai cikin mall din tsayawa nayi INA kallonsa har aka bude masa kofa ya fito mar daga sama saiga wani mutun daga gani daya daga cikin staff din mall din ne, fada naga yanayi masa saidai bansan me yake CE masa camera ta na saita na fara daukarsa, kawai sainaga ya taskawa mutumin mari har guda biyu, bayan ya tafi na Kira mutumin muka koma gefe na tambaye shi me yayi masa yace sata yayi wa wani mutun ya bashi kaya yasa masa a mota ya boye wasu, shine mutumin yakai kararsa nace ni yar jarida ce, inaso ka juya lbrn ka da temako ka nema yayi maka shine ya mareka zanyi maka tambayoyi, idan kayi yanda nace zan baka 50k. Aikuwa ya amince
Maman aysha
[9/7, 11:39] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣5⃣➖2⃣0⃣
8:30pm
Jama'a barkanmu da warhaka, barkanmu da sake saduwa daku acikin wanan shiri namu me farin jini na ya take ne? Kamar yadda kuka Sani ya takene? Shiri ne da yake kawo muku abubuwan alajabi, ban mamaki, da kuma barkwanci. A yau shirin namu zai fara ne da abin mamaki, abin mamakinmu nayau akan shahararran matashin me kudin nan ne kabir M Bagauda, Wanda yan mata da samari suke kira da adon gari. Wata yar iskar dariya nayi sanan naci gaba"duk Wanda ya kalli video nan dana sako muku yanzu, zaiga Mr kabeer ne ya takarkare ya taskawa wani bawan Allah mari, abin mamakin anan shine, mutane da yawa suna daukar Mr kabeer a matsayin mutumin kirki, me tausayi, kuma me son talakawa. To idan har hasashen da mutane suke masa gaske ne, me ya jawo hankalinsa ya mari mutumin da na tabbata ya haifeshi? Kuma wane irin lefi wanan bawan Allah yayi masa? Masu kallo waka a bakin me ita tafi dadi bari na hadaku da baba dattijo" baba me zaka ce game da tambayar danayi yanzu? Wato abinda ya faru shine "naji mutane suna fadin temakonsa, shine naje wajensa nima ya temaka min, Amma sai aka sami akasin hakan Ina gama fada masa matsalata kawai saiya mareni yace na tafi na bashi waje. Waw idan har zan Iya tunawa ba wanan ne karo na farko da adon gari yayi mari ba, domin kuwa ya tabayi agabana. Abin mamakin anan shine me yasa adon gari ya mari baba? Kudin da baba dattijo ya nema ne bashi da shi komai? Ko kuwa adon gari ya canja raayi daga me temakon talakawa ya koma marar temako? Naso jin amsar tambayata daga wajen adon gari saidai kash ban sami ganawa dashi ba. So masoya adon gari Ku biyomu wani satin don jin yadda zata kasance, baba dattijo ya take ne? Baba yace hakan take, wata yar iskar dariya nayi nace jama'a nima nace hakan take a madadin gdn TV na pyramid TV ni Ayshat Ahamad TURAKI nake ce muku maassalam sai mun hadu a shiri na gaba.
Zaune yake ya kurawa TV din ido xuciyarsa band tafarfasa ba abinda da take, nan take wayoyinsa suka hau kuka friends dinsa ne suke kira Amma yaki dauka sbd yasan zancan zasu yi mishi, wani kiran ne ya kara shigowa saiyaga mum dinsa ce da sauri ya dauka hlo mum kabir me yake faruwa ne? Ya akayi a matsayinka na babban mutun a gari sukai maka wanan tozarcin? Ita yarinyar waye ubanta a gari da zatayi maka haka eye? Kodai wasu ne suka biyata tayi maka haka? Wallahi mum ni kaina banida amsar wanan tambayoyin naki, abinda na sani shine da gaske na mari tsohon, Kuma zamba cikin aminci yayi, kuma kinsan ba mutumin dana tsana a duniya irin me cin amana, shi yasa na mareshi. Amma karki damu mum insha Allah zan dsuki mataki akai. Mikewa yayi ya kalli Sulaiman da jajayen idanuwansa tunda uwata ta haifeni baa taba bata min rai irin Wanda yarinyar nan tayimin ba, wallahi saita raina kanta, kuma saita gane dukiya ba karya bace, duk Wanda yake da kodi yafi karfin wulakanci. Ka fadawa Barr Bashir gobe inason mgn dashi, to shikenan ranka yallabai saida safe.
Zuciyata tayi fari tas don na tabbata duk inda adon gari yake yanzu yana nan acikin bacin rai, wayata na dauko na kira baba dattijo nace baba kana ina? Yayi min kwatancen inda yake nace to ka jirani INA zuwa yanzu. Baba abinda nakeso dakai shine ka tattara kayanka kabar garin nan sbd zaka Iya shiga matsala, a wane gari kake? Yace Adamawa, OK to zan kara maka yawan kudin ya zama 150k don Allah baba ka tsarkake zuciyarka kaje kaja jari dasu, kaji tsoron Allah, kayi Sana'a ka nemi na kanka. To nagode Allah ya zaka miki da alkairi, dama talauci ne yasani, Amma insha Allah zanje naci gaba da sanaata ta saida gwanjo. Saida na saukeshi a tasha ya shiga mota sanan na tafi gida cike da farin ciki
Maman Aysha
[9/7, 15:32] Amina Yakubu: πππKABEERππ
2⃣0⃣➖2⃣5⃣
Wacece Aisha Ahamad Turaki?
Yace ga Alhj Ahamd TURAKI, Dan kwangila Wanda yayi suna duk area Kano ba Wanda be San da zamansa ba, haifaffan garin bichi ne, kuma hamshakin me kudi ne daya mallaki kamfanoni da gidaje, kuma shine mamallakin gdn TV na pyramid TV. Matanshi biyu ne, Haj bilkisu itace uwr gd yayan ta biyu Zainab da samira, ita kuma amaryar sunanta Haj Jidda yayan ta uku aysha ce babba saida aka haifeta da shekara goma sanan aka haifi yan biyu wato basma da Ahamad, alhaj sbd tsananin murna yasawa Ahamad sunansa shine ake kiransa da junior. Alhaji yana tsananin son amaryarsa sbd tanada kirki gata da son addini. Idan yana tare da ita mantawa yake yanada wata matar, kuma yanda yake tsananin sonta haka yake son yayanta, duk Wanda ya shiga gdn alhaj Ahamad a kankanin lkc zai gane alhaji yafi son Haj Jidda da yayan ta. Gabady yayan nasa sunyi degree idan ka dauke yan biyu. Zainab political science ta karnta, public admin ita kuma aysha mass communication. Da Haj bilkisu da yayanta a bichi suke da zama, ita kuma Haj Jidda a Kano da alhaj ya gama ginin damfareren gdnsa saiya debosu ya hadasu waje daya Amma kowa da part dinsa. A yanzu haka Zainab shekararta 24, samira 22 aysha kuma 18yrs.
Waye kabeer M Baugauda?
Dane ga marigayi senator muhd Tahir BAGAUDA, mahaifinsa mutumin kirki ne kuma adali Dan asalin BAGAUDA ne shekararsa 12 yanayin senator a Kano, ya kawo cigaba a jahar Wanda tunda suke samun Dan siyasa baa taba samun me kirki da temakonsa ba, wanan shine dalilin da yasa sukai ta zabarshi har saida yace ya gaji, ba a siyasa kawai ya tsaya ba idan akazo harkar business ma shahararran Dan kasuwa ne ya mallaki kamfanoni da yawansu zai kai 40, banda sauran kadorori. Matarsa daya Haj asma'u da yayanta biyu wato Salma itace babba barrister ce, tana auran wani house reps a abuja take da zama, sai kaninta kabeer shi kuma civil engineer ne he very handsome, so kind, intelligent and very respectful. Mahaifinsu ya rasu ne a hatsarin mota akan haryarsa daga abj zuwa Kano, ba Iya iyalansa ne sukayi rashin sa ba, gabadaya Mutanen 9ja ne sbd alhaji mohd dattijon arziki ne. Bayan an raba gado sai kabeer yaci gaba da kula musu da dukiyar, kuma yana samun kwangila sosai sbd governor me ci a yanzu aminin babansa ne, babansa ne ya fara sashi a siyasa, kuma ba lefi ya rike alkawari sosai. Tun rasuwar mahaifinsa ya maye gurbinsa wajen temako da kaunar talakawa, har yaso yafi mahaifinsa ma, mata basa gabanshi kuma bayasan reni. Mutane ba karamin mamaki sukayi ba da sukaga program ya take ne? Da aysha ta nuna sbd kowa yasan ba halinsa bane
Cigaban labari
Maman aysha
[9/8, 09:50] Amina Yakubu: πππKABEERππ
2⃣5⃣➖3⃣0⃣
Cigaban labari
Daga tashar gd na wuce naje nayi wanka nayi sallah, sanan na fito falo ina cin abinci muna hira da mum, su basma kuma sun Dora Kansu akan cinyata. Abba ne ya shigo yayi dariya kaga mummyn yara me kuke tattaunawa ne da yaran naki? Murmushi mum tayi sanan tace hirar duniya muke, mikewa nayi zan koma naki don naga alama yau dad acikin soyayya yakeπ, kawai sainaji yace zauna ummina magna nake so muyi dake, kinsan alhaji Lawan mati? Eh Abba, deputy governor ko? Yawwa yar gari, tare muke dashi yanzu haka yana guest Palo, shine bakon danace zakiyi last WK kuma be sami damar zuwa ba sai yau, inaso kiyi sauri ki shirya kije karki bata masa lkc, sauran bayani idan kin dawo kyaji. Jiki ba kwari na tashi na koma daki, dama gown ce ajikina rolling kawai nayi na fita. Har kasa na durkusa na gaishe shi sanan ya kalli securities dinsa yace Ku bamu GU, da rawar jiki suka fice sanan ya dawo da hanklnsa wajena ba saina yi introducing kaina ba, nasan kinsan koni waye. Ina daya daga cikin masoya kallon program din da kike na Ya Take Ne? Kullum bana missing dinsa, idan ina kallo har wani nishadi nake,da ina ganin kamar program din ne yake birgeni daga karshe saina gane ke nakeso, na kamu da sonki alokacin da bansan lokacn daya shiga ba, ina tsananin sonki Aysha, kuma bazan boye miki ba matana biyu da Yaya goma. Ya salam haba baba don Allah, sona fa kace kanayi? Ba Kaine Baban su nazifi Lawan ba? Yes nazifi Dana ne, Amma kuma kace kanason karamar yarinya kamar ni, iam just 18yrs fa, don Allah ka rifamin asiri ka janye wanan maganar pliss. Bazan Iya ba Aysha da zan Iya janyewa da ban tari mahaifinki da mgnr ba, nayi kokari naga nayi ignoring abin Amma na kasa, don Allah ki temaka min aysha wallahi ina tsananin sonki, yanzu zan baki lkc kije kiyi tunani akai, zan dawo jibi in Allah ya kaimu na barki lpy. Jiki ba kwari na shiga Palo su mum suna nan zaune yanda na barsu dad ne ya kalleni harya tafi? Nace eh, to zo ki zauna nace to, sanan ya fara magana "alhaji Lawan uban gidana ne, yayi min abubuwa na alkairi Wanda bazan Iya saka mishi ba saidai nayi masa addua kawai. Tunda name dashi ban taba Neman Abu a wajensa na rasa ba, kullum addua nake Allah ya kawo ranar da zai nemi wani Abu a wajena, nima na saka mishi da abinda yake min, kwatsam sai gashi yazomin da maganar yanaso na bashi auranki. kuma aduniya ba abinda alhaji Lawan zai nema a wajena banyi mishi ba, sbd haka inaso kisa aranki shi na zaba miki a matsayin miji, kuma nasa date din daurin aure nan da 2 wks. Sanan lawyer n Mr kabeer yazo ya sameni yace mu tabbatar mun wanke Mr kabeer akan kazafin da akayi masa idan ba haka zasu shigar damu kotu,kuma kinsan banida kudin da zan Iya ja dashi, sbd haka inaso ki wanke shi a shirinku na gobe da zakiyi. Mum ce tace Amma daddyn yara taya zaayi ka rasa Wanda zaka aura mata sai tsoho, mutumin daya fika a hafe ma. Ya isa ya dakawa mum tsawa (abinda be taba mata a gabanmuba) indai akan alhaji Lawan ne karki kara yimin magana, na Riga na gama yanke hukunci, Ya mike ya tafi daki. kuka nake me taba zuciya mum me yake shirin faruwa dani ne? Me yasa dad ya zabi farin cikin uban gidansa fiye da farin cikin yarsa daya Haifa? Wallahi mum bana sansa tsohone sosai don Allah kiyi wani Abu akai. Kiyi hakuri Aysha zan yi mishi magana insha Allah bazaki aureshi ba, muje ki kwanta bazan taba barin farin cikin ki ya rushe ba, saida ta rakani har daki na kwanta sanan ta tafi, murmushin jin dadi nayi nace mum ba karamin sona take ba Allah ya bamu ikon yimusu biyayya.
Mama ce zaune a tsakiyar yayanta inajinki samira kikace deputy governor ne yazo gdn nan eh wallahi mama wata yar iskar dariya tayi lkc yayi da zan tarwatsa rayuwar Haj Jidda, na tabbata bazata so yatta ta auri tsoho ba kunga akwai rigima kenan, sabd haka zanje na sami boka dankundalo yayi min aikin da zasuyi rigimar da zata zama sanadiyar barinta gdn.
Maman Aysha
[9/9, 11:33] Amina Yakubu: πππKABEERππ
3⃣0⃣➖3⃣5⃣
Banyi wani baccin kirki ba inayin sallar asuba na zauna kart har saida rana ta fito, nayi addua na roki Allah ya fitar dani daga halin da nake ciki. Jiki ba kwari na tafi na hada break past, sanan nayi wanka, na tashi twins din mum ma na musu sukaci abinci sanan na kaisu sch. Gida na dawo na kwanta banda tunani ba abinda nake dad ya rasa Wanda zai auramin sai tsoho? Yaushe dad ya zarme da son kudi da har yake son kuntata rayuwa ta? Why dad don Allah kuka me karfi yaci karfina, saida nayi me isata sanan naje na wanke fuskata. Sai wajen 10 suka tashi ina jin motsinsu na fice naje na durkusa na gaishe su dad yace ummina lpy baki fita aiki ba yau? Murmushin karfin hali nayi nace yanzu zan fita, yau bamu da aiki da yawa ne shi yasa. Alright, ya zauna yayi break sanan ya fice. Mum ce ta kalleni ana ganin fiskarki ansan kinyi kuka Aysha, don Allah kiyi hakuri ki fitar da mgnr nan a zuciyar ki, insha Allah komai zai daidaita kinji dota na nace Allah yasa mum tace amin, ke kinci abincin ne? Nace aa, to zauna kici. Sai wajen 11am na shiga office, ina shiga elbash ya biyo bayana beauty meke faruwa ne yau? Na kiraki yakai sau goma bakiyi picking ba, dama wani mutun ne ya kawo kukanshi, wai wani alhaji yasa anyi nakiya irin wacece ake idan zaa fasa dutse a jikin gdnsa, as a result ginin yana Neman rushewa, kuma ya fadawa alhajin Amma yaki ya tausaya mishi, so shine nakeso muje mu dauko gdn, abi mishi hakkinsa, nace to muje. Beauty yau kalau kk kuwa? Duk da nasan you're calm, Amma yau shirun naki yayi yawa, is like akwai abinda yake damtafi? Ba abinda yake damuna muje kawai, ban yadda ba don Allah ki fada min, ya salam elbash banason mgn da yawa fa, dariya yayi yace oh I see ashefa yan jarida basa son mgna, nima dariya nayi muka fita a tare.
8:pm
Jama'a assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa acikin wanan shiri namu na Ya Take Ne? A yau shirin namu zai fara ne da bawa the youngest multi billionaire Mr kabeer wato adon gari hakuri akan akasin da aka samu a shirin mu daya gabata. Kamar yadda kuka Sani pyramid TV gdn television ne da yake yada abubuwa domin a kwatawa talakawa yancinsu, wanan shine dalilin da yasa muka haskawa jama'a abinda baba dattijo ya sanar mana saidai da muka tsananta bincike mungano cewa abinda ya fada mana ba gaskiya bane sbd haka don Allah pyramid TV na Neman afuwa a wajen adon gari da masoyansa. Shirin da muke tafe dashi acikin wanan sati shine.......
Jama'a anan muka kawo karshen shirin mu na wanan satin, ina me matukar godiya ga masoyana, kuma ina me bakin cikin sanarda masoyana cewa daga yau bazaku kara ganina ba, idan da Wanda na taba batawa rai daga lkcn Dana fara gabatar da wanan shiri zuwa yanzu don Allah su yafemin, amadadin hukumar gdn pyramid TV ni ayshat Ahamad TURAKI nake cewa bissalam.
Ina fita daga show room din office dina na shiga na kifa kaina a table ina kuka me taba zuciya shikenan rayuwata ta ruguje wanan wane irin kaddara ne kuka nake sosai. Elbash ne ya shigo office din aidama na fada yau ranki a bace yake kk musamin, kuma naji kin fadawa mutane cewa daga yau bazasu kara ganin ki ba, akwai abinda kk boye min beauty, don Allah ki fadamin me yake faruwa dake? Ko duk shakuwar da mukayi har yanzu bankai matsayin da zaki fadamin damuwarki ba? Ba haka bane elbash, to indai ba haka bane fadamin what is wrong with you? Auran dole dad yakeso yayimin da mutumin da ya girmeshi ma ahaife, wai deputy governor dad yake son aura min nan da 1 wk, kukane yaci karfina don Allah kababi shawara elbash yanzu ya zanyi? Kiyi hakuri kiyi biyyaya Aysha, kana nufin nayi biyayya na auri tsoho me mata biyu da yayya goma? Na Sani is unfortunate Aysha, Amma idan kk mishi biyayya Allah sai yayi miki zsbin abinda yafi alkairi. Shikenan zan duba na gani, ni zan tafi saida safe to Allah ya kaimu
Maman Aysha
[9/9, 21:58] Amina Yakubu: πππKABEERππ
3⃣5⃣➖4⃣0⃣
Washe gari
Yau ko office na kasa fita haka na wuni jiki asanyaye saidai INA kokari boye rashin hankalin da nake ciki sbd kar mum ta damu.
5pm
Zuciyata tace take min zafi, abin duniya ya dameni kuka kawai nake sonyi gashi ba dama mun tana nan, kawai saina yanke hukuncin fita zaga gari ko naji sanyi a zuciyata. Shiryawa nayi cikin wata English gown yellow rigar ta hadu sosai wajen 25k aka sayeta nayi rolling da wani karamin yellow mayafi sanan NASA black shoe&bag na manna dark brown glass nayi kyau sosai, sanan na shirya su basma da junior muka fito nacewa mum zamu Dan fita zaga gari tace to sai kun dawo Amma karku Dade kinsa yau Excellency zai zo nace to, na kama hanunsu muka nufi motata. Direct rose flower sweet and bakery muka tafi, wani waje ne dayake tashe akano adon gari ne ya bude wajen, sbd shima time to time yana zuwa ya huta awajen, Amma fa wajen yayyan masu kudi ne domin kuwa idan kudin ka bekai 20k ba, baka isa ka shiga wajen ba. Wajen a zagaye yake da lafiyayyun flowers kala kala, shi yasa akasa masa suna rose flower sweet and bakery. Wajene daya tattara haddadun yan mata da samari, Amma fa yayyan masu kudi, kuma dama don yan mata da samari kawai adon gari ya bude wajen. Muna shiga naje nayi mana ordering ice cream, pizza da kuma shawarma wata kujera na samu muka zauna na budewa su junior ice cream din na basu suna sha suna wasan su. Shiru nayi inata kallon yan mata da samarinsu kowa yana harkar gabansa cikin farin ciki da annushuwa, Abin very interest, nan take na tuna irin mijin da zan aura tsoho me yayya goma, ina!! Bazai yiyyu ba wallahi ai idan kanaso ka mure rayuwar aure to ka auri yaro daidai dakai, Amma tsoho me zai Iya? Wasu zafafan hawaye ne suka fara yawo a kumatuna, kamar daga sama sainaji wasu yan mata sun hada baki wajen cewa waww!! ADON GARI, Kuma a lkc guda naga gabadaya hankalin yan matan wajen yayi gunsa harda wadanda suke tare da samarinsu, nima juyawa nayi domin na kashe kwarkwatar idona. Sanye yake cikin wasu shegun black jeans and shirt, a jikin shirt din an rubuta SMART GUY da red paint, sanan ya Dora red jacket akai gashin kansa ya kwanta yayi lub gwanin ban sha'awa, yasa red flat cover shoe me mugun tsada, idonsa a rufe yake da Dan karamin farin sun glass dauke yake da murmushi a fuskarsa da alama waya yake, kuma daga gani wacece yake wayar da ita tana da matukar muhimanci awajensa. Haka yazo ya wuce ta gabanmu da body guards dinsa guda 6 ya nufi wani special waje da akayi fencing da wasu shegun flowers kuma aka zuba lafiyayyun kujeru na hutawa aciki.dama sbd shi aka tanadi wajen. Daya daga cikin yan matan da suke gefena tace alhamdulilla yau kwana na biyar ina zuwa wajen nan sabd naga adon gari Amma ban ganshi ba sai yau, dayar tace ni kuma zuwa na uku kenan, dayar da aka kira da Rashida tace oh iska tana wahalar da me kayan kara Ku duba fa kuga duk kafe shi da idon da mukayi muna kallonsa shi besam ma munayi ba. Nima a zuciyata nace tabbas adon gari ya hadu ba karya, lkcn da mukayi fada dashi ganin tsoro nayi masa shi yasa ban kare masa kallo ba, inama yace yana sona, nan take na tuno da matsalar da take gabana ta auran tsoho bansan lkcn dana fara kuka ba, kifa kaina nayi akan table inata gurzar kuka.
Basma da junior kuwa suna ganin wucewar KB sai suka bi bayansa har cikin wajen suka farayi masa surutu, yaran sun burgeshi sosai besan lkcn daya beye musu ba sunata bashi dariya yace wa yazo daku nan sukace da auntynmu muka zo, yace OK, apple ya dauko ya basu sukai ta murna. Saida nayi kuka me isata harna gaji, na manta nazo da yara saida na duba inda suke wasa naga ban gansu ba, nan take na fara nemansu duk inda nake tunanin zasu na duba bangansu ba saida naje har bakin gate din shigowa Amma ba alamsrsu. A bangaren yaran kuma, KB zai tafi sai ya kamo hannunsu yace muje na rakaku wajen Aunty nku ni zan tafi gida, da suka nuna mishi inda na zauna sukaga bana nan ran KB ya baci kallon su yayi yace tuda auntynku ta gudu ta barku muje na kaiku gdna shikenan na sami yayya, zaku Bini sukace eh a tare, aikuwa yayi wajen motarsa dasu. Ni kuma a dawo daga bakin gate kenan cikin fargaba da tashin hankali kawai sainagano su suna shirin shiga motar, da sauri na tafi wajen Malam ya haka? Kawai daga ganin yara saika sasu a mota, Ashe suna wajenka, inata shan wahalar nemansu........Shut up marar tarbiya kawai, kin tafi yawon banza kin barsu, wa ya fada miki ana zuwa da yara nan wajen? Inaso ki Sani daga yau idan zaki fito yawon iskancin ki karki kara tahowa dasu, ki barsu agida. Kallonsa nayi da idona daya gama rinewa sanan nace ni ba yar iska bace, kuma idan har nasan yawon iskanci zanzo ai bazan tahoda yara ba, kuma idan da gaske iskanci ake awajen nan ai kafi kowa daukar zunubi tunda Kai ka bude wajen, nagode da kulawarka akan kannena. Wani irin kallo tsana ya bini dashi sanan yace stupid girl. Ban kara bi ta kansa ba na kama hannunsu muka tafi.
Maman Aysha
[9/10, 12:11] Amina Yakubu: πππKABEERππ
4⃣0⃣➖4⃣5⃣
8:15pm
Na idar da sallar isha'i ina zaune ina lazimi na jiyo muryar dad yana kwalla min kira da sauri na fita, ina zuwa yace kiyi masa ki shirya Excellency yana jiranki cikin fargaba nace to, haka kawai naji gabana yana faduwa. Dake ban cire hijabin da nayi salla ba takalmina kawai nasa na fice. Saida nayi addua sanan nayi sallam na shiga ya amsa yana bina da wani mayyatacen kallo. Dukusawa nayi na gaisheshi, sanan yace kamar yadda mahaifinki ya Sanar dani kun riga kun gama magna, so bana bukatar jin ra'ayinki akaina. Abinda ya kawoni shine inaso kiyi list din abubuwan da kk bukata na hidimar biki. Cikin tashin hankali na dago muka hada ido dashi kawai saina fashe da kuka lalle ka tabbata marar adalci, sbd da kana da adalci danka yakamata ka nemawa aurena bakaida kanka ba, kuma kai mutun ne me tsananin sonkai sbd baka damu da yanda rayuwata zata Kasan ce ba idan na auri tsoho irin ka, kai kawai burinka ka mallake ni, to wallahi inaso kasani bana sonka, bana kaunarka, kuma wallahi saidai akai gawata gdnka domin kuwa dana aureka gara na kashe kaina da gudu na fice na barshi a wajen ina kuka me tsanani, mum tana zaune a falo(dake yau dad a part din mama yake) na wuceta da gudu na shiga dakina, cikin tashin hankalin ta biyoni me ya faru Dota? Me yasameki kk wanan kukan haka? Mum wallahi bana son shi, wallahi idan na aureshi mutuwa zanyi. Zatayi mgana kenan naga ambanko kofar dakin da sauri dad ne cikin bacin ran da bantaba gani a fuskarsa ba yace Ku fito falo inason ganin ku . mum ta kama hannuna muka fita, muna zuwa muka sami mama da Zainab da samira a zaune, cikin kakkausar murya dad ya fara magna Aysha naji rashin kunyar da kikayiwa Excellency, kin nunawa duniya cewa ni ban isa dake ba. Tabbas bahaushe yayi gaskiya da yace tsintacciyar mage, bata mage, wanan Karin magana haka yake. Yau zan fada muku abinda Baku taba Sani ba, kawai sainaga mum ta mike a zabure ta durkusa ta rike kafafunsa tana wani irin kuka me tsanani don Allah alhaji kayi hakuri da fadar maganar nan, kayimin alkawari ba Wanda zaiji mgnar nan meyasa zaka fada yanzu? Wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata yimin shiru ko ban fada yanzu ba dama wataran dole maganar ta fito, cikin wata dakkyakiyar murya yace Aisha nace na'am inaso yau ki Sani bani na haifeki ba.....innalillahi was inna ilaihir rajuun juyawa nayi na kalli mum nace waye mahaifina? Kamar daga sama naji muryar dad yace itama ba ita ta haifeki ba nan take na fadi sumammiya da gudu aka sami ruwa aka yayyafamin sanan na farfado rungume mum nayi ina kuka me tsuma zuciya nace mum don Allah kice min ba gaskiya bane, don Allah kice ba gaskiya dad yake fada ba, batayi magana ba sai kuka da take me tsanani. Mutsitsika idona na farayi ya Allah kasa mafarki nake....muryar dad ce ta katseni da cewa ba mafarki kike ba dagaske ne bamu muka haifeki ba, wato abinda ya faru shine....
18yrs back
Nakai Jidda asibiti bada shirin haihuwa mukaje ba sbd cikin wata 7 ne, saidai muna zuwa da aka dubata sai akace haihuwa ce, haka na zauna inata addua har Allah ya sauketa lpy, da sauri nurse din tazo tace na kawo kayan baby, sai alokacun na tuna bamu dakko ba, sai nace Amma zanje na kawo yanzu tunda ba nisa sosai. Harna shiga mota zan tayar sai nurse din ta kara fitowa da sauri tacemin iam sorry to say babyn ta koma, saida ka debowa uwar kayanta jiki ba kwari nace to na tafi. Na wuce ta jkin wani gdn gona saina hango cincirindon mutane, sai nima na karasa wajen na tambayi me ya faru sukace wata mata ce ta sato jaririya, ta fada cewa wani Dan siyasa ne yasata ta sato masa yar, Amma bata karasa bayani ba ta mutun, nace INA yar aka miko min ke kinata shan hannu kina kuka, shine na roki yansanda da su barmin ke zan rikeki. Nan take mukaje police station aka bude miki file, suka bani takardu nayi signing aka kafa shedu, sanan na basu cikkaken address dina, na barki a hannun yan sandan na koma asibiti bayan ansallamo Jidda direct police station muka wuce, nayi mata bayanin komai sanan na damka amanarki a wajenta tare da alkawarin ba Wanda zaiji sai ranar auranki.
Wanan shine abinda ya faru kuma nayiwa Excellency bayanin komai yace ya yadda zai aureki a haka, Amma dake baki da mutunci, kuma ke ba gudar jinina bace kika ki bin umarni na, sbd haka inaso ki Sani daga yau bani bake, ki tattara komatsanki kibarmin gdna sbd ko yar Dana Haifa acikina bata isa ta kaucewa umarnina kuma naci gaba da zama da itaba, ballantana ke yar tsintuwa, sbd haka ki manta da kin taba sanin wani me kama dani arayuwarki, mun rabu dake har abada. Mum yace idan ka mata haka bakayi adalci ba, ina kake tunanin zata nufa yanzu? Ta tafi ko inama niba damuwata bace. Tabbas ba damuwarka bace sabda bakai ka haifeta ba, Amma inaso kasani ba ita kadai ka kora ba harni ka kora domin kuwa bazan taba zama agdn nan ba tare da Aysha ba.
Maman Aysha
[9/10, 15:15] Amina Yakubu: πππKABEERππ
4⃣5⃣➖5⃣0⃣
Mama ce tayi wata shewa aidama ance sannu sannu bata had a zuwa, nidama nasan komai Daren dadewa asiri zai tonu, an Dade ana nunawa yayyana banbaci agdnan akan ki Ashe ma yar cin arziki ce, Allah ya raka taki gona. Haka na mike na fara Jan kafata da kyar na shiga daki da tattara kayan da nasan zasu min amfani, na janyo katuwar troly na hayen idona ya kafe, Ashe idan mutun yana kuka da hawaye ma rahamane? Falon na dawo na durkusa agaban Abba nace ga mukullin motarka nagode da kulawar da kuka bani, kuma harna mutu bazan taba taba mantawa da abinda kukayimin na alkairi, nagode Allah ya saka muku da alkairi Allah ya biyaku da gdn aljanna. A dakire yace ki rike motar ai taki ce, jiki ba kwari na mike nace mum don Allah ki yafemin, nasan kinyi dawainiya dani irin wadda kowacce Uwa takewa danta,kinyi fama dani tun ina jaririya nagode Allah ya saka miki da mafificin alkairi, kuma insha Allah zanci gaba dayi miki addua irinta da da mahaifi harna koma ga mahallicina, nagode Allah ya kaddara saduwarmu. Jan trolley nayi nafara tfy, da sauri mum ta rike hannuna jirani nazo mu tafi Aysha, ai nima na gama zama a gdnan sbd yau alhaji ya tabbatar min da ya daina sona, tunda ya koreki banga amfanin cigaba da zama dashi ba, alhaji rubutamin takarda ta mu taffadAi idan kinga mun rabu saidai idan mutuwace ta raba, kuma in banda ke da abinki kin manta cewa ni na baki amanar Aisha, kuma yanzu na karba sbd haka yanda na koreta kema dole kiyi hakuri da ita barima ki gani, wayarsa ya dauko ya kira abbanta bayan sun gaisa ya fada masa duk abinda ya faru, shi kuma yace a bata wayar yana bata abbanta yace mijinki ya fadamin abinda yake faruwa, sbd haka kibi umarnin sa idan kika sake kika fita daga gdn bada izninsa ba, ban yafe miki ba kina jina ko? Cikin tsananin kuka tace eh, sanan dad ya kalleni yace you can go. Harna je bakin kofa mum ta kara kirana daki ta koma ta debo wasu kaya ta miko min, wanan sune kayan da suke jikinki lkcn da muka karfeki, wanan kuma zanin goyen ne, wanan kuma sarka tace lkcn dana saya 500k ce Amma yanzu nasan tafi haka ki sayar kiyi amfani da kudin. Inayi miki addua Allah ya takaita miki wahala, yayi gaggawar hadaki da iyayenki cikin dauko, Allah yayi miki albarka kawai ta juya daki da sauri, nima da gudu na bude motata na fita daga gdn.
AmmaTafiya nake Amma bansan inda na nufa ba, saida nayi tafiya me nisa har na Dan wuce BUK new side sanan na tsaya a gefen titi na kifa kaina akan sitayari na fara kuka, ban farga ba naga 10:45pm na kalli wajen da nake ko motsin mutane babu, elbash ne ya fadomin a rai kawai saina kirashi hlo beauty ya akayi? Kazo kan titin gwarzo road gaba da new side kadan ina wajen. Tuki yake kamar zai tashi sama sbd shi a bompai yake, akwai nisa a tsakaninsu Amma sabd gudun da yake sharawa, kuma ba yawan motoci sbd dare ya fara a 30minute yaje wajen acikin mota ya sameni beauty meya faru kika zo bayan gari kika zauna? Cikin kuka nace komai ma ya faru elbash su dad basu suka haifeni ba, bansan iyayena ba, ba wani mutun da zan nuna nace Dan Uwana ne, bansani ba ko iyayena suna dare ko babu dad ya koreni a gdnsa yanzu banida kowa aduniya kuka yaci karfina. Ya salam Aysha zaki Iya driving? nace eh, to shiga mubar wajen nan ki shiga gaba zan ringa binki a baya zoo road zamu kinji nace to.
Maman Aysha
[9/15, 11:22] Amina Yakubu: πππKABEERππ
5⃣0⃣➖5⃣5⃣
Tun a hanya ya sanar da Yaya bilal suna zuwa brodan Elbash ne Uwa daya uba daya. suna isa kofar gdn aka bude musu gate suka shiga da motocinsu matar Yaya bilal da faraarta ta karbe mu, sanan aka kaimin kayana guest room, elbash ya kira yayanshi gefe yayi masa bayanin komai sanan ya rokeshi alfarmar na zauna a gdnsa zuwa next WK idan amaryarsa ta tare sai na koma gdnsa. Ni kuwa tunda na shiga guest room din nake kuka Wanan wane irin rayuwa ce? Dad meyasa kayimin haka don Allah? Me yasa bakayi hakuri kaci gaba da zama dani ba why pliss? Kuka nake me tsanani kaina banda ciwo ba abinda yake elbash ne ya shigo dakin Aysha har yanzu baki dena kuka ba? Don Allah kiyi hakuri nasan kina cikin wani hali Amma ki sani akwai Allah, kuma shi yafi kowa sanin abinda yasa kika sami kanki acikin wanan halin, inaso ki mika al amuranki a wajen Allah, kuma kiyi tawwakali insha Allah zai zame miki alkairi, nima nabar aiki a pyramidTV, sbd ke dama na nemi aiki a wajen, so tunda yanzu bakyanan nima dole na tafi. Wato abinda ya faru kafin na fara aiki a pyramid TV ina daya daga cikin masoya kallon program dinki, kuma cikin lkc kadan naji na kamu da sonki kawai saina yiwa dad dina mgn inaso ya Samar min aiki a pyramid da yaki Amma dana matsa masa dole yaje ya sama min, ranar dana fara reporting na roki manaja daya hadani aiki dake sbd na sami saukin samun kanki, saidai Dan banzan kwarjininki ya hana nayi miki mgn, daga baya saina gane kinfi karfina sbd ke zubin matar manya ce irinsu adon gari, tun daga lkcn na canja son da nake miki da irin Wanda Yaya yakewa kawarsa, ina tsananin sonki beauty ina jinki tamkar ciki daya muka fito dake. Sbd haka don Allah ki dena cewa baki da kowa ni zan zame miki Uwa, uba, kuma broda in Allah ya yadda zan rikeki a bisa amana kuma zan temaka miki wajen nemo familynki. Na sami aiki a CBN kuma next WK ne daurin aurena Sbd haka zaki zauna anan gdn zuwa next WK idan amaryata ta tare saiki koma gdn, kuma munyi shawara da Yaya zan yiwa daddynmu mgn ya Samar miki aiki, Sbd kwanan zaa Debi maaikata, kuma dad dinmu ne chairman na civil service commission. Don Allah kiyi hakuri ki cinye jarabawar da Allah ya Dora miki kinji beauty nace to fita yayi ya kawomin yoghurt da pcm nasha sanan na kwanta ya rufemin kofar ya tafi.
[9/15, 15:40] Amina Yakubu: πππKABEERππ
5⃣5⃣➖6⃣0⃣
Haka naci gaba da rayuwa a gdn Yaya bilal, matarsa aunty Kulsum tanada kirki saidai na fahimce dana da kishi sosai, shiyasa nake kaffa kaffa saina tabbatar mijinta ya fita office sanan nake fitowa na tayata aiki, sanan yana dawowa nake komawa daki bazan fito ba sai baya gdn. Kullum elbash ya zuwa musha hira dashi yana Iya kokarinsa yaga ya Sani walwala da farin ciki, gabadaya lkcnsa ni yake bawa shi kullum burinsa ya ganni acikin walwala, yauma as usual elbash yazo muna ta hira sai aunty Kulsum tace gaskiya ina tausayin amaryarka elbash, me yasa kikace haka aunty na? Gani nayi kullum anan kake yini, ko irin Dan shirin nan da angwaye suke kai bakayi, dariya yayi yace su sadik abokina sun gama shirya komai, shiyasa na taho wajen yar kanwata ko beauty? Murmushin yake kawai nayi.
1 WK later
Yaune aka fara gudanar da bikin elbash, run da aka fara bikin ko waya elbash baya samun damar kira, aunty Kulsum ta bukaci da muje wajen bikin Amma naki sabd nasan staff din pyramid TV zasu, koma duk jama'a sun San abinda ya sameni, so banaso na hadu dasu, ba kunya tace min ni kuma banaso na tafi na barki da mijina a gd, Sbd gaskiya kinada fitinennan kyau idan na barku komai zai Iya faruwa shiyasa nake tsananin tausayawa amaryar elbash Sbd zata kunshi bakin ciki. Yanzu kiyi tunanin inda zaki ki zauna kafin na dawo, wasu zafafan hawaye ne suka zubomin nace bari naje gdn siyama kawata, idan kin dawo saikimin waya, to shikenan, ni na fara fita daga gdn sanan ta tafi gdn surunkanta inda ake gudanar da bikin
1wk later
Anyi biki angama lpy amarya ta tare a gdnsa dake ring road dad dinsa ne ya Gina masa gdn kyauta ya bashi. Ina daki a kwance ina aikin kuka naji muryarsa aunty Kulsum tana tsokanarsa ango kasha kamshi sai yau aka sami damar fitowa, haka dai suka gaisa ya shigo dakina ya salam beauty har yanzu baki dena kuka ba dauki mayafiki mu tafi shi ya dauki trolley din muka fito nayiwa aunty kulsum godiya muka tafi. boys qtrs din gdnsa ya bani ciki da falo da toilet ne gdn nasa yayi kayau sosai sabd zaikai 15 million shi kanshi ginin BQ din yayi kyau, kuma elbash ya gyara min duk wani Abu najin dadin rayuwa ya sakamin Sbd TV plasma me kyau ya saka. Bayan mun ajiye kayan yace akwai abinda kk bukata ko abinda be miki ba? Nace komai yayi nagode allah ya saka maka da gdn aljanna yayi murmushi yace amin, sanan yace mu shiga ciki yayi introducing dina awajen amarya tunda muka shiga naji gabana yana faduwa kujera ya nunamin yace na zauna ya kira ta nace to. Sun dade kafin su fito, harna fitar darai dasu sai gasu ta makale ajikinsa kaina yana sunkuye har suka karaso suka zauna ina dago kai muna hada ido naga ta mike cikin bscin rai tace Aysha Ahamad TURAKI itace yarinyar dakake fada cafdi ai wallahi bazai yiyyu ba gaskiya ban yadda ba idan sonta kake kawai ka aureta Amma ya zaayi na zauna da wanan kyakyawar yarinyar agida daya bayan ba muharramarka bace shut up Rahama ban kawo Aisha gdn nan ba saida kika amince, me yasa yanzu zakimin haka? Da zan aureta da ban aureki ba sabd na riga saninta kafin ke, na dauki Aysha ne tamkar blood sister na kuma bazan miki dole ba, idan har kince bazaki zauna da ita ba bazan takura miki ba ke matata ce kuma ina sonki so kinga Dole na baki hakkinki, Amma inaso kisani zuciyata bazata taba yafe miki ba domin kuwa kin hanani na aikata aiki na alkairi. Cikin kissa tace ba komai angona magna ta wuce na hakura Allah yasa haka shi yafi alkairi cikin farin ciki yace amin nagode, sanan yace don Allah inaso ki riketa a bisa amana kinga kin girme mata shekararki 22, ita kuma 18 so kinga a matsayin kanwa take a wajen ki Sbd haka don Allah ki rike amana saida tayi wani fari da ido sanan tace ba matsala sanan ya kalleni yace Aysha ki dauki rahama a matsayin yayarki kinji nace to zama tayi akan cinyarsa swit heart na hada maka zobon fa na dauko maka? Ina ganin haka na mike nace zan koma daki saida safe elbash yace tsaya kisha zobo mana nace na gode, na fita na koma daki saida nayi kuka me isata sanan nayi bacci. Washe gari bayan elbash ya fita wajen aiki aunty rahama tazo ta kirani nayi mata aiki haka na wuni ina aiki har girki ni nayi mata tana kwance. Haka rayuwata taci gaba agdn kullum wuni nake ina aiki saita dadaici ya kusa dawowa sanan tace na koma part dina aunty Kulsum matar Yaya bilal ta kara zugata tsana take nunamin a fili kwata kwata banajin dadin gdn, gashi elbash idan ya fita tun 7am sai 6pm yake dawowa. Gashi ta hana shi zuwa part dina, sbd tace idan ya kara shiga saita fadawa iyayensa ya kawo mata karuwa ya ajiye a gd, shiyasa yake lallaba ta yanzu mostly saidai muyi mgn dashi a waya, Amma duk da haka yana Iya kokarinsa yaga ya kyautata min.
2wks later
Elbash ya shigo da farin ciki yace albishirnki nace goro yace an daukeki aiki zaki ringa koyarwa a wata secondary sch a yankaba da murna na karbi offer nace nagd Allah ya saka da alkairi yace amin munde zakiyi reporting nace to.
Monday 8am
Na fito cikin shiri na shiga nayiwa aunty rahama sallama yauma as usual ta farfadi bakaken maganganunta Wanda idan da sabo na saba. Naje nayi reporting principal ya bani js3 da ss1 na ringa daukar su English, naji dadin kasancewa da yaran sosai, daga fara zuwana har mun saba dasu. Tunda na fara zuwa aiki na rage shiga damuwa sabd ko rahama ta bata min rai INA haduwa da students dina sainaji na manta.
3 months later
Na goge sosai da teaching malamai da students din sch din kowa sona yake na saba sosai da sch din. Yauma as usual yara sun fita break mu kuma muna staffroom muna ta hira dasu malama halima principal ya aiki a kirani ina zuwa naga fuskarshi a cikin damuwa saida yayimin nasiha sanan ya mikomin takarda a envelope yace daga ministry of education ne aka aiko ya bani sun sallame ni daga aiki sabd sunyi bincike sun gano ni ba yar asalin jahar Kano bace, saidai idan zanyi casual
Maman Aysha
[9/15, 18:48] Amina Yakubu: πππKABEERππ
6⃣0⃣➖6⃣5⃣
Innalillahi wa inna ilaihir rajuun kawai na Iya fada sana na karba dama da bag dina a hannuna sbd haka INA fitowa daga office din PC mota ta kawai na shiga na tafi gd, direct part dina nashiga na fara kuka kamar raina zai fita waye yayi min wanan abin? Waye yasan niba yar asalin Kano bace, kuma me natare mishi? Haka na wuni a kwance band aikin kuka ba abinda nake matar gdn ma batasan na dawo ba. Sai wajen 6:30 lkcn na tabbatar elbash ya dawo yaci abinci sanan na kirashi a waya ya najin muryata cikin kuka ya mike a zabure rahama ta Dora kanta a ciyarsa besam lkcn daya dauke ya tashi ba tana tambayarsa me ya faru ko takanta be bi ba ya nufi part dina yana zuwa yace meya faru naji kina kukan da kika Dade kinayi takardar na dauko na mika masa ya karfa ya karnta, shima salati ya saki, sanan yace bari ya kira dad dinsa yaji ko yasan Wanda ya fadamusu . aikuwa dad dinsa yace duputy governor ne ya dasu su rubuta sabd ba asan asalina ba, sai yace to dad ka dauke ta contract mana, bazaiyiyu ba elbash sabd ya kafa matakai akanta, ka bawa abokin naka hakuri, to shikenan dad nagode. Matsowa yayi ya kama hannuna kiyi hakuri beauty don Allah karki daga halinki akan wanan abin, nayi miki alkawari zan nema miki aiki a company, idan company ni ne bashida damar da zaisa a koreki kinji nace to, zanyi tafiya zuwa abj gobe kwana uku zanyi, idan na dawo zansan ya zaayi nace to nagd ban karasa maganar ba kuka yaci karfina kamani yayi ya Dora kaina a kafadarsa yana rarrashi na daidai nan rahama ta shigo da gudu tazo ta fisgoni ta hankadani na fadi ta fara balai aidama nasan dole haka saita faru wanan Dan bazan kyaun nata dole ya rudeka aikai ba waliyi bane ni gaskiya ka dauke ta daga gdn nan idan ba haka ba wallahi saina fadawa dad dinka abinda yake faruwa ta karasa mgnr cikin kuka. Kama hannunta yayi suka tafi part dinsu yanata aikin rarrashi dakyar ta hakura.
Washe gari
Da wuri ya shirya saida ya kara rokonta akan don Allah ta rike amanata kafin ya dawo, idan ya dawo zai daukeni daga gdn, ni kuma ya bani hakuri akan nacigaba da jure duk irin wulakancin da zatayi min kafin ya dawo nace to. Yayi mana sallama ya tafi aunty rahama harda kuka wai zatayi missing dinsa, da kyar ya lallabata yayi shiru sanan ya wuce.
10pm
Aunty rahama ce zaune a falo ita da wata cousin dinta hadiya suna zaune suna hira dake kawarta ce dama shiyasa ta kirata tayin kwana. Lbri take bata akaina ita tarasa yanda zatayi dani, kuma ga dukkan alama mijinta sona yake, Amma yanzu na bude wuta nace bazan zauna da ita ba yace idan ya dawo zai dauke ta daga gdn nan. Kaji shirme, aike dama sokuwa ce wani lkcn ina kike tunanin zai kaita idan ya dauke ta? Gida zaije ya kama mata suci karansu ba babbaka, kinga shikenan ya sami gdn Hutu. Nidai idan zaki bi shawarata muje ki koreta adaren nan idan ya dawo ya Tatar bata nan, kai kinaso ya bata min kenan, zai Iya sakina fa akan wanan yarinyar, dalla manta dashi tsakanin mace da miji sai Allah sai kiyi amfani da kissa ki mantar dashi, duk fadan da zaiyi kice bakisan lkcn data fita ba. Dariya tasa suka tafa wanan shawara tayi muje mu sameta. Ina kwance harna fara bacci sainaji muryarsu sama sama, na tashi na bude musu kofa suka shigo hadiya ce ta fara cewa lalle saken naki yayi yawa haka ya gyara mata daki kamar wata matar shi sanan rahama tace ke aysha inaso ki hada komatsanki a Daren nan kifar gdn nan idan kuma ba haka ba zanyiwa mahaifan elbash waya na fada musu ke karuwarsa ce ya kawo ki kike zaune, kuma nayi imani idan dad dinshi yaji saiya kusan tsine mishi, kuma dole kibar gdn Sbd haka ki zafi daya ko ki tafi batare da kin jawo masa fishin iyayensa ba, ko kuma suzo su koreki a wulakance cikin shesshekar kuka nace karki fada musu zan tafi, mikewa nayi na tattara kayana na fice muna tafe tare har mukazo inda zamu rabu, sanan nace don Allah ina Neman alfarma kiyi hakuri nabar motata anan sabd bana Iya long journey da mota, idan kk bar mota nayi aikin banza kenan, Sbd zaki dawo daukar motarki wata ran. Karki damu koda nazo bazan cigaba da zama daku ba, kuma nayi miki alkawari bazan taba fadawa mijinki ke kika Koran ba, nagode da zaman da mukayi dani,kuma don Allah ki yafe min sabd kin shiga tashin hankali a dalilna. Naja trolley na na fice daga gdn, garin yayi duhu banda kukan karnuka ba abinda ake ji ga hadari ya hado sai walkiya ake, tafiya nake Amma bansan Inda zan dosa ba addua nake Allah ya dauki raina na huta Sbd rayuwata bata da sauran amfani ni bakowa bace face annoba, Yessss annoba ce ni sabd duk inda naje guduna ake nayi zurfi a tunani har nahau kan titi ban Sani ba.
Da gudu yake tafiya ya dawo daga wajen meeting, da motoci guda biyu kawai ya fita shi yake tuka motar da Kansa, dayar kuma body guards dinsa ne aciki be Ankara ba kawai yaji ya bige mutun cikin tsananin tashin hankalin ya fito ya dauke ta da gudu yasa a mota suka nufi asibiti
Maman Aysha
[9/17, 20:34] Amina Yakubu: πππKABEERππ
6⃣5⃣➖7⃣0⃣
Gudu yake kamar zai tashi sama, tun kafin ya kara ya sanar da family doctor nsu abinda ya faru, direct asibitin ya nufa, kafin ya karaso nurse din ta hada emergency bed, suna zuwa ya dauko ta da gudu ya shiga ciki, da sauri nurses suka karbeta suka Dora ta akan gadon, vital sign aka fara dauka sanan sukayi elevating bed din aka samata oxygen, akayi setting din cannula aka samata dextrose saline Sbd likita yace hypoglycemia ne, sun dauki blood sample na pcv da blood group, sanan akayi mata wasu allurai. Duk bayan 15 minute ake Chekiang vital sign din har suka dawo normal, pcv din nata da aka duba 28% sai doctor yace basai an kara jini ba. Duk wani emergency care an bata saidai har yanzu bata farfado ba cikin tashin hankali Mr kabeer yace don Allah Dr Abdul ka temakeni kar yarinyar nan ta mutu plisss, yace karka damu nayi mata scanning ko tasamu internal injury, Amma naga every thing is Norma so karka damu insha Allah zata farfado. Kallon guards dinsa yayi yace ina ganin Ku tafi gd ni anan zan kwana, daya daga cikin su me suna rabiu yace haba yallabai kai ka tafi ka huta ni saina kwana da ita, ba matsala rabiu kuje kawai Sbd idan na koma ma fargaba bazata barni nayi bacci ba, to shikenan yallabai saida safe Allah ya kara rufa asiri yace amin.
Dakin da aka kwantar ta special room ne gado guda daya ne a dakin, sai kujera 3 siter, sai TV plasma da reciever sai kuma karamin fridge. Motarsa ya koma yasa wasu substaff maza suka goge jinin daya zuba akayi dis infecting wajen da sprit, sanan ya bude boot din motarsa ya dauko sabuwar jallabiya fara Sol ya koma dakin da Aysha take ya shiga ya rufe da key sanan ya shiga toilet ya cire suit din jikinshi yayi wanka, dake toilet din is very neet, sanan ya saka jallabiyar, ya fito ya kunna A/c dakin, ya kwanta akan kujera. Juyawa yayi ya kalli gadon da take sai yaji yanaso yaga fuskarta Sbd acikin duhu ya kadeta, kuma tunda suka shigo asibitin be kalleta ba. A hankali ya karasa bakin gadon yana dubawa ya ganta .amaki ya kamashi a knli ya furta Aisha Ahamad TURAKI ita na buge dama? To ina zata da tsohon Daren nan? Kuma ina motarta ta fito a kafa? Fuskarta ya zubawa ido yana kallo, a zuciyarsa yace tana da kyau sai rashin kunya, tsaki yayi ya koma ya kwanta.
Washe gari
Da asuba ya tashi yayi sallah, yayi addua sosai akan Allah ya bata lpy. Har nurse din ta shigo medication bata farka ba. Wajen 8:30am doctor ya shigo ya kara dubata yayi mata RBS yaga ya dawo normal, cikin damuwa Mr kabeer yace yanzu ya zanyi doctor karka damu any time zata Iya farfadowa. To shikenan Allah ya temakeni ma nasan iyayenta bari na kirasu na sanar dasu abinda yake faruwa, Dr Abdul yace OK, bari. naje office yace to. Wayarsa ya dauko ya fara dialing bayan anyi picking ya gaishe shi cikin girmamawa sanan ya fara masa bayanin abinda ya faru, saida ya bari ya gama sanan yace OK indai magnar Aysha kake to ba yata bace amma ni na riketa tun tana jaririya, kuma yanzu na koreta Sbd kin bin umarnina da tayi, kuma ni yau Kasan wata hudu kenan ban sata a idona ba. Idan kaga zaka temaka mata to, idan kaga bazaka temaka mata ba shikenan, nidai bani ba ita. Besan lkcn daya kashe wayar ba sabd tsananin mamaki ya kara maimaita mgnr a zuciyarsa bashi ya haifeta ba? Taki bin umarninsa? Kuma bashi ba ita? To meke faruwa da Aysha ne? Matsawa jikin gadon yayi har yanzu tana nan a yadda ya barta nan take yaji tausayinta ya kamashi
Maman Aysha
[9/18, 12:50] Amina Yakubu: πππKABEERππ
7⃣0⃣➖7⃣5⃣
Ya Dade yana kallonta , sanan ya fita zuwa office din Dr Abdul, doctor inaso naje gd nayi wanka, so don Allah wa zaka bani ya zauna da ita kafin na dawo? Zan yiwa nurse luba magna, to shikenan, cikin muryar damuwa yace amma Doctor ina tsoron kar wani Abu ya sameta, tun jiya fa rabonta da abinci, ai da tausayi. Dariya doctor yayi, Mr kabeer ko itace amaryar tamu ne? Naga ka damu da yarinyar sosai, aa wallahi kawai dai INA tausayinta ne, to karka damu zata dawo normal very soon, is alright bari naje na dawo, to shikenan saika dawo. Diriver shi ya aika gdn mum dinshi aka karbo masa break fast yayi wanka yaci abinci sanan ya Dan kwanta sabd jiya beyi baccin kirki ba, duk bayan yan mintuna yana kiran Dr Abdul yaji ko ta farfado, amma har yanzu shiru.
6 hours later
Zaune yake office din doctor cikin tsananin tashin hakli yake cewa Dr Abdul karfa yarinyar nan ta mutu baka sani ba, ace mutun tun jiya har yanzu fata farfado ba? Kafin yayi mgn phone dinsa ta fara kuka yana picking yace ta farfado? alhamdulilla muje Mr kabeer patient dinka ta farfado, da sauri suka shiga dakin likita ya karayi min wasu allurai, sanan yace a bani abinci naci nidai binsu kawai nake da kallo adon gari kawai na gane acikin su to me me yasa aka kawoni nan? Me yahadanida adon gari? Nan take brain dina ta karantomin abubuwan da suka faru, bansan lkcn da nasaki wani irin kuka ba adon gari ne ya kama hannuna ya rakani toilet, ya bani sabon brush da MacLean nayi brush, sanan ya had amin ruwa ya fita nayi wanka, kafin na fito naga ya ajiyemin lotion da perfume da kuma wata shegir bul gown blue damayafinta ya fice, shafa man nayi sanan na dauki rigar nasa na fesa turare. Saida jikin sa ya bashi na gama shirya wa sanan ya shigo dakin dauke da yan ubansun food wormers ya dauki plates ya zubamin abincin da kansa yace na karba naci mamaki ne da kuma tambayoyi fal cikin zuciyata, saidai bazan Iya tambaya ba. Hadadden abinci ne Amma inayin loma biyu naji bazan Iya Ciba kawai sauna ajiye plate din wani irin kallo ya watsa min da bazan Iya fassara abinda yake nufi ba, sanan cikin wata unique voice dinsa yace ko bazaki Iya ci ba nazo na baki? Ya salam kawai na furta a zuciyata, wanan golden voice dinfa kodan mostly idan mun hadu da fada muke rabuwa shiyasa bansan voice dinsa ba, can't you answer me? Naji daddadar muryar shi ta daki kunnena, bani da apatite ne na bashi amsa a kasalance, OK Amma da kin daure kinci ko kadan ne, Sbd kusan 24hours kenan bakici komai ba, idan kuma akwai abinda kike sha'awa ki fada na sayo miki yanzu, nace ba komai nagode.
2 hours later
Tare suka shigo shida Dr Abdul da Suleiman PA doctor ya kalleni yace ya jikin? Da sauki, Allah ya kara sauki nace amin, na sallame ki zaku tafi gd yanzu akwai drugs din Dana rubuta zai baki ki tabbatar kina sha kinji ko nace to, shikenan yallabai zaku Iya tafiya to nagode doctor, zaki Iya tashi ko na taimaka miki? Zan Iya, to saukko muje ina fara tgy naji jiri yana kwasata, na tafi zan fadi da gudu ya rikeni aidama nasan bazaki Iya ba shiyasa na tambayeki, tallafoni yayi muka karasa har bakin mota ya bude min na shiga sanan ya zagaya ta daya bangaran ya zauna Suleiman PA ya zauna a gaba, driver ya tashi motar muka fita daga asibitin gabana banda faduwa ba abinda yake, Sbd ina tsoro kar ya maida ni gida phone dinsa ce ta fara kuka yana dauka yace hlo Yaya Salma kin wuni lpy? Lpy kalau Broz, ga babynka ta dameni da rigima wai yau tru out baka kirata ba, ayya bani ita hlo my baby stop crying, ko kinaso nima nayi kuka? Aa na daina, yauwa gud girl, to uncle yaushe zakazo very soon zaka sayomin ice cream? Har chocolate zan kawo miki, thanks uncle bazan kara kuka ba yawwa gud girl saina zo bawa mamanki, hlo my sis nayi missing dinku da yawa wallahi may na shigo abj next WK, I miss you too Broz, OK saika zo dama inason ganin ka nayi maka budurwa idan kazo mayi mgnr, wata yar iskar dariya yayi yace gud nyt. Driver ne ya juyo yace yallabai ina zamu? Kaimu gd, muna zuwa ya matsa remote katon gate din ya bude muka shiga, shi ya temaka min muka shiga har cikin gdn fadar kyau da tsarayuwar gdn bazai yiyyu anan ba, nidai nace Allah ya yi mana arziki na halal. Wani daki ya shiga dani na zauna a bakin gado sanan ya kalleni me kike shawa akawo miki kici? Nayi shiru, Aysha dake nake magana fa wayyo Allah nace a zuciyata mutumin nan yana Neman kashe ni da unique voice dinsa Ashe wasu irin qualities yake dauke dasu shiyasa yan mata suke manne masa? Can't you answer me? A firgice nace ice cream, wani shu'umin kallo ya watsamin ice cream abinci ne? Mostly idan nasha da cake shikenan ba saina ci abinci ba, fita yayi ya kawo min da cake din ya fice, nima ina gama saha na kwanta
Maman Aysha
[9/18, 14:31] Amina Yakubu: πππKABEERππ
7⃣5⃣➖8⃣0⃣
Ban farka ba sai asuba, ina tashi nayi alwala nayi sallah dake yasa an shigo min da trolley na saina bude na dauko alkur'ani na fara karatu daga yussabihu zuwa kasa, a massalacin gdnsa yayi sallah dake akwai liman yana biyansa duk wata so har makotan gdnsa ma suna zuwa sallah massalacin. Yana shiga falon yaji kira'arta me dadin gaske tana tashi kawai saiya samu waje a falon ya zauna yana bin surar da take a hankali dake shima ya sauke. Haka yaita bin duk surar da take karantawa har saida nakai suratul nazi'at, kawai sai kuka yaci karfina nan take na fara addua ya Allah kafi kowa sanin halin da nake ciki bani D's kowa, Allah kafi kowa sanin ba wani mutun da zan Iya nunawa a matsayin Dan Uwana na jini, ya Allah ka Sani tunda nazo duniya banji dimin da yakeji agun mahaifiyarsa ba, idan har iyayena sunada rai ya Allah kai gaggawar hadani dasu, idan kuma basa raye kayi gaggwar daukar raina na bisu inda suka tafi kuka sosai nake da har nakasa control din kaina. Ji nayi an rukoni, ina daugowa muka hada ido dashi Aysha me yasameki? Ko jikin ne? Nace aa, to fadamin me ya faru? Nace ba komai are you sure ba abinda yake damunki nace eh, to karna kara jin kukanki kinji? Nace to. Yana fita naje nayi wanka nasa wasu Riga da siket na atamfa, pink and white ne kalar atamfar saina dauki hijabi pink nasa, na dauki hand bag dina daya hannun kuma naja trolley din na fice daga dakin a falo na sameshi ya zabga uban tagumi nace ni zanje na tafi, nagode da temakon da kayimin Allah ya saka maka da gdn aljanna. Harna juya na fara tafy naji yace Aysha tsaya, cak na tsaya ba tare da najuyo ba wane irin sauri kike zaki tafi baki karya ba? Daga tafiya na dawo ne ko gd banje ba ka bugeni, so nasan yanzu hankalin yan gdnmu dole a tashe yake, yess I see, hanklinsu yana tashe Amma ko media basu bada cikiyarki ba yau kwana biyu? Zo ki zauna akwai mgnr da nake so dake, banyi musu ba naje na zauna, sanan ya dubeni yace baki mamaki ba dana taho dake gdn, instead of na wuce dake gdnku? Yaci gaba da magana washegarin ranar da abin ya faru na kira dad dinki nayi mishi bayanin cewa na bugeki da mota kina asibiti unconsciousness, me makon ya tausaya yanda kowanne uba yakewa dansa idan Abu ya faru, saiya jefeni da wasu maganganu da nake son jin amsarsu daga gareki, Aysha zan tambayeki bana son kimin karya, Sbd ba mutumin dana tsana irin munafiki, makaryaci da kuma me cin amana, so pliss I want you to tell me d truth. Tambayata ta farko wane irin umarni dad dinki ya baki kika ki yi? Yace rabonsa dake kusan wata hudu kenan, a gdn wa kike bayan kin bar gdnsa? Sanan daga ina kike lokcn dana kadeki? Cikin nutsuwa na fara bashi lbri tun daga ranar da deputy governor yace yana sona, korata da daddy yayi, zama agdn elbash aikin dana fara da kuma korata da matar elbash tayi Wanda shine sanadiyar fitowata harka kade ni. Saida ya zubda hawaye don tausayi sanan yace kin tabbata lbrn da kika fadamin gasky ne? Nace eh, yace to karki damu naji duk adduar da kikayi dazu bazan boye miki ba da natsaneki Sbd rashin kunyar da ki kayimin, da kuma tozartani da kikayi a media, Amma yanzu na hakura kuma zan temaka miki, zan baki daya daga cikin gdajena ki zauna, zan nemo miki wata tsohuwa data tafa aiki a gdnmu mutuniyar kirki ce Ku zauna tare, sanan zan daukeki aiki a matsayin sakatariya ta, Amma inaso ki tsare mutuncin kanki. Insha Allah zanyi nagode Allah ya saka da alkairi, amin, idan yaso Monday saiki fara fita
Maman Aysha
[10/14, 9:52 PM] Chopy: [9/20, 10:13] Amina Yakubu: πππKABEERππ
8⃣0⃣➖8⃣5⃣
A ranar yaje gwamai ya dauko baba mero, ya direct gdn daya bamu mu zauna a lamido crecent ya wuce da ita ya sami almajirai suka tayata gyarn gdn, sanan yaje mall dinshi ya iyo mana provision, duk wani Abu da Kasan ana bukata a gd adon gari ya sayo mana, har detergents saida ya siyo, ya sayo mana gas cooker da cylinder saida ya tabbatar komai yayi normal sanan ya dawo gd. Ni kuwa tunda ya fita nake bacci ban farka ba sai after 3 toilet na shiga nayi wanka nayi alwala INA sallah naji motsin shigowarsa, bayan na idar nayi addua saina fita a dinning na same shi har yayi wanka yasa wasu shegun blue shirt da black jeans saida na Dan rusuna nace ina wuni? Ba tare daya kalleni ba yace lpy INA gajiya, ya jikin? Nace da sauki hankalinsa gabadaya akan phone dinsa yake, shiyasa na sami damar kare masa kallo wato bayan fitinanan kyaun da yake dashi, yana dauke da wani sirri da saika Tara maza dari baka sami guda daya me irinsa ba, in fact kyaun shi is very unique......ke meye kika zuba min ido kina kallona ina ta mgn ba responding? Kunya ce ta kamani na rasa me zance masa, bismilla zo kici abinci nace to a kujerar gefensa na zauna, tunda na zuba abinci bancin banci yakai 3 spoon ba sai wasa da spoon din kawai da nake Sbd tsananin kwarjini da kuma kunyarsa da nake ji, inajin ko ganewa yayi sainaji yace koma daki tunda ba zaki Iya ci a gabana ba, aikuwa da sauri na mike ina tafiya kmr wacce kwai ya fashewa a ciki na shiga daki naci, bayan na gama na shiga kitchen zan wanke plate din yace na bari me aikinsa zai wanke, dake duk masu aikin gdnsa mazane. Ina zaune ina kallo a laptop dina ya shigo dakin ni xan fita, sbd inada meeting yanzu. kamar yadda na fada miki na dauko baba meron tanacan a gdn so ki hada kayanki nayiwa bala driver mgn zai kaiki karbi wanan ya miko min wrappers din 1000 guda biyu, Ku biya ta boutique ki sayi kayan da zaki ringa zuwa office dasu, dakai food items gdn idan da akwai abinda babu kayimin magana, ina phone dinki nasa miki no na, phone dina a kashe take Sbd inaso na canja layi saidai na rubuta a paper. Be quick da Allah sauri nake da hanzari na dauko yana fadamin harna rubuta, sanan yace 9am nake fita office, so iam expecting you b4 nine kuma bana son late coming be jira abinda zance ba kawai ya fice daga dakin wata sansanyar ajiyar zuciya na saki dole kayi abinda yafi haka ma, Sbd Allah ya baka duk wani Abu da Dan Adam yake bukata a duniya, ba abinda ka nema karasa gabadaya voice dinsa ta tafi dani, Sbd gashi dai da harshen Hausa yake min magana, amma yanayin yanda yake pronouncing kowacce kalma saika rantse ba Hausa yake ba. Me karatu kar kuga kamar na zake da yawa, wallahi adon gari ya hadu ne sosai, is not my fault yanada fitenannan kyau ne, kuma ga class shiyasa
Maman Aysha
[9/20, 16:34] Amina Yakubu: πππKABEERππ
8⃣5⃣➖9⃣0⃣
Ta wani B classic boutique nabi na sayi kaya masu kyau, Amma gown sunfi yawa aciki na debo haddadun shoe & bag sanan muka wuce lamido crescent inda sabon gdn yake. Muna zuwa me gadi ya bude mana gate muka shiga, gida flat house ne me kyau anyi interlocking gdn gabadaya, kuma yanada packing space da zaa Iya ajiye motoci 4, Dan madaidaicin falo ne dauke da arch guda biyu, na bangaran gabas dauke yake da corrido sai dakuna guda biyu suna kallon juna da toilet a tsakiya, na bangaran yamma, kuma one bed room ne da toilet aciki da alama a matsayin master room akayi bangaren arewa kuma dinning area ne da kuma kofar ketchen gdn yayi kyau sosai, ga unguwar very silent ba hayaniya.
Wasu yan madaidaitan kujeru yasa lemon green, so komai na falon lemon green ne, sanan gabadaya 3 bed room din ya zuba furniture's aciki, da alama bakinsa da yake saukarwa da agdn. Malam bala da baba megadi ne suka shigamin da kayana ciki, dakin da yake a matsayin master room na zaba a matsayin dakina, kuma baba mero ta tareni da faraarta.
2 days later(7:45pm)
Zaune muke muna rangada hira nida baba mero sbda matar tanada tsananin kirki ga barkwanci duk lkcn da muka zauna saita bani dariya, yau kwana biyu kenan da fara zamanmu amma kamar mun shekara da ita. Tana bani wani lbri inata dariya ya shigo gdn yanata sallama bamuji ba, har saida ya shigo cikin falon wata night gown ce me laushi a jikina, doguwa ce har kasa kaina ba dankwali saida na raba gashin gida biyu na tuke su sun kwanta a gadon bayana. Fuskarsa ba yabo ba fallasa saida na rusuna na gaishe shi sanan yace kinsan gb zaki fara fita ko nace eh, to abinda ya kawoni na manta ban fada miki address din wajen ba, Sbd state government ta karfi hayar BAGAUDA house, na koma kamfanina na club road, nace to, kinsan wajen ne? Eh mun taba zuwa Neman ka wajen daga office din mu OK to nan zaki goben har yanzu baki sayi sim card din? Nace aa, ga wani saiki yi amfani dashi Sbd da kinada waya da bansha wahala nazo ba, juyawa yayi yace baba mero ya gdn ba matsala dai ko? Tace wallahi ba komai, don Allah dama inaso na fada miki karki bari mum dina tasan kuna nan, sanan don Allah ki kula da Aisha sosai kamar yadda zaki kula da yarki, ki dauke ta a matsayin ya kuma ki kula da tarbiyar ta don na fuskanci kanta yana rawa. Ke kuma Aysha inaso ki dauki baba mero a matsayin Uwa, kuma kiyi mata biyayya banason rashin kunya kinji ko don nasan baki da kunya. So ni zan tafi saida safe muka amsa da Allah ya kaimu. Baba mero ce tace ke Aisha haka ake bazaki tashi ki rakashi ba, dariya nayi nace ni awa zan rakashi? Tab kinaso ya wulakantani kenan, wane irin wulakanci? Ba saurayinki bane? Aa wallahi ba abinda yake tsakanina dashi tausayi na kawai yake , to ai saida so ake samun tausayi, aa baba mero kibar wanan maganar, yaga ina bukatar taimako ne kawai, saiya temaka min zanje nayi sallah na kwanta gobe tashin wuri zanyi
[9/20, 20:02] Amina Yakubu: πππKABEERππ
9⃣0⃣➖9⃣5⃣
A bangaren elbash kuwa yana dawowa gd ya sami aunty rahama tana jiki duk a sanyaye, yace rahama me yake faruwa naga kamar baki da lpy, dariyar yake tayi sanan tace kalau nake, muje kayi wanka kaci abinci yace to, a daddafe yayi wankan Sbd gabadaya hankalinsa yana gun Aysha ya matsu yaje yaga halinda da take ciki, tunda ya isa abuja yake Neman ta a waya be sameta ba, kuma ya kasa tambayar rahama Sbd kar ranta ya baci. Harta jire masa abinci akan dining zai fara ci kenan saiyaga bazai Iya cin abinci ba tare daya ganta ba, kawai saiya mike rahama INA zuwa bari na duba Aysha don Allah, nan take ta saki kukan munafirci Aysha fa yau kwananta uku rabonta da gdn nan, nayi duk Iya kokarina naga na nemeta Amma na rasa, kuma ba Wanda yasan lokcn data fita da naga motarta tana nan nayi zaton itama tana ciki, saida na duba dakin naga wayam. Tunda ta fara mgn yake salati, daga karshe kawai saiya fashe da kuka idan ma guduwa Aysha tayi to kece sila, jikina yana bani abin kikayi mata ya bata mata rai harta bar gdn. Me yasa rahama? Meyasa kika fiye son kanki da yawa? Me yasa kika bar zuciyrki ta bushe kika zama marar imanin da kika kasa tallafawa rayurwarta? Bata da kowa fa, kuma ni kadai ta aminta dashi a garin nan yanzu wa yasan inda ta tafi? Why pliss itama kuka take sosai tabbas ni nayi silar tafiyarta, Amma wallahi nayi regretting don Allah kayi hakuri ina masifar sonka kishi ne yasa na aikata don Allah ka yafemin zama tayi tana rasgar kuka kana kallon ta zaka San tayi nadama, kamota yayi ya rungemeta ajikinsa yace shikenan daina kuka Allah yasa ta fada hannun nagari, kuma Allah yasa haka shine mafi alkairi a gareta rahama tace amin.
Yau kwana na biyu kenan da fara fita aiki, kuma ba wata matsala inayin aikina succefully, ya kafa matakan tsaro sosai, Sbd sai an tsallake office hudu sanan azo nawa, office na farko screening din mutun ake a tabbatar baya dauke da makami, harmu sttaf din wajen akewa, office na biyu kuma body guards dinsa ne suke zama physically suke checking din mutun, idan basu yadda da mutun ba tunda daga nan suke korarsa, sai office na uku kuma anan ake duba sunan mutun aga idan da sunansa acikin list din Wanda zai gani a ranar, office dina ne na karshe ni kuma duk Wanda yazo zan mishi waya na fada masa idan ya amince saiya shiga.
Zaune yake a office yana signing wasu files kawai sai wayrsa ta fara ruri yana dubawa yaga deputy governor ne yace yallabai ka wuni lpy? Lpy kalau, Aysha Ahamad TURAKI ta dawo company ka da aiki, Sbd haka inaso ka kureta yanzu nan, to yallabai tayi wani lefin ne? Umarni nake baka, baka da right din da zaka Sani na koreta yallabai Sbd kamfanina ba a karkashin gwamnati yake ba idan zan koreta ni zanyi raayi da kaina ba wani ne zai Sani ba, kuma yarinyar tana tsananin bukatar taimako banga abinda zaisa a koreta ba. Idan maganar da nayi ta bata maka rai kayi hakuri bissalam. Yana katse kiran ya fara dialing no me girma governor yayi na farko baa dauka ba, yana kara dialing aka dauka governor yana tsananin son adon gari Sbd aminin babansa ne, kuma yanada amana. Bayan sun gaisa ya bashi lbrn abinda ya faru tsakaninsa da duputy, yace to ba matsala kazo around 8pm sai muyi mgn, yace to Abba nagode
Maman Aysha
[10/14, 9:52 PM] Chopy: [9/21, 16:33] Amina Yakubu: πππKABEERππ
⃣9⃣5⃣➖1⃣0⃣0⃣
Yaje ya sami governor yayi masa bayanin komai a tsunake, me girma governor ya tausayamin sosai, kuma yayi masa alkawari zai dauki kwakwaran mataki akan shi. Adon gari na fita daga government house me girma governor ya kira deputy da chairman din partynsu, da kuma wasu mutun biyu masu fada aji a party din sunyi mishi warning sosai akan ya fita harkata, kuma sun fada mishi duk abinda ya sameni y kuka da Kansa, ya bada hakuri kuma yayi alkawari bazai kara ba.
Yauma as usual ina office banda aikin tunanai ba abinda nake, maganar da mukayi da baba mero ce ta dawo min kodai da gaske adon gari sona yake? Sbd caring Da yake nunamin yayi yawa, kuma naga baya shiga harkar yan mata aikuwa idan da gaske adon gari yana sona nafi kowa saa wani lallausan murmushi nayi, sai wata zuciyar tace min kinga Aysha kar ki zake da yawa tausayin ki kawai yake mutumin daya hada duk wasu qualities da ake nema ajikin da namiji me zaiyi da marar asali irinki. Nan take na dawo hayyacina tabbas gaskiya zuciyata ta fadamin, elbash ne ya fadomin a rai Allah sarki ko ya yaji da yazo ya tarar bananan? Phone dina na dauko na fara dialing no dake sabuwar no ce harta katse be dauka ba, saida na sake dialing ya dauka yana jin muryata yace Aysha INA kika shiga INA ta nemanki? Kina Kano ne, ko kin tafi wani garin? Kuma a gdn wa kike yanzu ko kin sami parents dinki ne? Mikewa nayi na tafi ta wajen window na fara bashi lbrn abinda ya faru tunda ga ranar da nabar gdnsa har zuwa yanzu. Kina nufin kina kano? Eh OK to zanzo na sameki a office din gobe nace to shikenan, awaiting call ne ya shigo phone dina har three missed call INA dubawa naga Mr kabeer da sauri na dauka, shigo office dina yanzu nace to, INA shiga naga wasu mata guda biyu dayar sanye take da uniform din yansanda, dayar kuma kana ganin ta zakasan gayu ya ratsa ta, suna tsaye abakin kofa kafin nayi magana yace da wane Dan iskan kike waya har wadanan useless din suka shigo min office batare da naba da izini ba? Rasa amsar da zan bashi nayi Sbd bansan lkcn da suka zo suka wuce ba. Kallon su yayi yace ke nazlee Kike kowa, inaso kisani bana sonki, har abada bazan taba sonki ba, kuma wallahi na kara ganin kafarki a wajena saina saba miki, kuka ta fara haba adon gari don Allah, meyasa kake wulakantani Allah ne ya jarafceni da sonka ka tausaya min mana, cikin tsawa yace nace ki fice min daga office ko sai nasa anfitamin dake, da gudu tafice tana kuka woman police din da suka shigo tare ta bita da sauri. Ba tare da ya dago ya kalleni ba yace ke kuma baki amsa min tambayata ba? Voice dina tana rawa nace uhmm....elbash ne, aiki kika fito yi ko soyayya? Wallahi ba saurayi......dalla yimin shiru be shafeni ba idan ma sonki yake, nidai abinda nakeso ki gane shine karki ga na baki na baki gd, kuma INA nuna miki caring kiyi tunanin ko kinada wani matsayi ne a wajena, your nothing tausayin ki kawai nake, so duk abinda nake miki sadakatur jariya nake Sbd haka ki dauki kanki a matsayin ke ba kowa bace face staff dina, matsayin ki dayane da duk wani ma'aikaci dayake aiki a karkashina, kuma wallahi idan kika kara barin wani ya shigo bada izinina ba sainayi punishing dinki, idan zakiyi soyyayar ki bari idan kin koma gd kyayi, I hope you get me right? Tunda ya fara fadansa nake kuka, dakyar na Iya ce masa eh, sanan yace fita ki bani waje na juya na fice jiki ba kwari. Kujerata na koma na Dora kaina akan table inata aikin kuka saida nayi me isata sanan na shiga toilet na wanke fuskata INA fitowa naga wani had some saurayi a tsaye kana ganinsa kasan he is smart muna hada ido yace min kabeer yana nan kuwa? Nace eh wa zaa ce masa? Kice marwan ne, OK phone din da na saba kiransa da ita na dauka na fara dialing yana dauka na fada masa yace ya shiga, juyawa nayi nace yace ka shiga wani mayen kalau ya bini dashi, sanan ya wuce. Yana shiga yace adon gari kana sha'aninka, a ina ka sami wanan beautyn? kuma dan iskanci ka barta a matsayin sakatariyarka is she not a graduate? Graduate ce mana, mafioso tayi aiki a kusa dani ne, tayi aiki a kusa dakai kana sonta ne? Ba wani so inaso na kare mutuncinta ne, Sbd idan tana kusa dani zansan duk wani move dinta. To tunda baka sonta ni ina ciki sabd gaskiya she is beautiful kuma tanada class Kasan harna gama tsayuwa ta a wajen bata naga kai ta kalleni ba, saidai is lyk kamar tayi kuka naga Golden eyes dinta sun Dan kumbura, ko Kai ka bata mata rai? Bansan ba, Kasan bana son surutu da yawa don Allah ka fadi abinda ya kawo ka, OK zuwa nayi mu tafi gdn kaci abinci, nasa anyi maka favourite dinka, kamar Kasan yunwa nakeji kuwa, bari na fadawa mum karta aikomin da abinci yau. Tare suka fito suna hirarsu suna dariya ni zantafi ki rufe office din ki tafi, nace to, marwan ne yayi min wani lallausan murmushi yace bye Aysha, nace OK bye.
Maman Aysha
[9/22, 13:25] Amina Yakubu: πππKABEERππ
1⃣0⃣1⃣➖1⃣0⃣5⃣
Ina fitowa naga hadari ya hadu a garin har an fara iska ina tsayi INA jiran me keke napep kawai saina ga wata shegiyar mota ta faka a gabana aminci Allah ya tabbata a gareki ranki ya Dade, sunana Barr Faisal, na Dade INA Neman ki Allah be hadamu sai yau idan bazaki damu ba don Allah ki shigo na baki lift sbd inaso nasan gdnku. Bana bukatar taimakonka don Allah mallam ka tafi, nima don Allah ki taimaka ki saurareni, ni masiyinki ne ba makiyi ba pliss, wallahi na Dade INA sonki, yayyafi naji anfara sai kawai na hakura na shiga muka tafi daidai lkcn kuma motar marwan ta fito, Mr kabeer yana gdn gaba, marwan ya kalli Mr KB yace kare mata mutuncin da kake ya tashi a banza indai a commercial car zata ringa yawo, yanzu haka wanan guy din yanzu ya fara ganin ta, amma kaga yayi convincing dinta ta shiga motarsa yarinyar nada shu'umin kyaun da duk haduwar namiji saiyaji yana sonta, so you have to be very careful, cikin bacin rai KB yace bisu abaya muga INA zai kaita. Haka sukayi ta binmu har kofar gd munyi exchanging no dashi sanan na shiga gd, saida suka tabbatar ya tafi sanan suka dau hanyar gdn marwan.
6:15pm
Kwance nake akan gado abin duniya yayi min zafi, tunanin mum dasu junior ya addabeni yanzu shikenan dad ya rabani dasu? Allah sarki mum, koda wasa bata taba nunamin ba ita tahaifeni ba duk so da kaunar da take nunamin tashi daya mun rabu, ko ya takeji a zuciyarta? Gashi na kira layinta baya shiga, daidai nan naji Kira ya shigo wayaata INA dubawa naga elbash ne, hlo ka wuni lpy? Lpy kalau na matsu na ganki bazan Iya jira harsai gobe ba, so yanzu haka INA kan titin lamido crescent yimin kwatancen gdn, nace to inayi masa sai gashi har kofar gdn, saida na fadawa baba mero sanan na fita, fararen kujeru na ajiye muka zauna a compound din gdn, yana kallon fuskata ya gane nayi kuka, wato har yanzu baki daina kuka ba ko beauty? Wallahi tunanin mum dasu basma ne yaki ya fita a zuciyata, kuma abinda yafi damuna shine idan na kira layinta baya shiga, aikuwa akwai yar matar babanta a office dinmu, Bari na kirata ta turomin sabuwar no ta. Aikuwa yana mata magana ta turo masa Sbd sonshi take, yana bani na fara dialing, bugu biyu ta dauka inayin magna ta fashe da kuka nima kukan nake saida mukayi me isarmu, sanan take fadamin dad ya maida ita abuja Sbd ni, kuma shi ya canja mata layi, nima na Bata labari tun daga ranar da nabar gdnsu har zuwa yanzu in brief ta tausayamin sosai na tambayata su basma da junior ta basu muka gaisa tace kullum sai sun tambayeni sai nace musu kina makarnta, mun Dade muna fita da ita kafin muyi sallama, na Bata hakuri akan ta kwantar da hankalin ta nima yanzu bana cikin matsala hankalina a kwance yake. Cikin farin ciki nacewa elbash nagode Allah ya saka da alkairi, wallahi bakaji yanda naji dadi ba, daidai nan me gadi ya bude gate adon gari ne ya shigo gdn sanye cikin orange shirt da black jeans gashinsa ya kwanta yayi lub, ga wata iska me dadi da take kadawa fuskarsa ba walwala ya karaso wajen ya mikawa elbash hannu sukayi musabaha, ko kallon inda nake beyi ba ya shiga ciki elbash ne yace Aysha ni zan tafi kici gaba da hakuri kinji nasan halinsa yana da miskilanci dariyar yake nayi nace la karka damu wallahi ka gaida aunty rahama yace to zataji insha Allah. Gabana yana dukan uku2 nayi sallama na shiga na same she suna ta hira shida baba mero, ita kadai ce ta amsa min sallama, Amma shi ko kallona beyi ba saida na rusuna na gaisheshi kamar yadda na saba, Amma da kyar ya amsa min ina ganin haka kawai saina tafi daki, INA shiga ya biyoni Ashe ke yar iska ce bansani ba? I don't think lbrn da kika bani gaskiya ne, Sbd na fuskanci kinada rawar kai, wato kin fara Tara maza ko? Cikin sanyin murya nace elbash ne fa, eh nagani elbash ne, Wanda yayi dropping dinki dazu kuma fa? Rasss naji gabana ya fadi.......ko aure kike so? Still banyi magana ba, bazan hanaki soyayya ba tunda bani zan aureki ba, Amma inaso kisani bana son shashanci da rashin kamun kai, ban yarda ki ringa Tara min baza agida ba Sbd haka ki fadawa elbash din ya turo iyayensa wajena muyi maganar aure tunda shi yasan ko ke wacece, zai yadda ya aureki ko besan asalinki ba. Wanan shine last warning dazan baki car key ya wurgomin kan gadon, ga keyn motar da nazo da ita yanzu nan, na barmiki ki ringa zuwa wajen aiki, gud bye. Tunda ya fara magana nake kuka harya fice ya Allah ka kawomin hanyar da zanga iyayena cikin ruwan sanyi ko a daina yimin gori, saida nayi me isata sanan na shiga toilet nayi alwalar sallar magrib.