Shirin Fadama III zata samar wa matasan wasu jihohi 23 ayyukan yi, Malam Bashir Dayyabu ya ce ba a sanar da suna jihohi 23 da zasu amfana da shirin ba,
Shirin karin tallafin kudi ga Fadama III wato FADAMA III Additional Financing (AF) ta ce za ta horar da matasa 6, 900 a fanin aikin noma da kuma kasuwanci a jihohi 23 a fadin kasar.
Jami’in sadarwa na AF ta kasa, Malam Bashir Dayyabu ya bayyana haka a Minna babban birnin jihar Neja a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli a lokacin wata taron FADAMA III.
Dayyabu wanda bai ba da suna jihohi 23 da zasu amfana da shirin ba, ya ce bayan horor na mako biyu da za a yiwa matasan, za a sama masu tallafin kudi wanda zasu iya fara aikin gona ko kasuwanci.
Dayyabu ya ce: '' Mun fara tantance matasa 6, 900 da zasu amfana a cikin wannan shirin na aikin noma a jihohi 23 a fadin kasar”
Ya ce shirin da aka sani da '' Fadama Guys '' na wani bangare ne na kokarin da gwamnatin tarayyar Najeriya da kuma Bankin Duniya ke yi don samar da ayyukan yi ga matasa da kuma inganta aikin noma.