Mata kan yi amfani da sabulun wanka, ko sinadarin detol ko turare ko wasu sinadarai da yanzu ake sayar da su a kantuna don yin wannan wanki, hakan ta sa suke ganin kamar abu ne mai kyau tun da ana sayar da shi ta ko ina,
"Watakila su kasashen da ke irin wadannan sinadari sun gwada da yanayin jikin matansu ne, sai suka yi sinadaran ta yadda ba za su yi musu illa ba. Don haka kamata ya yi mu ma a ce an yi hobbasar yin bincike don a yi na daidai matan nahiyarmu, yadda ba zai yi musu illa ba.
"Amma gaskiya a yanzu likitoci ba su da tabbacin wadannan sinadarai sun dace da jikin matan nahiyarmu ba, kuma mun ga illar su sau da dama, don haka daina amfani da su shi zai fi alheri."
Ita al'aurar mace an halicce ta ne da wasu kwayoyin halitta (vaginal flora) irin wadanda ba a gani da kwayar ido, wadanda aikinsu shi ne su kare wajen daga saurin kamuwa da cututtuka. Su kuma wadannan kwayoyin halitta ba a so a dinga sa musu wani sinadari mai karfi a wajen don zai kashe su ne, "Da sun mutu kuma, to al'aurar za ta zama ba ta da kariya nan da nan cuta za ta iya shiga wajen,"
Sakamakon hakan cututtuka kala-kala za su iya shigar mace ta al'aurarta, saboda duk wata kariya, karfin sabulu da sinadaran nan sun kawar da ita.
Wadanne cututtuka ne mace za ta iya kamuwa da su?
Likitoci da dama sun bayyana cewa da zarar kwayoyin halittar da ke kare al'aurar mace sun mutu, to za ta iya fuskantar hadarin kamuwa da cututtuka kamar:
Mata kan iya kamuwa da cututtuka da dama da yawa ba su san illar tsarki da sabulu ba
Cututtukan da mata za su iya fuskanta idan kwayoyin halitta suka mutu Haifar da kwayoyin cuta (Infection) da za su baibaye al'aurar mace wadanda za su iya kara hadarin jawo nakuda tun lokacin haihuwa bai yi ba, da kuma hadarin saurin kamuwa da cututtuka masu alaka jima'i kamar ciwon sanyi da sauran su.
Yana iya jawo kwayoyin cuta ga mahaifa da kwayayen haihuwa da aka fi sani da Pelvic inflammatory disease (PID). "Wannan al'amari na iya hana mace samun haihuwa kwata-kwata, ko kuma ya sa mace ta dinga daukar ciki a wajen mahaifa, Wata mujallar lafiyar mata ta Amurka ta intanet WebMD, ta ce wani bincike da aka yi ya gano cewa mata masu wanke al'aura da sabulu ko sinadarai sun fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar PID.
Title :
Illolin Amfani Da Sabulu Wajen
Tsaftace Al'aura
Description : Mata kan yi amfani da sabulun wanka, ko sinadarin detol ko turare ko wasu sinadarai da yanzu ake sayar da su a kantuna don yin wannan wanki,...
Rating :
5