Hukumar kula da jin dadin mahajjata ta kasa NAHCON ta sanar da cewa a ranar 30 ga watan Yuli ne maniyyata hajjin bana za su fara tashi zuwa kasar Saudi.
Hukumar ta kuma ce ta fara hada takardun tafiya na maniyyatan wanda ya kai 40,000.
Kakakin hukumar NAHCON Uba Mana ne ya sanar da hakan wa manema labarai a yau Talata.
Ya kuma yi kira ga jihohin kasarnan da su fara yin alluran rigakafi sannan kuma su tanadi kudaden guzirin maniyyatan jihohinsu da wuri.
Uba Mana ya kuma shawarci sauran mutanen da suke da niyar zuwa aikin hajjin da su hanzarta biyan kudaden tafiya kafin lokaci ya kure.
Cikin mutanen da suka kammala biyan kudin tafiyarsu sun hada da maniyyata daga jihohin Kaduna wanda ta fi yawan maniyyatan da yawansu ya kai mutane 6,335, sannan sai jihar Neja, sannan jihohin Zamfara, Kano da Sokoto.