1) Bayern Munich ta dauki dan wasan gaban Real Madrid James Rodriguez a matsayin aro na shekaru biyu da kuma damar sayansa idan ya yi mata. Dan shekaru 25 din wanda ya rattaba hannu na shekaru lokacin da ya zo Real daga Monaco akan £71m a shekara ta 2014, ya buga wasanni 22 ne kacal a La Liga a kakar wasan da ta gabata. An yi ta rade-radin cewa James zai koma Chelsea ko Manchester United.
2) Chelsea na gab da sayan dan wasan tsakiyar Monaco Tiemoue Bakayoko mai shekaru 22, kuma zai iya sa hannu akan lokaci don yabi tawagar kungiyar zuwa China da Singapore.
3) Ko kuma Manchester United na shirin yin tayi sama da na Chelsea, inda kulob din na Old Trafford ya shirya biyan sama da £40m ga dan wasan tsakiyar da ake ta hari.
4) Koci Jose Mourinho na son kungiyar ta kai tayin sama da £60m ga dan wasan tsakiyar Tottenham Eric Dier mai shekaru 23.
5) United ba za ta yiwa dan wasan gaba Zlatan Ibrahimovic mai shekaru 35 tayin sabuwar kwantaragi ba, duk da cewa ta amince da ya ci gaba da jiyyar raunin da ya yi a gwuiwa a filin daukar horonta na Carrington.
6) Har yanzu United bata yi tayin adadin kudin da Inter Milan ke nema akan dan wasan gaban Crotia Ivan Perisic mai shekaru 28 ba, amma ana tsammanin cinikin wanda ke tsakanin £45m zuwa £50m zai iya kammaluwa nan da mako mai zuwa.
7) An rawaito cewa Arsenal na da kwarin gwuiwar ci gaba da rike dan wasan tsakiyarta Alex Oxlade-Chamberlain. Dan shekaru 23 na da ragowar watanni 12 ne a kwantaraginsa.
8) Koci Arsenal Arsene Wenger ya kudiri niyyar ci gaba da rike dan wasan gaba Alexis Sanchez mai shekaru 28, duk da cewa ya ki sanya a sabuwar kwangila kuma ana ta cewa yana son komawa Manchester City.
9) Wenger kuma ya ki yarda ya sayar da gaban Faransa Olivier Giroud mai shekaru 30, har sai an san makomar Sanchez da kuma dan wasan Monaco Thomas Lemar.
10) Gunners din kuma za ta yi takara da Liverpool da Manchester City a kokarin sayen dan wasan bayan Southampton Virgil van Dijk mai shekaru 26.
11) Chelsea za ta mayar da hankalinta akan dan wasan gaban Real Madrid Alvaro Morata mai shekaru 24, a yayin da ta ke kara nuna cewa dan wasan gaban kasar Sifaniya Diego Costa mai shekaru 28 zai bar Stamford Bridge.
12) Ko kuma zai iya sauya shawara don tattaunawar zaman lafiya da Antonio Conte, don ya ci gaba da zama a Chelsea.
13) Roma na son sayen dan wasan gaban Manchester United Anthony Martial mai shekaru 21 a matsayin aro na shekara guda, amma Reds din bata da niyar barinsa ya tafi.
14) Manchester City na cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa na turai guda da suka shirya biyan £27m don sayen dan wasan bayan Real Sociedad Inigo Martinez mai shekaru 26.
15) Barcelona ta fadawa Munir El-Haddadi cewa zai iya barin kulon din akan €14. Kungiyoyin Premier uku Crystal Palace, Southampton, da West ham duka suna nemansa.
16) Barcelona za ta kai tayin karshe na €25m ga dan wasan tsakiyar Guangzhou Evergrande Paulinho.
17) Barcelona ta shirya kai tayin £26m ga dan wasan bayan Arsenal Hector Bellerin.
18) Real Madrid ta bude kofar sayar da dan wasan tsakiya Mateo Kovacic. Ana alakanta dan kasar Crotian da komawa Tottenham, a yayinda Los Blancos ke tattara kudin da take son sayen dan wasan Monaco Kylian Mbappe.
19) Manchester United ta za6i Michael Carrick a matsayin kaftin dinta bayan tafiyar Wayne Rooney zuwa Everton.
#1arewa
Title :
HADA HADAN YAN WASAN KWALLON KAFA A YAU
Description : 1) Bayern Munich ta dauki dan wasan gaban Real Madrid James Rodriguez a matsayin aro na shekaru biyu da kuma damar sayansa idan ya yi mata. ...
Rating :
5