RADE-RADIN SAYAN YAN WASA
1. Arsenal ta amince cewa babu tabbas ko za a sayar mata da Thomas Lemar daga Monaco. Gunners din na ta kokarin sayo dan kasar Faransan daga Monaco amma hakan ya ci tura, saboda Monacon ba ta shirya rabuwa da wani dan wasan ba bayan da ta sayar da Bakayoko da Benjamin Mendy. A yanzu babban burin Arsenal shi ne ta rarrashi dan gabanta Alexis Sanchez ya ci gaba da zama a kulob din.
2. Za a gwada lafiyar mai tsaron ragar kasar Ingila Joe Hart mai shekaru a yau Litinin kafin ya koma West Ham a matsayin aro na shekara guda.
3. Sevilla ta sayi dan wasan gaban kasar Sifaniya Nolito mai shekaru 30 daga Manchester City akan kudi £7.9m.
4. Akwai yiwuwar dan wasan gaban Real Madrid Alvaro Morata mai shekaru 24 ya ki amincewa da koma Premier League, inda zai ya koma kulob din Serie A AC Milan.
5. Ana tsammanin Manchester United za ta kammala sayan dan wasan tsakiyar Inter Milan Ivan Perisic mai shekaru 28 nan da yan kwanaki a cinikin da zai kai £28m.
6. Dan gaban kasar Wales Gareth Bale ya ce yana farin ciki a Real Madrid duk da alakantashi da ficewa daga kungiyar da ake yi.
7. Chelsea ta shirya yin asarar sayen dan wasan bayan Juventus Alex Sandro mai shekaru 26, saboda kulob din na kasar Italiya bai shirya rabuwa da wani dan wasan bayan ba, bayan da ya sayar da Leonardo Bonucci mai shekaru 30 ga AC Milan.
8. Liverpool za ta kara tayinta zuwa £57m ga dan wasan tsakiyar kasar Guinea Naby Keita, amma kocin RB Leipzig Ralph Hasenhuttl ya ce dan shekaru 22n na jin dadin zama a kungiyarsa.
9. Shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya ce kulob dinsa ya kawo karshen sha'awarsa ta sayen dan wasan gaban Arsenal Alexis Sanchez mai shekaru 28 a wannan kakar wasan.
10. Dan wasan tsakiyar Chelsea Nemanja Matic mai shekaru 28 ya kagu ya koma Juventus, amma Blues ta ki rage farashin £40m da take nema a kansa.
11. Kocin Arsenal Arsene Wenger zai karkata ga neman dan wasan gaban Celtic Moussa Dembele mai shekaru 20 idan Sanchez ya bar kulob din.
12. Chelsea na son sayen dan wasan gaban Manchester City Sergio Aguero mai shekaru 29.
13. An yi watsi da tayin £88m da Chelsea ta kai ga dan wasan gaban Juventus dan kasar Ajentina Gonzalo Higuain mai shekaru 29.
14. Dan gaban Arsenal Alexis Sanchez ya ce, yana so ya buga wasa a gasar zakarun turai wato Champions League.
15. Kocin Manchester United Jose Mourinho zai bukaci a bashi dan tsakiyar kasar Jamus Toni Kroos mai shekaru 27, idan Real Madrid ta nace sai ta sayi mai tsaron raga David De Gea mai shekaru 26.
16. Real Madrid na duba yiwuwar sayar da dan gaban Walea Gareth Bale mai shekaru 27, don ta samu kudin sayen dan gaban Monaco Kylian Mbappe mai shekaru 18.
Title :
Hada-Hadan kasuwan Kwallon Kafa a Yau
Description : RADE-RADIN SAYAN YAN WASA 1. Arsenal ta amince cewa babu tabbas ko za a sayar mata da Thomas Lemar daga Monaco. Gunners din na ta kokarin ...
Rating :
5